HUKUNCIN WALIMAR SAUKAR AL-QUR'ANI

HUKUNCIN WALIMAR SAUKAR AL-QUR'ANI


                                 TAMBAYA❓
Slm. malam ko akwai nassi da yake nuni akan halarcin yin walimar saukar alqur,ani.??

                                     AMSA👇

To dan'uwa malamai suna cewa : Yin walimar saukar Alqur'ani ta kasu kashi biyu:

1. Wanda ya sauke Alquir'ani ya yi walima saboda godiya ga Allah, wannan kam ya halatta, saboda nassoshin da suka zo wadanda suke kwadaitarwa akan godewa Allah akan ni'imominsa.

2. Yin walimar saboda riya cewa ibada ce mai zaman kanta, wannan kam bidi'a ne tun da ba'a samu Annabi ï·º da sahabbansa sun yi ba, don haka yana da kyau wanda ya yi walima ya bayyanawa mutane cewa ya yi ne don godewa Allah, ba wai don kasancewar hakan ibada ce mai zaman kanta ba.

Amma abin da aka rawaito cewa: Umar R.A ya yanka rakumi bayan ya gama haddace & kiyaye suratul-bakara, to wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Ibnu-kathir A Musnadul-farouk 2\571, saboda a cikin sanadinsa akwai Abu-bilal Al-ashhary, wanda Dara-kudni ya raunana.

Allah ne mafi sani

Don neman Karin bayani duba fatawaa Allajna Adda'imah 2\488.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.


Post a Comment (0)