HALIN YAU 1 & 2


🌺 *HALIN YAU*! 🌺


https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/


*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*Ina farawa da sunan Allah, ina neman tsari da rubuta 'Barna! Ina rokon na yi rubutun da za'a 'karu , ayi amfani da shi.Tsira da aminci ga shugaba Annabi(S.A.W.).*

       *GARGADI*
_A kiyayi taba min labari na ta kowacce siga, Hakkin mallakar tawa ce ni ka'dai, Dole sai da izinina kafin a karanta shi a kowacce irin kafar sadarwa, wadda ya shiga hakkin mallaka kuma ubangiji ya isar mini._

          *JAN KUNNE* 
  *Gaba'daya Wannan labarin kirkirarsa aka yi(Fiction)!haka sunaye da garuruwan da ke ciki bana kowa bane, na zabe sune kawai dan 'kawata labarin, dan haka duk wadda yaci karo da abin da ya yi kamacanceceniya da rayuwar sa bada shi ake ba, arashi ne kawai*

         *JINJINA*
_GA MARUBUCIYA_
*FADILA LAMIDO*
*SUGARI BA KI YI FARIN BANZA BA*.


    *SADAUKARWA*
_Tun daga farkon labarin har zuwa karshen sa gaba'daya sadaukawa ne ga shugaban kungiyar_ *LAFAZEE WRITERS*
*SADIQ ABUBAKAR*.



                 1-2




Harabar makarantar kwana ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Kiyawa (FGC Kiyawa), cike take mak'il da motoci da jama'a kama daga iyayen yara, da su kansu daliban rukuni-rukuni, gungu-gungu, cike da walwala sai ciye-ciye ake yi kasancewar yau ake ziyarar dalibai (visiting day).

Daga can gefen lambun makarantar, wata matashiyar uwa ce da a 'kalla ba za ta wuce shekaru talatin da biyu ba. Zaune take kan lallausar darduma wacce da alamu da ita ta zo, gefenta kulolin abinci ne da kuma ledoji masu dauke da tambarin *Sahad Store.*

Zaune take tana baza ido ta ga ta ina tilon dan'ta zai bullo, ba ta ankara ba ta ji an rungume ta tare da ambaton "Mamiii!"

Cike da dariya ta dago kai.

"Jawad wai ba ka san ka girma ba ne? ba don a zaune nake ba ai da ka kayar da ni."

 Ya sake komawa ya kwanta a jikinta tare da cewa,

"Nayi kewarki Mami! Ina Inna?".

"Ta ce, a gaishe ka, shekaranjiya ta tafi Gamawa biki"

"Ki ce ba ta yi mini girebar ba kenan?" Ya fada cikin turo baki irin na sakalan yara.

"Wace ita? Ai ranar Laraba yini ta yi tana hidimar girebarka, bata samu sukuni ba sai da ta kammala."

Sai a lokacin ya saki fuskar yana cewa,

"Allah Sarki Innata!" Ya tashi a jikinta ya ci gaba da cewa,

 "Ina yini?"

Ta amsa tana bin sa da kallon mamakin irin girman da ya 'kara cikin lokaci 'kalilan da ba ta gan shi ba, tana mamakin inda ya sami girman jiki tun da dai daga ita har mahaifinsa ba wani girma ne da su na a zo a gani ba, hasalima in ba ka sani ba cewa za ka yi 'kaninta ne.

"Kai Mami sai kin gano munina!".

Ya fada yana rufe idonsa da hannuwansa. Ta yi murmushi,

 "Girmanka ne yake ba ni mamaki Jawad ka kerewa tsawona fa!"

"To, Mami aike tsayinki kadan ne, ni kuma irin tsayin Babana na yi."

"A'a, kai kam sai ka fi shi tsayi duka-duka fa watan jiya ka yi sha uku amma ka zan'kale haka!"

Cikin shagwaba ya fara fadin "Haba mana Mami ki daina fada, kar ajiyo. I am 15 fa!"

Ta kwashe da dariya tare da cewa 
 "Mantawa na yi ashe ka fi ni sanin ranar haihuwarka?".

Daidai lokacin ya zuge Jakarta ya dauko tsaleliyar wayarta ya mik'a mata, ''Bude mini na kira malam na ji ko ya dawo."
Ba ta ce uffan ba, ta karba ta bude masa kamar yadda ya bukata. Lambobi ya shiga daddanawa har ya jera lambar da ke adane a 'kwa'kwalwarsa a cikin wayar ya danna kira ya kara a kunne, tamkar da ma jiran kiran ya shiga ake yi, ya ji an dauka ba tare da ba ta lokaci ba, sallama ya yi tare da fadin,

 "Malam!"

Daga cikin wayar aka amsa da, 
"Jawad kana lafiya? Ka gan ni nan ina kan hanyar zuwa wurinka." 

Cike da murna yace. "Ka dawo daga Bauchin ke nan?"

"A'a ban dawo ba yanzu dai nake kan hanyar dawowa na iso Babaldu zan biyo ta Dutse na iso Kiyawa."

Dadi ya kama Jawad, ya shiga masa addu'ar isowa lafiya, tare da cewa, "Ina wajen da muka zauna a waccan ziyarar."

Ya kashe wayar yana cewa "Oh! Allah ya so ni, jiya fa da na yi masa waya ha'kuri ya ba ni akan ba zai sami zuwa ba sai satin sama, saboda yana Bauchi, ko don bai ji na amsa masa na ha'kura ba ne, shi yasa ya bar komai ya taho?"

Ita dai ba ta sa masa baki ba har ya kammala maganarsa.
tana nazarin lokaci a agogon hannunta daya nuna 'karfe biyu har da mintuna talatin da biyar. "Ko ina ne Babaldu kuma? Ko har zai iya isowa kafin hukumar makaranta ta rufe shigowa?"

Tabe baki ta yi tana ji a ranta to ina ma ruwanta? Amma wani sashi na zuciyarta na fada mata saboda Jawad ne, ina mama ba wadda ya zo mini? Ya katse mata tunani,

"Baban Khalifa ne ba lafiya yana asibiti ka ga ai bai kamata na yi maganar mu taho tare da wani cikinsu ba."

"Me ya same shi?" Ya tambaye ta cike da nuna damuwa.

"Malaria yake ta yi har ta kada shi."

"Muma Mami ita ake ta yi anan, Allah ya sauwa'ke ya bashi lafiya, to yanzun a tasha kika sauka?"

Ta girgiza kai tana cewa, "Shatar mota muka dauko ni da iyalan gidan Ma'aji. Ka ci abincin sai mu je ku gaisa, suna can gefen mata."

Bayan La'asar ba da jimawa ba, ya iso cikin makarantar sanye yake cikin tsadadden yadi fari 'kal! 'Kafar shi dauke da takalmi cover ba'ki, kansa cike da gashi, ya dora hular zanna-bukar wadda ba ta rufe gashin ba, 'kamshin turaren Versace ke tashi a jikinsa.
A hankali yake tafiya cikin nutsuwa, matsakaicin jiki ne dashi, amma dogo ne yanayinsa daya da tauraron wasan kwaikwaiyon nan Yakubu Muhd, ba yadda za ka yi ka kalle shi ka ce shi ya haifi Jawad, sai dan tsananin kamar da Jawad ke yi da shi.

Tun kafin ya'karaso Jawad ya hango shi, don haka ya kwasa da gudu ya nufe shi. 
Ga mamakin Sa'adah, sai ta ga ya 'daga Jawad cak ya yi juyi da shi tamkar yadda yake masa yana yaro. 

Ya dire shi, ya ru'ko shi ta gefen shi suka doso ta, wadda duk ilahirin mutanen dake wajen sai da suka bi su da ido suna sha'awar Jawad da Babansa.

Kujera ya samo masa ya zauna daga gefe, amma ba wani tazara da inda Sa'ada ke zaune, ta juya musu baya. Hira suke cike da doki.
"Amma anya Jawad kana karatu kuwa? Ina *C.A* Result dinka?" Ya zura hannu a aljihun wandon shi ya zaro takarda ya mika masa ya karba ya bude yana dubawa, fara'arsa na 'kara fadada, ya ninke ya kalli dan nasa ya ce, "That is my boy weldone! Ka ci gaba da dagewa."

"Ni da zan zama direban jirgin sama, ai dole sai na yi karatu Malam, ko ka manta?"

"Murmushi kawai Malam din ya yi yana satar kallon gefen da Sa'adah ke zaune kamar ko yaushe ta ci kwalliya ta burgewa cikin tsadadden leshi doguwar riga(bubu), hannayen ta sun ci jan lalle da zobunan Dubai Gold, 'kamshinta na dindin na turaran Escada sentiment, turare na mussaman mai sau'kar da nutsuwa ga duk wadda yake shakar shi, sai kai wa hancinsa ziyara yake yi.
Ta sake zamowa yar yarinya, ta fi kama da 'yan shekaru ashirin da biyar ba wadda ta ba wa talatin baya ba.
Jawad ya mi'ke yana cewa, "Malam Ina zuwa.''

Kai kawai ya kada masa, kai tsaye uwarsa ya nufa, gabanta ya tsugunna ya ru'ko dukkan hannayenta,

 "Mami ki zo ku gaisa da Malam mana"

Kai ta girgiza masa alamun ba za ta ba.

"Haba Mami gaisuwa kawai?"

Kan ta sake girgizawa a karo na biyu, tana ci gaba da latsa wayarta a cikin manhajar WhatsApp inda abokan tafiyarta suka ce mata ya kamata su ta fi haka nan, kar su yi dare. dan haka ta fara tattare warmers din da ta zo da su, tare da mi'ka masa ledojin siyayyar da ta kawo masa, tana sake jaddada masa ya kula da karatu ya kuma kula da ibada, muryarsa na rawa alamun zai yi kuka ya ce mata, "Ba fa ki gai da Malam ba".

A dan tunzure ta ce "Dole ne?"
Ganin kwalla a idonsa sai jikinta ya yi sanyi ta dauki handbag din ta tare da basket mai dauke da kulolin ta ce "mu je to."

Karbar basket din ya yi suka nufi Malam din da tazarar su bai fi taku biyar ba, don haka a kan kunnen shi duk yake jin tattaunawarsu.

 Ba ta isa daf da shi kamar yadda Jawad ya yi ba, ta tsaya daga dan nesa ta ce, "Ina yini?"
 ji ya yi kamar ba zai amsa ba tunda a wulakance ta yi gaisuwar, Irin gaisuwar je ka na yi ka, amma ganin Jawad ya zuba musu ido, sai ya amsa har ya na tambayar Inna, wanda ta ji shi, amma sai ta yi kamar ba da ita yake ba. Hannu ta mikawa Jawad akan ya ba ta basket din, no'ke kafada ya yi tare da cewa!

 "Mami, Malam fa Kano zai wuce, don Allah ki bari ku wuce tare."

Wani malolon ba'kin ciki ya sa ke turnuketa, bayan ya tilasta ta, ta gaishe shi, ya kuma sake baro wata magana.

Ba ta ce masa komai ba ta fincike basket din tana cewa,
"Na gode ba sai ka kara gani na zo ba bare ka yi mini wannan iya shegen!"

Ta juya ta fara tafiyarta mai cike da nutsuwa, da sauri Jawad ya bi bayanta, yana cewa, "Haba mana Mami kar mu yi haka da ke!"

Kawai sai ta saki basket din hannunta da jakarta ta riko shi ta ringa zuba masa rankwashi tare da dundu, a sukwane Uban ya taso ya karbe shi yana jin takaicin ta na sake kama shi, wai a makaranta ma cikin jama'a ba za ta fasa halinta ba? Sa'arsa daya ma, wajen ba mutane kusan duk an watse sai tsirarru.

Ta sunkuya ta debi kayanta ta tafi tana huci, ganin haka Jawad ya fincike daga hannunsa ya bi ta yana fadin,"Ina zuwa Malam!"

Da gudu ya cim mata ta baya ya rungeme ta yana fadin,

 "Am sorry Mami, very sorry!"

"Ai ni kuma ba ruwana da kai Jawad, tun da dai kai ba ka jin magana, na hana ka wannan manyancen naka, na hana ka shiga abin da bai shafe ka ba, amma ka 'ki, to ka je ka yi ta yi."

Ya marairaice yana ba ta ha'kuri har dai ya samu ta ha'kura ya ga murmushinta.

Malam yana zaune yana kallon su har suka ba ce ma ganinsa, a ransa yana mugun tausaya wa Jawad, tun da shi burinsa a ce Mamansa na tare da su, wadda faruwar hakan sai ikon Allah.

Yana zaune, ya dawo ya tarar da shi yana ta tunani, "Ni ma ai zuwa zan yi na tafi. Mu je mota ka kwaso kayanka."

Daidai lokacin wayarsa ta dauki ruri, yana dubawa yaga matarsa ce Farida ya amsa, tambayar Jawad ta yi, wayar ya mi'ka ma yaron tare da cewa, "Karbi!" 

Ba wani karsashi ya karbi wayar har ita ma ta ji babu dadi tana tambayar shi ko lafiya ya ce mata, "Lafiya lau!" Bana son Malam ya tafi ya tafi nee, sannan baku zo ba ke da Hajiyan Bichi".
 ta shiga bashi hakuri cike da murna ganin ya fara dawo mata tamkar farkon zamansu.

Suna tafe yana masa nasiha tare da nuna masa ba ayina uwa ba a yin musu da ita, dole a bi ta yadda take so, sannan ya daina shiga matsalar da ba tashi ba, hawaye yake gogewa tare da cewa, 

"Ni dai Malam ka dawo da ita gidanmu ni ma in dinga ganin Mamana a gidanmu, kamar yadda nake ganin na friends dina, kowa Mamansa da Babansa tare suke zuwa masa amma banda ni!"

Ya 'karasa cikin kuka sosai, janyo shi jikinsa ya yi yana dan bubbuga bayansa alamun rarrashi yana cewa
 "Ina ce ni ma tare da Antinka nake zuwa maka?"

"Amma ai ba da Mamana kuke zuwa ba!"

"To ka kwantar da hankalinka, ka dinga mana adddu'a sai ka ga very soon ta dawo har ma ka zama Yaya Jawad kana so?"

Ya daga kansa tare da sa hannu yana goge hawayen da ya'ki tsayawa.

"To in dai kana son haka, ka daina damuwa ka kuma daina yiwa Mami maganar bare ta dake ka, kawai addu'a za ka na yi, ni kuma ka dinga tuna mini, wataran sai dai ka dawo hutu ka ganta a gidanmu."

 "Malam da gaske?" ya tambaya cike da zumudi.

"E Mana indai ka daina kuka, ka daina damuwa, ka daina damunta, kana addu'a to ina tabbatar maka ba abin da ya fi addu'a juya lamura!"

Murmushi ya shiga yi yana goge hawaye da handkerchief din hannunsa yana 'fadin,
 "Ai ko Malam ban san murnar da zan yi ba,, kuma har da kai zan 'dauka a jirgin nawa".

Dariya Mk ya yi tare da cewa "Ai kuwa dai nima naji dadi tunda albakacin Mami zan shiga jirgin Jawad"
Kunya ta kama yaron yace "Ai dan ita bata taba shiga bane"

Ya sake cewa, "Malam ka gai da Hajiya, kuma ina zuba idon zuwanta, tunda ba ta zo yau ba, ina bin ta bashi!"






  Alkalamin
 Surayya Dahiru ✍️
Post a Comment (0)