HUKUNCIN YIN SALLAH NAFILA A LOKACIN DA LIMAN YAKE HUDUBAR JUMU'A
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum, shin ana nafila a lokacin da liman yake hudubar Juma'a?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus salam, idan liman na huɗuba sai mutum ya shigo masallaci ya halasta ya yi sallah raka'a biyu a matsayin gaisuwar masallaci (Tahiyyatul Masjidi), saboda hadisin da Sahabin Manzon Allah ﷺ Jabir ɗan Abdulahi ya ruwaito cewa:
Wani mutum ya shigo masallaci a dai-dai lokacin Manzon Allah ﷺ yana huɗuba a ranar Juma'a, sai Manzon Allah ya ce: "Shin ka yi Sallah?", sai ya ce: a'a, sai Manzon Allah ya ce: "To ka tashi ka yi sallah raka'a biyu".
Muslim 875.
Wannan hadisi ya nuna ingancin yin sallar nafila alhali liman yana huɗuba. Sai dai duk da haka akwai Manyan malaman Fiq'hu Allah ya yi masu rahama da suke da fahimtar rashin halascin yin nafila a lokacin da liman yake huɗuba bisa ijtihadi ta hanyar dogaro da wasu dalilai. Abin da ya fi fitowa sarari game da wannan matsalar shi ne, ya halasta mutumin da ya shiga masallaci ya yi nafila raka'a biyu ko da a dai-dai lokacin da liman yake huɗubar Juma'a ne.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEأَسْئِلَةً وَأَجْوِبَةٌ فِي الْإِسْلاَمَمَم177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ