*MUGUN ABOKI...................*
👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬
*FUTOWA TA👇*
*(3)*
*SIFFOFIN ABOKI NA KWARAI*
Akwai wasu siffofi wadanda babu yadda za'ayi aboki ya zama na kwarai ba tare da ya siffantu da su ba siffofin sune kamar haka :
*1- Dabi'antuwa da kyawawan dabi'a :* siffantuwa da kyawawan dabi'u na daga cikin mafi kyawun siffofi ga aboki na kwarai, kuma ya kasance ya nisanci duk kanin munanan dabi'u, domin dabi'a tana yin naso daga aboki zuwa ga abokinsa.
*2- Ambatansa da shahararsa a tsakanin mutane da kyawawan dabi'u:* mutum nagari jama'a zasu san sa wajan nagarta da kyawawan dabi'u ta yadda saboda shi jama'a za su yi wa gabaki daya abokansa kudin goro wajan nagarta.
*3- Fadin gaskiya kai tsaye:* gaskiya abace mai wahalar fada domin ko da mutum yasan gaskiya ka ke gaya masa bata mai da di aransa domin haka halittar dan Adam take, shi yasa masu hikima suke cewa ka zauna da wanda yake saka ka kuka wajan gaya maka gaskiya,domin wata rana zai yi kuka akanka na soyayyah saboda yadda kayi nasara, kada ka zauna da wanda yake saka ka dariya da nishadi baya gaya maka gaskiya domin wata rana zai yi dariya akan ka lokacin da yaga ka shiga cikin matsala, aboki na kwarai baya jin nauyin gaya maka gaskiya duk dacin da zatai maka.
*4- Shi mutum ne amuntacce:* daga cikin siffar aboki na kwarai akwai amana, domin zai kiya ye sirrin abokinsa ya boye shi, kuma zai ki ya ye alfarmar gidansa da iyalansa, amanarsa tana cikin maganganunsa da aiyukansu, yana baiyanawa mutane abun da yake baiyanawa a abayan idonsu dan gane da su.
*5- Mai kiranka ne zuwa ga duk wani alkhairi:* aboki na kwarai yana kiranka zuwa ga duk kanin wani alkhairi da kyakykyawar zuciya, baya maka rowa wajan nasiha mai amfani, duk rashin da din da zatai maka domin yasan yin hakan wajibine a garesa.
*6- Baya hassada:* hassada na daya daga cikin miyagun dabi'u wadanda suke warware nagartar mutum kuma ta cinye kyawawan ayyukansa, aboki na kwarai yana yiwa abokinsa fatan alkhairi da kyakykyawar zuciya, yana jin dadi duk lokacin da yaga abokinsa yana cikin nasara, yana masa fatan dauwama cikin nasara, haka zalika yana mika hannun taimako iya iyawarsa zuwa ga abokinsa domin ya dauwama cikin nasara.
*7- Daukar nauyin abokantaka:* Daukar nauyin abokantaka na daya daga cikin ababe masu nauyi a abokantaka, wanda duk wani aboki na kwarai yake daukarsa , aboki na kwarai baya guduwa daga wajan abokansa ya yin da suke bukatarsa akusa , yana tsayawa tsayin daka akan al'amuransu, baya bukatar wani sakamako akan abin da ya yi musu.
*8- Yana jiwa abokansa tsoran abun da zai cutar dasu* aboki na kwarai yana kishi da jin tsoro ya yin da yaga wani abu zai cutar da abokansa, yana bayar da duk abun da yake tare dashi domin ya karesu daga cutarwa.
*9- Shi madubi ne ga abokinsa:* aboki na kwarai shi madubi ne ga abokinsa zai taimaka masa wajan ganin kansa yaga ne abubuwan da yake na dai dai da na kuskure.
*10- Aboki na kwarai :* ko da yaushe fuskarsa a sake take, harshensa a tausase yake, zuciyarsa abude take, hannunsa a sake yake, fushinsa a kame yake, kuma ya lazimci girmama ga abokinsa, ga bayyana farin ciki gare shi, yana iya bakin qoqarinsa wajan boye aibinsa da munanan ayyukansa, da bayyana darajojinsa ga ban jama'a.
Wadannan sune siffofin da zaka kula dasu kafin ka riki mutum a matsayin aboki domin ka rabauta da abokantakarsa kuma kaci riba.
*UBANGIJI KA NISANTAR DAMU DAGA MIYAGUN ABOKAI*
*MU HADU A FUTOWA TA 04*
*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
*Dalibai masu neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
*(Abu Rumaisa)*
🥏08145437040🥏
*MARYAM HUSAIN ABDULLAH*
*(UMMU HANAN)*
🥏08026799975🥏