HUKUNCIN ITIKAFI
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Menene hukuncin i'itikafi ga namiji da mace?
Kuma shin sharadi ne sai i'itikafin ya zama tare da azumi?
Sannan da wadanne abubuwa ake son mutum mai i'itikafi ya shagalta da su?
Yaushe ne kuma zai shiga wurin i'itikafinsa?
Yaushe ne kuma zai fita daga cikinsa?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀:👇
:
I'itikafi sunnah ne ga maza da mata, saboda abun da ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) na cewa ya yi i'itikafi a watan Ramadan, kuma daga qarshe sai lamarinsa ya tabbata akan i'itikafin kwanaki goman qarshen Ramadan, kuma sashin matansa sun kasance suna yin i'itikafi tare da shi (صلى الله عليه وسلم), haka kuma matansa sun cigaba da yin i'itikafi a bayansa.
Kuma mahallin da ake yin i'itikafi shi ne: masallacin da ake yin sallar jam'i, kuma idan a kwanakin i'itikafinsa juma'a za ta gitta to an so ya aiwatar da i'itikafinsa a masallacin juma'a.
Kuma a mafi ingancin magana daga zantukan maluma; i'itikafi bashi da wata iyaka da aka iyakance masa, kuma ba a shardanta yin azumi tare da i'itikafi, saidai kuma yinsa tare da azumin shine ya fi.
Kuma sunnah ga i'itikafi shine mai yinsa ya shiga wurin i'itikafinsa a lokacin da ya niyyaci haka, ya kuma fita daga wurin bayan qarewar lokacin da ya diba wa kansa; (ko ya niyyata), amma ya samu damar ya yanke i'itikafinsa (ya fita daga masallaci) idan akwai buqatar hakan, saboda kasancewar i'itikafi sunnah ne, da baya wajaba akan mutum don shiga cikinsa ko fara shi, matuqar dai ba na bakance ba ne.
Kuma mustahabbi ne a yi i'itikafin kwanaki goman qarshen watan Ramadan, a matsayin koyi da Annabi (صلى الله عليه وسلم), kuma duk wanda zai yi i'itikafinsa to mustahabbi ne ya shiga wurin i'itikafin bayan sallar asubah, a yinin ashirin da ɗaya (21), yana mai koyi da Annabi (صلى الله عليه وسلم), sai kuma ya fita idan kwanaki goman suka qare, idan kuma ya yanke shi gabanin cikar kwanaki goman to babu laifi akansa, matuqar dai ba bakance ya yi ba, kamar yadda ya gabata. Kuma abun da ya fi shine ya kama wuri aiyananne a masallaci –in hakan ya sauqaqa masa-, kuma an shar'anta wa mai i'itikafi cewa ya yawaita ambaton Allah, da karatun alqur'ani da neman gafara, da addu'oi, da kuma salloli matuqar dai ba a lokutan hani ba ne. Kuma babu laifi wassu daga cikin abokansa su ziyarce shi, haka kuma babu laifi ya yi tadi da su, kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) wassu daga cikin matansa su ke ziyartarsa, su ke kuma yin tadi da shi, harma a wata rana matarsa Uwar muminai Safiyyah ta ziyarce shi alhali yana i'itikafi a cikin watan azumi, a yayin da ta tashi za ta koma sai ya tashi tare da ita ya raka ta bakin kofar masallaci, Sai hakan ya nuna cewa babu laifi kan aikata irin wannan.
Kuma wannan aikin nasa ya qara fito da cikar qanqan-da-kan Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) da tawali'unsa, da kuma kyakkyawar mu'amalarsa tare da matansa, Allah ya yi daɗin yabo da salati a gare shi.
([1]) Wannan mas'alah an yaɗa ta a cikin littafinsa TUHFAUL IKHWAAN, tana nan kuma a cikin MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH (15/441-443).
([2]) Wannan ya zo daga A'ishah (رضي الله عنها) a cikin Sahihul Bukhariy (lamba: 2072), da Muslim (lamba: 1172).
([3]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 2035), da Muslim (lamba: 2175).
Wallahu A'alam
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ