Azumi Ake Fa!
.
Yanayin garin ya kasance mai zafi rau, duk da iska tana kad'awa amma zafi take fitarwa.
" Azumin yau fa za a sha wahala."
Miko ya fad'a a zuciyarsa, lokacin da yake k'ok'arin barin majalissa don zuwa siyo ruwan-gishiri-da-suga (O. R. S) Kyamis d'in Lawandi ya nufa, amma tun daga nesa ya ga wajen a cike mak'il. Isarsa wajen ke da wuya ya samu waje ya tsaya, don raguwar layin ya siyo abin da ya kai shi ya dawo. Lullu6in biri! Wani matashi ne ya zo wajen don siyan magani, bai kama da soko ko ga6o ba amma aykinsa ne zai ba shi wani suna da ya yi kama da haka. Aka gama sallamar mutane aka zo kan Miko, sai ya yi alkunya ya bari a sallami wannan matashin. O. R. S ya siya da kuma bega, ana mik'o masa bud'ar bakinsa ya ce:
" Yarinyar nan za ta gane yau shayi ruwa ne."
Miko da maikyamis suka d'auke wuta, don maganar da wannan saurayin ya fad'a. Amma shi ko ya kula kunama ta harbi kasko. Can Miko ya yi ta maza ya fuskanci matashin, ya ce masa:
" Afuwan na tambaye ka?"
"E."
" Kai Musulmi ne kuwa?"
Ya yi tiris da mamakin tambayar Miko.
" E."
Ya amsa fuskarsa ta canja domin ya yi mamakin, wannan tambayar da Miko ya yi masa.
" Ka san wannan kalmar da ka fad'a, za ta iya karya maka azumi? "
Matashin nan da nan ya harzuk'a, ya ba shi amsa:
" Ban sani ba sai da ka fad'a 'Danmasani!"
Miko ya san magana ya fad'a masa, amma ya k'ara daurewa ya k'ara ce masa:
" Ya kamata ka san irin kalaman da za ka rik'a yi, ko ba don kare mutunci ba don raya Azuminka kada ya karye."
Tashin hankali ba a sa maka rana! Nan fa matashin nan ya fara zage-zage, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba ya bar wajen. Mamaki ne ya kama Miko ya ce:
" Wasu mutanen kawai suna Azumi a baki ne, amma ayyukansu ne zai nuna maka Azumi ya yi Gabas su sun yi Yamma."
Bayan Miko ya dawo gida duniyar tunani ya fancala, yadda mutane suke wasa da Allah bayan ya ce:
" Bai halicci mutum da aljan ba, sai don su bauta maSa. Amma sai ka ga wasu mutanen suna wasa da bautar."
K'arshe....
© Salisu Salisu.