KINA JI NA?

KINA JI NA? 



Idan ya ce ki ba shi haďin kai ku yi sa6on Allah (Zina) in dai kina son shi, ki faďi mashi Zina ba ta daga cikin ma'aunin nuna soyayya. Idan kuwa sai kin ba shi kanki ne zai tabbatar kuna son juna, to ki tuna masa cewa ai ya fi son mahaifiyarsa fiye da ke, don haka ya je ya fara yi da mahaifiyarsa da 'yan uwansa mata matukar hakan shi ne So. Idan kuwa ya ki yin hakan, kin ga ke ce ya ďauka sakarya Qazama kenan 🤷.

Namiji zai iya barin aikinsa na yini daya, ya yi tafiyar yini daya, ya kashe maki kuďi masu yawa duk don saboda ya biya bukatarsa tare da ke ba tare da ya ta6a jin sonki na second ďaya a zuciyarsa ba. Don haka sai ki yi wa kanki karatun ta natsu. Sex is not a Loveometre.

Masoyan zamani a yi hakuri idan na kausasa harshe 

*Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*
*30/01/2019.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*
Post a Comment (0)