YA FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA ?

YA FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA ?    
                                                


                     Tambaya : Ass.Malam shin mutum ya furta saki ga matarsa ba ta jiba, shin ta saku ?     

Amsa: To dan'uwa matar ta saku, saboda sanin an sake ta, ba shi daga cikin sharudan saki, mutukar miji ya furta saki, mace ta saku koda ba ta ji ba, yana daga cikin ka'idoji a wajan malaman fiqhun musulunci: Duk wanda ba'a damu da yardarsa ba wajan tabbatuwar abu, ba'a damuwa da saninsa, yardar mace ba sharadi ba ce wajan zartuwar saki, haka ma saninta an yi sakın ba sharadi ba ne wajan tabbatuwarsa.  
                                                                                Allah ne mafi sani. *Jamilu Zarewa.* 31/10/2015.

*📚Irshadul Ummah.*
Post a Comment (0)