HUKUNCIN WANDA YA QI YIN AURE

HUKUNCIN WANDA YA QI YIN AURE


TAMBAYA TA 1817
****************
Da fatan ka tashi lafiya? Yaya iyali, malam miye hukuncin Wanda yaki aure kuma yana da hali, kuma yaki Kare kansa daga Neman mata?

AMSA
***
Wanda ya qi yin aure da gangan ba don wata matsalar dake tare dashi ba, Kuma yana da halin yin auren, Kuma yana da sha'awa tare dashi, To hakika wannan ya kauce ma Sunnar Manzon Allah (saww).
Manzon Allah (saww) ya kwadaitar da al'ummarsa akan suyi aure. Yace :
"KUYI AURE KU HAYAYYAFA, DOMIN NI ZANYI MA SAURAN AL'UMMATAI ALFAHARI DAKU ARANAR ALQIYAMAH".
Kuma yace : "AURE SUNNA-TA NE. DUK WANDA BA YA KWADAYIN SUNNAH-TA, TO BA YA TARE DANI".
To lallai idan muka dubi wadannan hadisan zamu fahimci cewar duk wanda ya Qi yin aure, Hakika ya jefa kansa acikin garari.
Malamai sunce duk wanda yake da sha'awa ajikinsa, to aure ya mmzama Wajibi gareshi. Domin aure yana da fa'idodi masu yawa. Kamar samun ladan ciyar da iyali, Bin umurnin addini, koyi da Sunnar Manzon Allah (saww), Samun Qaruwar al'umma, Samar da zuriyar da zasu yi maka addu'a koda bayan ranka, Qulla zumunci, etc.
Allah shi kiyayemu.

WALLAHU A'ALAM.


Post a Comment (0)