HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI 1️⃣1️⃣
🔷 Tambaya:- Idan jini yazowa mace mai ciki acikin watan ramadhan da rana shin zaiyi tasiri wurin ɓata mata azumi??
🔶 Amsa:- Idan jinin haila ko Nifasi yazowa mace alhalin tana azumi to azuminta ya ɓaci saboda faɗin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama "ba shin idan tayi haila bata sallah da azumi ba". Bukhari 1951.
Dan haka haila tana cikin abubuwan da suke ɓata azumi hakanan Nifasi, fitar jini ga mai ciki da rana acikin watan ramadhan idan har haila ne to hukuncin sa kamar hukuncin wacce bata da cikine, azuminta ya ɓaci, Hailar da zai zowa mai ciki shine irin hailan da zai na zuwa mata akwanakin da ta saba tun daga farkon ɗaukan cikin, Abisa zance mafi inganci cikin zantukan malamai yanada hukuncin haila, amma idan jinin ya ɗauke mata bayan ɗaukar cikin sai ya kasance yana zuwa mata kaɗan kaɗan ba yadda ta saba ba, to wannan ba haila bane kuma bashida hukuncin haila".
📝 المصدر :
[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص١٦].
# Zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah