KUSKURENA YA YIN DA NAKE ALWALA 06

*KUSKURENA YA YIN DA NAKE*
                *ALWALA*

🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*FUTOWA TA 👇*
           *(6)*


*AMBATAN SUNAN ALLAH A BANDAKI*

   Shima yana daga cikin kusakuran da mukeyi ya yin Alwala kuma sunnah ta zo da bayanin nisantar hakan kamar yadda hadisin Abdullahi bn umar ya zo da cewa wani mutum ya wuce manzan Allah (saw) a lokacin yana fitsari ya yi masa sallama amma bai mai da masa da amsaba. 
   Wannan hadisin yana nuni akan cewa an karhanta ambatan sunan Ubangiji ya yin biyan buqata, haka zalika gaisar da mai atishawa, amsawa mai kiran sallah (ladan) anso ka jin kirta har ka kammala biyan buqatar taka sannan kayi alwala ko taimama sai ka aikata kamar yadda farin jakada (saw) ya yi taimama sannan ya amsa sallamar da akai masa, sai dai malamai sun fitar da wasu abubuwa guda biyu dawowa da wanda ya yi maka sallama da amsawa mai kiran sallah suka ce mutum ya bari har sai ya yi Alwala ko taimama sai ya aikata su idan kuwa yana jin tsoran zasu kufcemasa sai ya fada acikin zuciyarsa kamar yadda yazo cikin littafin *(SHARHUSSUNNAH)*


🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*MU HADU A FUTOWA TA 07*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
         *Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
             *(Abu Rumaisa)*
          🥏08145437040🥏


Post a Comment (0)