KUSKURENA YA YIN DA NAKE ALWALA 02

KUSKURENA YA YIN DA NAKE
                ALWALA


🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*FUTOWA TA 👇*
          *(2)*


*BARIN ADDU'A YAYIN SHIGA BAN DAKI KO FUTA*

    Yana daga cikin kuskure mai girma rashin ambatan sunan ubangiji yayin shiga ban daki, saboda shi zikirin shiga ban daki kariyane ga musulmi daga shaidanu, barin aikata hakan na budewa shaidan kofar saka maka kokonto azuciyarka, shi yasa sunnar farin jakada saw ta gudana akan cewa idan zaka shiga cikin ban daki sai ka nemi tsarin ubangiji daga shaidanu maza da mata. 
    Ibn hajar yake cewa mutum zai fadi hakan ne yayin shiga ba wai bayan ya shiga ba, amma lokacin da zai futa kuma sunnah ta gudana daga abun da ummuna Aisha ta rawaito cewa manzan Allah (saw) idan ya futo sai yace "ALLAH KAYI MIN GAFARA" ma'ana yana fadan haka bayan ya futo daga cikin ban dakin.

🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*MU HADU A FUTOWA TA 03*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
                      *Dalibi mai neman ilimi*
                      *Nazifi Yakubu Abubakar*
                      *(Abu Rumaisa)*
                         🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)