MIJIN ƘAZAMA 03

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•

      
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀    
           *MIJIN KAZAMA*
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

             *Na*                            

          *Maman Hafiz* 
        
                  *Niger*


*Bismillahi Rahamani Rahim*

*Page 3*

Bayan momynsa ta fita ya ci gaba da aikinsa ya kammala, daki ya rufe ya kwanta, addu'ar barci ya yi ya shafa.

Washegari tun da wuri ya tashi ya gama shirinsa tsaf ya fesa turare, kiran momy ne ya shigo a wayarsa. "Hello momy an tashi lafiya?"

"lafiya kalau ka zo mu yi petit déjeuner."

"Ok momy na gama shiryawa gani nan!" 

Kashe waya ya yi, ya saka a aljihunsa ya dauki jaka ordinateur dinsa ya fita. Sashen iyayen nasa ya nufa can yake petit déjeuner, mai aiki ta gama shirya abinci kamshi sai tashi yake da ka tun kari wajan table din, shigowa ya yi bakin sa dauke da sallama, a tare suka amsa masa cikin nuna so da kauna na tilo dan nasu

Gaishe su yake cikin ladabi, amsa masa suka yi daddy ya ce, "Ashe ka gama shiri? Na zata ma ka koma barci bayan sallar Asuba."

" Daddy aiki gare ni mai yawa a ofis shi yasa zan tafi da guri don in kammala." 

"Allah ya taimaika." Daddy ya fada. 

''Amin" Ya amsa masa  

Abincin suka fara ci suna dan taba hirar su har suka kammala. Sallama ya yi wa iyayen nasa ya fito ya nufi motarsa kirar V8, maigadi ne ya nufo sa, gaishe sa ya yi cikin girmamawa. Amsa masa ya yi ya koma ya bude masa gate. ficewa ya yi cikin tukuinsa mai nutsuwa.

Amina ce kwance a dakinsu chatting take da saurayinta da ta hadu da shi a Facebook, soyayya suke amma ba su taba ganin juna ba. *Ko waye wannan?* Muje zuwa dai.

Hira suke cikin jin dadi kamar suna tare da juna, suna yi suna dariya, soyayya gwanin ban sha'awa. Ba su taba ganin juna ba amma idan suna hira ka ce sun san juna.

Hanane ce ta shigo ta isko ta tana dariya, kallon ta ta yi ta ce, "Ya Amina me kika samu ne haka kike dariya ke kadai?" 

"Sadik ne ke ba ni dariya Hanane."

Murmushi ta yi ta ce, Allah Sarki Sadik ya kamu da son ki ya Amina amma duk ranar da ya san halinki zai fasa son ki."

"To ta ya zai gane halina? Shi da ba garinmu daya ba? Tsaya ki ji Hanane ni fa ba 'yar wahala ba ce, fatar jikina ba ta yi kama da fatar 'yar wahala ba. Kin sani ba wai aikin ne ban iya ba kawai hutu ne nake so shi yasa kika gani komai ba na son yi daga salla sai cib abinci. Ko zuwa école ma da nake yi don ya zama tilas ne, Baba ba zai bari ba na fasa. Abincin ma ya zama tilas ne nake cin me nauyi, idan da hali da chocolate da wainar kwai da frite da dai dan kayan fruits da su zan rika ci, amma idan na auri Sadik na san zan cika burinna In Sha Allah."

"Allah Ya taimaka yaya ni ma ina son aurenku da shi. Amma dai ki canja hali, kazanta ba abin yi ba ce."

Wani kallo Amina ta bita da shi, Hanane ficewa ta yi daga dakin, hirarta ta ci gaba da yi tana yi tana dariya  

Sadik ne a Bureau (Office) bayan ya kammala aikin nasa ne ya shiga chatting da budurwarsa da ya kamu da son ta, bai taba ganin taba sai a waya da ta turo masa da hotunanta, yana jin dadin hira da ita. Sosai yake nishadatuwa da firarta.


*Maman Hafiz*✍️

Post a Comment (0)