AZUMIN YAU NA DUKA 😢

AZUMIN YAU NA DUKA 😢



_Haba Dan uwa! Ina imanin?_

Zan yi amfani da wannan damar don in tunatar da 'yan uwa game da wani al'amari da ya zama ruwan dare ga musulmai a social media a lokacin azumi.
.
Da zarar an fara azumi, sai ka ga yan uwa (musamman Matasa) an fara post a kan azumi na wahalarwa, wasu ma sai su mayar da abin jokes don a yi dariya.
.
Haba dan uwa, 'Yar uwa! Ibada fa kike ba wasa ba.
.
Ko dama azumin don riya kike ba don Allah ba?
.
Abu ne sananne cewa duk wanda ya dauki lokaci mai tsawo be ci abinci ba dole ne ya ji yunwa ko kishirwa. To meye amfanin posting, hakan shi zai sa yunwar ta ragu?
.
Wallahi! Mu yi hankali da riya za ta iya ruguza mana ayyukan mu, mu sha yunwar banza, ba lada ba la'ada.

Mu yi hakuri, Allah Ya farlanta azumi ne a kanmu domin mu samu Taqawah kuma ya fi mu sanin halin da muke ciki.

Shawarata ce wannan gare ku 'yan uwa. Kada mu bama Kafirai damar cin zarafin mu.
.
Allah Ya amshi ibadunmu. 🤲🏽
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*08166650256.*
*28-05-2018.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
Post a Comment (0)