HAQIQA YIN SAHUR ALKHAIRI NE.
Yana daga cikin albarka da mai azumi yake samu a cikin watan Ramadan, wato tashin ya yi sahur, domin akwai alkhairi a cikin hakan Kuma zai taimaka wajen yin rangwame wa mai azumi. Barin yin sahur haqiqa yana jawo asarar falala mai yawa:
Bismillahir Rahmanir Raheem.
عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: قال رسول الله ﷺ: ”تسحروا فإن في السحور بركة“. متفق عليه.
An karɓo daga Anas bin Malik (r.a) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku yi sahur, domin a cikin sahur akwai albarka”. Bukhary Muslim.
.
An so mai azumi ya jinkirta lokacin sahur ďinsa, wato kada ya yi shi cikin dare sosai, kuma kada a yi sakaci har alfijir ya fito.
Allah Ya sa mu dace Kuma Ya sada mu da alkhairai da suke cikin wannan wata mai albarka.
.
*✍🏿Ayyub Musa Jebi.*
*ANSAR.*
*05-05-2019.*