JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 03
Kamar yadda ya gabata muslunci ne ke riqe da jagoranci tun farkonsa, ba wai kafirci ya fara zuwa sannan musluncin ya zo don ya kawar da shi ya shimfida bautar Allah a bayan qasa ba, mafi yawan malamai sun tafi ne kan cewa Wud, Suwa', Yaguth, Ya'uuq da Nasra gumaka ne na wasu bayin Allah mutanen kirki da suka rayu a bayan qasa, su ne mutanen Nuh AS suka riqa bauta musu a wancan lokacin, da yake bincike da diddigi sun tabbatar da cewa Nuh AS a Iraqi ya yi rayuwarsa isar wadannan gumaka zuwa ga Larabawa ba wani abu ne mai wahala ba, su ma sun gaji bautar kuma sun ci gaba a mabambantan lokuta, yadda jagorancin muslunci ya sami rauni kenan a wannan zamanin.
.
Ibn Abbas RA yana cewa an sami sabani kan mutanen kirkinnan masu wadancan sunayen na sama:-
1) Maganar farko ta hanyar Ibn Jarir: Ya'uuq da Nasra bayin Allah ne salihai daga jikokin Annabi Adam AS, suna da dalibai masu yi musu biyayya suna koyi da kyawawan dabi'unsu to da suka mutu sai muridansu da sauran mabiyansu suka yanke shawarar cewa lallai a dan yi gumakansu don a riqa tunawa da su, duk lokacin da aka gan su sai a sake samun kuzari wurin bautar Allah.
.
Wannan ya sa suka yi gumakan suka ajiye, yau da gobe su ma suka bar duniyar na bayansu suka zo, Iblis ya sami damar kurdo musu sai suka shiga bauta wa gumakan, suna roqonsu ruwan sama da sauransu, tun daga lokacin aka bar Allah aka koma bautar gumaka, dalilin da ya sa Allah SW ya turo Annabi Nuh AS kenan don ya tuna musu asalin dalilin zuwansu duniya, da kuma wanda ya cancanta su bauta masa, wasunsu suka ce {Kar ku taba juya wa allolinku baya, kar ku bar Wud, da Suwaa, da Yaguth da Ya'uuq da Nasra...} Sutatu Nuh.
.
Sufyan ta hanyar babansa daga Ikrima RA ya ce "Tsakanin Adam AS da Nuh qarni 10 ne (wato shekara 1,000) kuma dukansu suna kan muslunci ne (Tafseerin Tabari J23 p639; Tafsirin Qurtabi J4 p307-308; Tafsirin Ibn Kasir J4 p426) kenan in mun kula duk wani bawan Allah da zai nusar da kai a duniya in ya mutu tsakaninka da shi addu'a, kai ne za ka roqa masa don in banda sadaka mai gudana bai da komai, in kuma ka koma roqon ya yi maka wani abu to fa an koma gidan jiya kenan, ko hutunan shehunnai da ake liqawa ko ake roqonsu duka dai wani qoqari ne na komawa wancan hanyar ta baya.
.
2) Magana ta biyu kuwa ita ma shahararriya ce daga Ibn Abbas din wace yake cewa: "Wadannan gumakan suna dauke ne da sunayen mutanen kirki, bayin Allah na gari daga cikin al'ummar da Nuh AS ya rayu, Buhari ya rawaito daga Ata' daga Ibn Abbas din inda yake cewa " Gumakan da mutanen Nuh AS suka riqa bauta mawa sun shiga hannun Larabawa daga baya, Bani-Kalb a Dumatu-janda suka riqi Wud, Suwaa kuma na Huzail, sai Murad ne daga baya kuma Banu Gutaif a Saba suka dauka, Ya'uuq kuwa na Hamdan ne, sai Nasr a Humair da Aal Zil Kala suka riqa.
.
Ba shakka sunayen bayin Allah ne mutanen kirki wadanda su ma jama'ar da Nuh AS yake ciki ne, da suka shude sai Shedan ya riqa hure wa mutanen bayansu kunne ya ce su yi gumaka a wuraren da suke zama su sanya musu sunayensu, suka yi din kuwa, amma ba su bauta musu ba, sai da wadanda suka yi din suka qare masaniyarsu da bayin Allan ta wuce sai aka fara bauta musu (Tafsirin Ibn Kasir J4 p426; Qurtabi J9 p308)". Duka dai za mu ga cewa musluncin ne farko, mutanen kirkin Allah suke bauta masa ba su damu da kowa ba shi ya sa ba a ambaci wani kafinsu ba a ce da shi aka dogara sai dai su din.
.
Su ma fa don ba su riqi wani dan adam suna yi masa irin abinda aka riqa yi musu bayan mutuwarsu ne ba, sun tsaya ne suka bauta wa Allah wanda hakan ya ba su wannan girman a idon jama'arsu, to har zuwa wannan lokacin muslunci ne a sama, shi yake jagorantar jama'a kuma shi yake shiryarwa, daga lokacin da aka fara fadin cewa gumakansu da aka ajiye a majalinsu suna da matsayinsu kuma za su iya taimaka wa bawa ya isa ga Ubangiji lokacin addinin ya fara rauni abubuwan da suke samu a wurin mahalicci suka fara daukewa har sai da Allah SW ya turo manzon farko wato Nuh AS don ya jawo hankulansu.
.
Manzon ya ce musu {Ku nemi gafarar Ubangijinku - shi maigafara ne- zai ba ku ruwan sama a wadace, ya yalwata muku dukiya, da 'ya'ya ya ni'imta ku da lambuna da koguna} Suratu Nuh, ya ja hankulansu da hujjoji na ilimi wadanda in dai qwaqwalwa na da lafiya za ta dauka, amma suka qi ji suka ba wa kafurci damar da ya shiga gaban muslunci, sai da Allah SW ya halakar da su kafin jagorancin da muslunci ke riqe da shi ya dawo, ashe dai ba mutum ke dawo da shi da qarfin tuwo ba, Allah ne mahalicci ke dawo qarfin musluncin ya ji qan bayi da shi.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248