YA MATSAYIN MAIMAITA FATIHA A CIKIN SALLAH?

217 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU

YA MATSAYIN MAIMAITA FATIHA A CIKIN SALLAH?


TAMBAYA:

Assalamu alaikum, malam dan Allah za a iya maimaita fatiha a sallar nafila saboda ina son in yi wata sallah ce a ka ce wai sai na maimaita fatiha guda goma a kowace raka'a?

AMSA:

Wa'alaikumus salam, da farko dai ƴar uwa an karhanta maimaita Fatiha sau biyu ko fiye da haka a cikin sallah, abin da ya sa hakan ya zama ba daidai ba shi ne saboda ba a ruwaito hakan daga Manzon Allah ﷺ ba, mutumin da ke maimaita Fatiha a cikin sallah da nufin maimaitawar a matsayin wata ibada ce, to tabbas ya yi abin qyama, domin da ace hakan ya kasance alheri ne, to da Manzon Allah ﷺ ya aikata hakan.

Sai dai wanda ya maimaita Fatiha saboda ta kuɓuce masa bai yi ba, ko saboda bai yi ta a surar yadda aka so a yi ta ba, to wannan halas ne, misali: Mutum ya asirta karatun Fatiha a sallar da ake bayyanarwa, to wannan babu laifi idan ya maimaita Fatiha daga farkonta don ya riski abin da ya kuɓuce masa na yadda aka shar'anta a bayyanar...

Dubi Assarhul Mumti'u Alá Zádil Mustaqni'i (3/239) don neman qarin bayani.

Saboda haka ƴar uwa bai tabbata daga Manzon Allah ﷺ cewa yana maimaita Fatiha na wani adadi sananne a cikin sallar Nafila ko Farillah ba, kenan sai ya zama wannan sallah da aka ba ki aka ce a maimaita Fatiha sau goma a kowace raka'a bid'a ce ba sunnah ba, kuma makomar bid'a ita ce wuta kamar yadda hadisi ya tabbatar, Allah shi kare mu.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
17/09/2019 M.

Daga:
ZAUREN SAQON ANNABTA NA MATA ZALLA
Post a Comment (0)