*💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi.*
*✨سؤال وجواب في أحكام الصيام.*
Wallafar:
*Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin.*
.
.
(6) ABUBUWAN DA BA SU KARYA AZUMI.
*3. Ɗanɗana abinci, iyo (swimming), kuskure baki da shaƙar ruwa a lokacin alwala.*
.
Tambaya I: Shin ɗanɗana abinci yana karya azumi?
Amsa: Idan ba a haɗiye abincin ba, azumi yana nan amma kada a yi hakan sai in ya zama wajibi.
Tambaya II: Menene hukuncin yin iyo ga wanda yake azumi?
Amsa: Babu wani abu don mai azumi ya yi iyo yadda yake so. Amma ya yi ƙoƙari kada ruwa ya kai maƙogoronshi. Bugu da ƙari, iyo a ruwa yana sa annashuwa ga wanda yake azumi kuma ya taimaka masa wajen hana shi shan wuya
.
Tambaya III: Idan mutum ya kuskura bakinsu ko ya shaƙa ruwa a lokacin alwala kuma ruwan ya zarce zuwa maƙogoronshi, shin azuminshi na nan?
Amsa: Idan mutum ya kuskura bakinshi ko ya shaƙa ruwa har ya kai ga ruwan ya kai maƙogoronshi, azuminshi yana nan saboda ba da gangan ya yi ba. Allah (S.W.T) Ya ce:
*”وَلَكِن مَّا تَعَمَّدَتْ قُلُوبُكُمْ“*
Ma'ana: *“kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukãtanku suka ganganta....”* (Ahzab: 5).
.
Mu haɗu a tambaya ta gaba.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*▫️Ansar.*
*📚Irshadul Ummah.*
Ku kasance da mu a Whatsapp ta wannan number *08166650256.*
Telegram:
https://t.me/irshadulummah1