HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI 1️⃣2️⃣

HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI 1️⃣2️⃣


🔷 Tambaya:- Idan mace taga jini acikin kwanakin hailarta, washe gari kuma bata ganshi ba tsawon wuni guda, yaya zatayi?? 

🔶 Amsa:- Abunda yake zahiri shine, wannan tsarki ko bushewar da ta gani acikin kwanakin hailarta, shima yana cikin haila, bazata daukeshi a matsayin tsarki ba, dan haka zata kame daga dukkan abinda mai haila take kamewa daga gareshi, na daga sallah da azumi da jima'i...
    Wasu malamai kuma suna cewa; duk wacce take ganin jini yau, gobe bazata gani ba, jinin da ta gani haila ne, bushewar kuma tsarkine, zatayi haka har tsawon kwanaki goma sha biyar, idan ya haura kwana goma sha biyar ya zama jinin istihadha, wannan zancen shine zancen da yafi shahara a mazhabar Imam Ahmad Allah ya masa rahama". 

📝 المصدر :
[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص١٧].

# Zaurenfisabilillah 

https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)