YADDA AKE YIN SUJJADAR TILAWAR AL'QUR'ANI?

YADDA AKE YIN SUJJADAR TILAWAR AL'QUR'ANI?


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum.
Allah ya qarawa malam lafiya da hukuri .
Malam inada tambaya dan Allah malam idan mutum yana karatun Alqur'ani (ba'a cikin sallah ba) sai ya riske inda ake sujada to dan Allah malam yaya akeyin sujadar kuma me ake karantawa acikin sujadai. ALLAH YA QARAWA MALAM ILIMI YA KUMA BAWA MALAM ZURI'A DAYYIBAH.
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus Salam warahmatullah wabarakatuhu.

Anayin Sujjada ne akan gabobi bakwai (7), hadisin yazo cikin sahihul bukhari, bukhari ya kaho hadisin karkashin babin Falalar sujjada
.
1- Goshi da hanchi abu daya (don haka duk lokacin da mutum yayi Sujjada toh dole ka tabbatar goshinka da hanchin ka ya sauka a kasa.)

2- tafukan hannaye guda biyu (uku kenan)

3- gwiwowi guda biyu (biyar kenan)

4- Sannan gyabban yatsu na kafa (bakwai kenan)
Domin ko wane daya ake kirgawa a matsayin daya.

Waɗannan gabobi sune gabobin sujjada waɗanda in mutum ya aikata laifi an sashi a wuta, (Allah ya kiyayemu) toh wuta zata ci ko ina amma banda waɗannan gabobi, saboda Falalar Sujjada.
.
Wannan Sujjada itace ibada mafi girma wadda Allah Maɗaukakin sarki ya halicce ta saboda ita, shi kuwa Makasudin Ibada yana tattaruwa a cikin Sujjuda gaba ɗaya ne.
.
Akwai gurare da aka shar'anta Sujjada a halin ba'a Salla bane kamar yadda kayi tambaya, daga cikin guraren akwai. "Gurare tsakanin guda Goma Sha biyar a cikin qur'ani, waɗanda idan kana karantasu zaka yi Sujjada." 

AYOYIN DA SUKE KUNSHI SUJJADAR TILAWA: SUNE KAMAR HAKA:

1- Suratu Al-a'araf aya ta 206.
2- Suratur Ra'ad aya ta 15
3- Suratun Nahli ayata 50.
4- Suratul Isra'i aya ta 109.
5- Suratu Maryama, aya ta 58.
6- Suratul Hajj, aya ta 18.
7- Suratul Hajj, aya ta 77.
8- Suratul Furkan aya ta 60.
9- Suratun Namli, aya ta 26.
10- Suratus Sajda, aya ta 15.
11- Suratu Saad aya ta 24.
12- Suratu Fussilat aya ta 38.
13- Suratun Najmi aya ta 62.
14- Suratul Inshikak aya ta 21.
15- Suratul Alak aya ta 19.

Toh duk inda ka karanta zakayi sujjada sannan da duk wata ni'ima data samu gare ka.
.
ISujjadar tilawar alqur'ani ana yinta ne yayin da kazo inda akeyin sujjadar cikin qur'ani, zaka kalli gabas Sannan ka karanta wannan Addu'ar ko ka roke Allah buqataunka :- ga Addu'ar kamar
سَجَدَ وَجْهِيَ لِلَّذِي خَلَقَهُ، وَشَقَّ سَمْعَهُ وَبَصَرَهُ، بِحَوْلِهِ وَقُوَّتِهِ، فَتَبَارَكَ اللهُ أَحسَنُ الْخَالِقِي
 FASSARA:-
"Fuskata tayi Sujada ga wanda Ya halicce ta, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta, da iyawarsa da kuma Karfinsa. Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita.

اللّهُـمَّ اكْتُـبْ لي بِهـا عِنْـدَكَ أَجْـراً ، وَضَـعْ عَنِّـي بِهـا وِزْراً ، وَاجْعَـلها لي عِنْـدَكَ ذُخْـراً ، وَتَقَبَّـلها مِنِّـي كَمـا تَقَبَّلْتَـها مِنْ عَبْـدِكَ داود
 Fassara:
Ya Allah! Ka rubuta mini lada saboda ita (sujadar) ka kankare mini zunubai saboda ita, Ka sanya ta ta zamo taskar arziki gare ni a wajen Ka, kuma Ka karbe ta daga gare ni kamar yadda Ka karbe ta daga bawanka Dawuda.

Duk wacce kayi tayi

WALLAHU A'ALAM

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)