JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 04
.
1) Tarihi ya tabbatar da cewa Annabi Nuh AS shi ne manzon farko da Allah SW ya fara aikowa.
2) Ya fi kowa dibar shekaru yana kira zuwa ga Allah amma ba wanda ya yi imani da shi sai 'yan mutane qalilan.
3) Hatta a cikin gidansa ya yi fama da qalu-bale, matarsa da 'ya'yansa.
4) Ga nuna yatsa da hantara gami da kashedi, suka ce {Nuh In ba ka rabu da mu ba tabbas za mu jefe ka} Suratus shu'ara.
5) Ya damu matuqa da halakar yaronsa, ya yi duk abinda zai iya amma abin ya ci tura.
.
Zancen gaskiya ko a wannan lokacin muslunci ya ci babbar nasara, domin an riga an danqwafe shi, kusan ma ba shi ake magana ba, ko da Nuh AS yake kiransu suna ganin shi ne ya zo da sabon abu yake qoqarin batar da su, duk gaskiyar da zai fada musu ko ya nuna musu ya gabatar musu wace a qarshe ya yanke qauna har ya yi addu'ar Allah ya halakar da su kawai, amma fa muslunci ya dawo da qarfinsa kamar yadda yake a da, Allah SW ya kawar da kafurcin tare da kafurai.
.
Sai ya zama babu sauran kowa sai musulman da Allah ya kubutar a jirgin ruwa, qarfin muslunci ya dawo ya zama shi yake jagoranci a bayan qasa kamar yadda tun farko shi din ne a gaba, Allah SW kan daukaka muslunci ne tare da musulman, kamar yadda yake qasqanta kafurci tare da kafurai, da ya so ba manzo zai turo ba, sai ya tashi wasu a cikinsu su riqi makamai su ce dole muslunci ne zai yi rinjaye a bayan qasa, don haka kowa ya dawo cikinsa ko kuma a kashe shi.
.
Amma Allah SW bai yi haka ba, sai ya turo manzo, manzon ya zauna a cikinsu, ya yi takiransu a boye da sarari, har toshe kunnuwansu suke yi wai ba sa son jin maganarsa, sai izgili suke masa a kowani lokaci, amma ya yi haquri, haka dabi'ar masu da'awa take, haquri suke yi a kowani lokaci sai Allah SW ya ba su abinda suke nema, dubi dai yawan shekarun da ya kwashe amma tarihi bai rawaito mana cacan bakin da ya yi da wani kafuri ba bare a kai ga maganar fada ko kisa.
.
To ko a zamanin Nuh AS Allah SW ya hallaka kafurai, ya karya taurin kai da wuce gona da iri, ya amshe qarfin mulkin da suke taqama da shi ta wurin hallaka su, ya dawo wa Nuh AS da shi, qasar ta dawo ta musulmai masu bautar Allah shi kadai (Haqiqatul Intisar na Dr Nasirul Umr p38-39). Kenan akwai dama da masu kira zuwa ga Allah za su ci gaba wurin amfani da juriya da haquri da sanya hikima har Allah SW ya kawo musu dauki ta yadda zai dauki mataki da kansa.
.
Allah SW ya sauko da Adam AS ne kawai da matarsa, amma a hankali ya cika duniyar da wannan al'ummar na tsawon shekara dubu, a lokacin da suka kafurce suka saki addininsa sai ya cika alqawarinsa na cewa zai cika haskensa koda mushrikai sun qi, sai ya kawar da su lokaci guda ya tabbatar da hasken nasa ta wurin hallakar da kafuran da dawo da Annabi Nuh AS, duk da cewa wadanda suka kubutan ba su da yawa amma sun sake cika duniyar sannu a hankali, muslunci ya sake dawowa da shugabanci.
.
ABUBUWAN DA ZA MU KOYA
1) Muslunci ne farko a bayan qasa, kafin kafurci ya zo.
2) Sakin bautar Allah ke sa shedan ya sami damar shigo wa jama'a.
3) Adana hutunan malamai da ba su wata girma ta masamman zai sa daga baya wasu su zo su fara bauta musu.
4) Sakin bautar Allah ke kawo nasarar kafurci a kan muslunci.
5) Haquri wurin bauta wa Allah shi kadai da goce wa kiran wani in ba shi ba.
6) Yin amfani da hikima wurin da'awa ba zage-zage da cin mutinci ko kisa ba.
.
7) Bari wa Allah aikinsa na ladabtar da wadanda suka saba masa, don sunnan magabata kenan, ba wai a shiga masallaci ko kasuwa a yi kan mai-uwa da wabi ba.
8) Gasgata alqawarin Allah na kawar da kafurci a kowani zamani da tabbatar da imani wurin bautarsa.
9) In dai za ka tsaya a turbar Ubangiji za ka yi fama da jarabawoyi daga mutanen dake zagaye da kai.
10) Yawan mabiya a lokaci guda ba ya nufin gaskiya kan abinda aka dogara.
11) Qauracewar jama'a ba ta nufin shikenan mutum ya gaza don haka ya dena kira zuwa ga Allah.
12) A duk lokacin da za ka kira mutane zuwa ga Allah shi kadai za su ce kai ne ka zo da sabon abu kuma za su yaqe ka.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248