MACE MAI HIKIMA
Bayan auren su da shekaru uku bai taba nesa da matar sa da dansa ba, kwatam sai tafiyan kwana 3 ta kama shi.
Ya sallami matar sa, dan sa da mahaifiyar sa. Dabi an maza ne duk lokacin da tafiya ta kama su, sukan yi waya da matar su a duk lokaci ko bayan kowani minti 30
Bayan ya tafi, sai matar sa ita kuma ta shiga bangaren mahaifiyar sa.
Tana zaune da dansa da mahaifiyar sa, tafiyan sa bayan awa 1 ya kirata don shaida wa matar sa halin da yake ciki na tafiya amma bata daga wayan ba.
Chan bayan wani awa 1 ya sake kiran ta taki dagawa, haka har wannan ranan ya wuce yana kiran ta bata dagawa.
Mai gidan da yaga haka sai ya kira kanwar sa yace taje ta duba matar sa da dansa ko lafiya in ya kirata a waya bata dagawa, kanwar sa ta shaida masa lafiya bayan ta ziyar ce su.
Rana ta biyu yaci gaba da kiran ta bata daga ba, ya sake kiran kanin sa daya je gidan sa ya duba lafiya, shima ya shaida masa lafiyan su.
Chan tsakiyar rana ya kira mahaifiyar matar sa, itama taje ta duba su ta kuma shaida masa suna cikin koshin lafiya.
Shi kuma in ya kira ta a waya bata daukan kiran sa, hankalin sa yaki kwanciya ya shiga damuwa sosai, har ya soma zargin matar sa anya ba ha'intar sa ta soma ba kuwa, ko tana tare da wani namijin ne a gidan sa.
Wannan tunanin da kuma tunanin matar sa da dan sa suka hana shi sakat, a cikin wannan daren na kwana biyu mai makon kwana 3 ya tashi don ya dawo gida
Yana isa gidan sa, yana kwankwasa kofa sai matar sa ta bude masa kofa? Tace lafiya ka dawa a wannan lokaci bayan kace min kwana 3 zakayi?
Mijin yace na shiga damuwa sosai na rashin daukan kiran wayan da nake miki, han kalina ya kasa kwanciya, tunanin ki da dana ya hana ni in tsaya don karasa wannan aiki na kwana ki uku.
Nanfa matar nan ta zuba kafafun ta a kasa tana neman gafara.
A wannan lokacin take tambayan mijin nata cewa:
Shin tunda ka tafi ka kira mahaifiyar ka don jin yedda take?
Yayi shiru
shin ka kira mahaifiyar ka don shaida mata halin da kake ciki na yanayin tafiya
mai gidan nata yace a a
Nan fa matar tace: wallahi tallahi halin da ka shiga na rashin ji daga gare ni da danka bai kai rabin halin da mahaifiyar ka taji na rashin ji daga kare ka ba.
Hakika mahaifiyar ka tana cikin damuwa na rashi sanin halin da kake ciki na tafiya.
Kana fita na dauki danka muka tafi wajen ta, nake sa hankali kan wayanta ko zaka kira ka shaida mata halin da kake ciki na tafiya amma baka kira ba sai nawa wayar kake kira.
Wannan dalilin ne yasa naki daukan wayar ka, me yasa ka damu da ni da danka baka damu kaji daga mahaifiyar kaba?
Kasani aljannar ka tana ga mahaifiyar ka, ni kuma aljanna ta tana daga kare ka, ya zama wajibi in nuna maka yedda zaka sami aljanna kafin in sami tawa aljanna.
Don haka mahaifiyar ka a kullum ta zamo mace ta farko wacce ya kamata ta san halin da kake ciki ba matar ka ko dan ka ko yarka ba.
Mahaifiya itace abu mafi girman girmamawa bayan Allah da manzon sa.
Allah karawa Annabi daraja
Allah karawa iyayen mu mata daraja yasa Aljannar firdau si itace makomar su.
idan an anfana da wannan sako
Na sadaukar da ladan zuwaga mahaifiyata umma na.
Allah yasa maza sugane uwa dabam take sudinga fifita mahaifiyarsu akan komai tsakanin ya'yan su da matayensu Allah yasa agane gsky amin
Pls sisters mu zama masu taimakawa yan uwanmu maza da mazajin mu da samarin mu su aikata biyayya tare da hidimtawa iyayen su