HUKUNCIN KISS TA HANYAR WAYA

HUKUNCIN KISS TA HANYAR WAYA 📱

TAMBAYA❓


Assalam alaikum.Malam SHIN ya halatta mutun yayiwa budurwarsa KISS yayin da suke waya, idan har an bashi ita kafin suyi aure?

AMSA👇

Wannan yana daga cikin ire iren abubuwan da fitsararrun samari da 'yan matan zamani suka Qirkiro. Kuma yana daga cikin abubuwan da suke cire musu kunya, kuma yake afkar dasu acikin zina.
Misali saurayi da budurwar da suka saba yiwa Junansu Kiss ta waya, da zarar sun hadu FACE TO FACE, babu abinda zasuyi tunani illa su aiwatar da Kiss din azahiri.
Irin wadannan al'adun turawa ne, bai dace da dabi'unmu da addininmu ba..
Mu a addininmu ba'ayin kowanne irin Kiss sai bayan an daura muku aure da juna.
Annabi (saww) yana cewa: ''Kunya tana daga Imani. Duk wanda bashi da kunya, to bashi da Imani.." kuma yace "DUK WANDA YAYI KAMA DA WASU MUTANE, TO TABBAS YANA CIKINSU".
Don haka duk wanda yake so ya haifi
'ya'ya masu albarka, to wajibi ne ya nuna dabi'u masu kyau irin na Musulunci tun alokacin neman auren mahaifiyarsu.

Allah ya shirye mu baki daya, Yasa masu yi su daina. Ameen 

WALLAHU A'ALAM.

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

 ```Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.``` 

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)