FALALAR AMBATON ALLAH {2}

*_FALALAR AMBATON ALLAH_* {2}




Yaku bayin Allaah! ambaton Allaah wato zikiri shi ne yake raya zukata, zukata ba su rayuwa sai da shi, Buhari ya ruwaito a cikin sahihinsa daga Abu Musa Al’ash’ari (RA) daga Annabi (ﷺ) ya ce: *_“Misalin wanda yake ambato ko tuna Ubangijinsa da wanda ba ya ambato ko tuna Ubanginsa kamar misalin mai rai ne da matacce.”_*

Hakika zukata ba za su samu tabbatuwa da natsuwa ba, ko su samu jin dadi su samu sa’ada ba, sai tare da zikirin Allaah da tunawa da Shi. Allaah Madaukaki Yana cewa:

الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ اللَّهِ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ

*_ “Wadanda suka yi imani, zukatansu suna samun natsuwa ne da ambaton Allaah. Ku saurara! Da ambaton Allaah zukata suke samun natsuwa.”_* 

_Ambaton Allaah shi ne ke kawo mafita a bayan kunci, ya kawo sauki a bayan tsanani, ya kawo farin ciki a bayan wahala da damuwa. Shi yake kwaranye abubuwan da suke kawo bakin ciki ya saukaka al’amura ya tabbatar da raha da sa’ada a duniya da Lahira._ Babu abin da yake magance bakin ciki ya gusar da tsanani kamar ambaton Allaah da zikirin Allaah Madaukaki. Annabinmu (ﷺ) ya kasance a duk lokacin da wani abin bakin ciki ya same shi yana cewa: *_“La ilaha illallahul azim, la ilaha illallahul halim. La ilaha illallahu rabbus samawati wa rabbul arshil karim.”_* Ma’ana: _“Babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah Mai girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah Mai hakuri. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa kuma Ubangijin Al’arshi Mai girma.”_ Sannan Mai Tsira da Amincin Allaah yana cewa: “Addu’ar ma’abucin kifi: *_“La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimina.”_* Ma’ana: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Tsarkinka ya tabbata, lallai ni na kasance daga cikin azzalumai.” *_Babu wanda zai fada a cikin bakin ciki da zai yi addu’a da ita face an kwaranye masa bakin cikinsa.”_*



Ina roqon Allaah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allaah mai iko ne a bisa kowane abu. Allaah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alqur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin qai



*الله تعالى أعلم*


_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
Post a Comment (0)