HUKUNCIN WANDA YA MANTA DA SUJJADA KABLI KO BA'ADI



HUKUNCIN WANDA YA MANTA DA SUJJADA KABLI KO BA'ADI
:
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum
 Tambayata itace shin menene hukuncin wanda yamance sujada kabli ko ba'adi yayinda ta kama shi?.
:
*AMSA*👇
:
ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ .
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ،


*Imam Mardaawi (Rahimahullah)* yace acikin _Al-musannaf (2/154)_ na Ibn Qudamah: A rankon sajadar mantuwa Akwai sharadi guda biyu.
1. Ya kasance cikin masallaci.
2. Ya kasance aikin baiyi tsawo ba. Ma'ana ba'a samu tazarar lokacin yin mantuwar da tinawa ba.
Wannan shine ra'ayi mai kyau kamar yadda *Al-Mardaawi* yace.
*Imam Ahmad (rahimahullah)* yace; Zaiyi sajadar ne idan ya tina anan kusa. Koda kuwa ya fita daga masallacin ne.
Kuma yace zaiyi sajadar koda bayan lokaci mai tsawo ne ya tina, ko kuma yayi magana, ko kuma har bayan ya fita masallaci ne. Wannan shine ra'ayin da *Shaykhul Islam Ibn Taymiyyah* ya zaba.
_*Al-Ikhtiyaaraat al-Fiqhiyyah, Shafi na 94).*_

Idan mutum ya manta sujudar mantuwa wacce zaiyi kafin sallama (Sajadar Qabli kenan), har ya sallame bai tina ba, toh zaiyi sujudar qablin ne anan take kuma wajibi ne yinta (idan ya tina anan kusa).

Amma idan kuma ya sallame kuma Bai tina ba har sai bayan an dauki lokaci mai tsawo, ko ya fita daga masallaci, ko alwalarsa ta warware. Toh anan babu bukatar yin sajadar mantuwa, kuma sallasa ta inganta.
_*Al-Rawd al-Murabba’ Sharh Zaadal Mustaqna’ (2/461)*_

*MISALI:*
Idan mutum ya manta tahiyar farko, anan sajadar qabli ta kamashi, toh sai ya manta ya sallame batareda yayi qabli ba, toh zaiyi qablin ne idan ya tina nan take. 

Amma idan bai tina ba anan kusa har sai bayan wani lokaci mai tsawo ko ya fita masallaci, toh anan bazai yi sajadar qablin ba kuma sallarsa tayi.

*Shaykhul Islam Ibn Taymiyyah* yace zaiyi sajadar ne idan ya tina, koda ya tina ne bayan lokacin mai tsawo. Saboda hakan zai zama cikon abinda ya bari ne a sallarsa.

Amma Ra'ayin da yafi kyau shine ra'ayin Mawallafin (rahimahullah) Wanda shine idan bai tina ba sai bayan lokaci mai tsawo, toh bazai rama sajadar ba kuma sallarsa tayi. Idan kuma ya tina anan kusa zaiyi sajadar. 

 والله أعلم،

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)