FALALAR AMBATON ALLAH {1}
Haqiqa zikiri ko ambaton Allaah yana daga cikin mafiya tsarkakan ayyuka da kyawawansu da girmansu kuma mafiya soyuwa a wurin Allaah Azza Wa Jalla. Tirmizi da sauransu sun ruwaito daga Abu Darda’u (RA) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ashe ba zan ba ku labarin mafi alkhairin ayyukanku kuma mafi tsarkinsu (dadinsu) a wurin Mamallakinku kuma mafi daukakawa ga darajojinku kuma mafi alkhairi gare ku daga ciyarwarku ga zinari da takardun kudadenku ba, kuma mafi alkhairi gare ku a ce kun hadu da abokan adawarku su doki wuyayenku ku doki wuyayensu ba?” Sai suka ce: “Hakika muna so ka ba mu (wannan labari) ya Manzon Allaah!” Sai ya ce: *_“Zikirin (ambaton) Allaah Madaukaki.”_*
Masu ambaton Allaah, masu tunawa da Allah su ne a kan gaba wurin tafiya don haduwa da Allah da kuma Ranar Lahira lami lafiya. An karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (ﷺ) ya ce: *_“Masu kadaitawa sun wuce gaba. Suka ce su wane ne masu kadaitawa ya Manzon Allaah?” Ya ce: “Masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambato (da yawa) mata.”_* Wadannan su ne -bayin Allaah- wadanda Allah Ya yi musu tattalin masauki mai girma da lada mai girma. Allaah yana cewa
وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا
*_“Masu zikiri (ambato da tuna) Allah da yawa maza da masu zikiri mata, Allaah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani lada mai girma.”_*
Ina roqon Allaah dacewa da shiriya zuwa kowane alkhairi, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allaah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alqur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin qai
*الله تعالى أعلم*
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_