HUKUNCIN MAHAIFIN DA YA CINYE SADAKIN 'YARSHI

HUKUNCIN MAHAIFIN DA YA CINYE SADAKIN 'YARSHI 


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum Dr. Tambaya ta itace: menene hukuncin mahaifin da ya cinye sadakin 'yarshi da kudaden aure gaba ɗaya, ba gado ba kujeru, bai mata komai na kayan aure ba, bai kuma biyata kudadentaba, wai Don mijin 'yaqi kawo akwatin 'yar agani alhali kuma yasamu yaqinin cewa anyi akwatin.
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikum assalam, Annabi S.A.W yana cewa: (Kai da abin da ka mallaka na mahaifinka ne) kamar yadda Ibnu Majah ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (2291) da kuma Ibnu Hibban a Sahihinsa 2/142.

Malamai sun yi karin haske game da wannan hadisin inda suke cewa Ya halatta Uba ya ci dukiyar 'dansa ko 'yarsa da sharuda guda uku:

1. Idan Ɗan ba ya tsananin bukatar abin.

2. Idan ba wani ya bawa kyauta ba, shi ya yi amfani da shi.

3. Idan bai zama a rashin lafiyar mutuwar daya daga cikinsu ba.

A bisa sharudan da suka gabata,. za mu fahimci abin da Uban ya yi bai dace ba, tun da 'yarsa tana tsananin bukatar abin da ka ambata na Gado da kujeru da sauransu.

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)