TAMBAYOYIN AZUMI 02

*💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi.*

*✨سؤال وجوب في أحكام الصيام.*


Wallafar:
*Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin.*
.
.


*(2) KAMEWA:*

Tambaya: Menene hukuncin cin abinci ko shan abin sha a yayin da ladan yake kiran sallah? Or bayan wani ɗan lokaci da kiran sallar, musamman in babu tabbacin fitowar alfijir.

Amsa: Mu kula da wayewar gari. Idan ladanin mai kula ne (wato ya san lokuta sosai), har ya kasance ba ya kiran sallah sai alfijir ya keto, to mutum zai daina cin abinci da zarar ya ji kiran sallarsa, Idan ladanin yana kiran sallar ne tare da kokonto, abin da ya fi shi mutum ya kame daga ci da sha idan ya ji kiran sallah.

Wallahu A'lamu.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*▫️Ansar.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*

Telegram:
https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)