KUNUN KUSKUS



*🥘GARKUWA RAMDAN KITCHEN*🥘🥙
            *DAY 2*

KUNUN KUSKUS

Abubuwan haÉ—awa

1-Cous-cous
2-Sikari ko zuma
3-Madara
4-Tufa
5-Ayaba
6-Filebo na banila

*YADDA AKE HAÆŠAWA*

_Ki sami madarar gari ko ta ruwa, duk wadda ki ke da ita, idan ta gari ce sai ki kwaɓa ta da ruwa ta yi tsululu sai ki ɗora akan wuta, idan ta tafaso sai ki kawo kus-kus din ki ki zuba a ciki ki ringa juyawa domin ka da ya dunkule. Idan kin zuba iya yawan da ki ke so sai ki cigaba da juyawa har zuwa minti biyar. Idan ya dahu kuma kaurin ya yi miki sai ki sauke daga kan wuta ki zuba sikari, ki yanka tufa da ayaba ki saka sikari ko kuma zuma duk wanda ki ke so, sannan ki ƙara madara, ki zuba filebo mai kamshin banila ki juya shi kenan sai sha._
A sha daɗi lafiya.😋
 

*Hafsat A Garkuwa*✨🌹
08132761212
Post a Comment (0)