MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA ZUWA BAYAN ASUBA, A WATAN RAMADANA ?

MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA ZUWA BAYAN ASUBA,
A WATAN RAMADANA ?



*Tambaya:*

Assalmu alaikum, malam ina da tambaya shin meye
hukuncin matan da za su sadu da mijinsu lokacin azumi,
amma ba za su yi wanka ba har sai alfijir ya fito, shin yaya
matsayin azumin su yake.? Nagode

*Amsa:*

Wa alaikum assalam, ya halatta mace ta sadu da mijinta su
jinkirta wanka zuwa bayan ketowar alfijir a watan
Ramadhana, a zuminsu kuma ya inganta, saboda Annabi
S.a.w yakan yi haka da matansa, kamar yadda iyalansa
A'isha da Ummu Salama suka rawaito hakan, kuma Muslim
ya fitar da riwayar a Sahihinsa a hadisi mai lamba ta: 1874.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

21/05/2016


FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/miftahulilmii

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)