YADDA AKE YIN SUJJADAR SHUKURI?

YADDA AKE YIN SUJJADAR SHUKURI?
:


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Da fatan kowa ya tashi lafiya, malam ya haquri da mu? Allah ya saka da alkhari, dan Allah malam ya ake yin sujudar shukri Rabbi in Allah ya yi wa mutum ni’ima yana son gode masa, sallah ake yi ko kawai sujjada ake yi? Allah ya sa ku gama da duniya lafiya Ameen na gode.
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus Salámu Wa Rahmatullahi Wa Barakátuhu.
 
Amin na gode da wannan kyakkyawar addu'a. Sujúdus Shukri ita ce sujjadar da ake yi domin nuna godiya ga Allah saboda wata ni'ima da Allah ya azurta bawa da ita. Sujúdus Shukri sujjada ce falan ɗaya, wato ba sujjadu biyu ba ne irin yadda ake yi a sallah.
Hadisi ya tabbata daga Sahabin Manzon Allah ﷺ Abu Bakrata Allah ya qara masa yarda cewa: "Manzon Allah ﷺ ya kasance idan wani abun alheri ya zo masa, ko kuma aka yi masa bushara da shi, yakan gurfana yana mai sujjada, yana mai godiya ga Allah". Imam Attirmizhiy ya ruwaito kuma ya kyautata shi a hadisi mai lamba ta (1578), Abu Dáwud a lamba ta (2774), Ibn Majah kuma lamba ta (1394).
Yin Kabbarar Harama a lokacin yin sujúdus Shukri bai tabbata daga Manzon Allah ﷺ ba, haka yin kabbara a yayin sunkuyawa yin sujjadar, haka nan yin sallama idan an kammala sujjadar, duka waɗannan ba su tabbata daga Manzon Allah ﷺ ba, ko daga Sahabbansa ba.
Wasu malaman suna da fahimtar mai yin sujúdus Shukri zai faɗi tasbihin da ake faɗi ne a cikin sallah, saboda dama sujjada mahalli ne na yin tasbihi. Amma shi Imamus Shaukani sai ya ce: "A game da abin da Annabi ﷺ yake faɗi a sújudus Shukri bai zo a hadisai ba, to wanda ya yi sujjadar mene zai faɗa kenan? To abin da nake cewa shi ne: ya kamata ne ya yawaita godiya ga Allah Mai girma da buwaya; saboda dama ai sujjada ce ta godiya".
Duba Assailul Jarrár (175).
Haka nan ba dole ne sai mutum yana da alwala zai yi sujudus Shukri ba, saboda ita ba sallah ba ce, malaman da suke sharɗanta alwala ko tsarki ga mai sujudus shukri suna qiyasta ta ne da sallah, zancen da ya fi inganci shi ne sujúdus shukri ba daidai take da sallah ba, ba dole ne sai mutum ya cika sharuɗɗan sallah ne zai iya yin sujjadar godiya ga Allah ba, saboda duka waɗannan sharuɗɗa ba su tabbata daga Manzon Allah ﷺ a kan sujúdus Shukri ba.
Domin qarin bayani a duba Majmú'ul Fataawá (21/277), da (23/170), ko a duba Fataawál Lajnatid Dá'ima (7/263).

Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)