RAMADANA WATAN TSORON ALLAH (01)

RAMADANA WATAN TSORON ALLAH (01)



• Watan Ramadana wata mai girman daraja da albarka!

• Watan Azumi a yininsa da tsayuwa da yin nafilfili da Ibadu a darensa, Watan Karatun Al-Qur’ani, Watan Yanta bayi da kuma yin gafara, Watan Sadaqa da alheri.

• Watan da ake bude Kofofin Aljannah, kuma ake ninka lada ayyuka,Watan amsa Addu’o’i da daukaka darajoji, kuma ake gafarta zunubai a cikinsa.

• Watan da Allah Yasa azumtar shi ya zamo É—aya daga cikin rukunnan Musulunci, don haka Annabi SAW Ya azumce shi kuma ya umurci mutane da azumtar shi, harma Annabi SAW Ya bada labarin cewa duk wanda ya azumce shi yana mai Imani tare da neman lada a wajen Allah, an gafarta masa abunda ya gabata na zunubansa.

• Watan da daren daraja da albarka a cikinshi yake, daren da yafi dare dubu alheri, duk wanda aka haramta wa wannan alheri ya kade ya shiga uku.

Don haka Yan’uwa Musulmi mu girmama wannan Wata ta hanyar kyautata niyya, da dagewa wajen azumtar shi da raya dararen shi, da yin gaggawa zuwa ga ayyuka alheri a cikinsa, tare da kokarin tuba ta gaskiya daga dukkan zunubai.

✍ AnnasihaTV
Post a Comment (0)