🌺 *HALIN YAU*! 🌺
https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
*Tukuici ga*
*FADILA LAMIDO*
*BINTA UMAR ABBALE*
*ZAINAB MAZAWAJE*
*Nagode da Shawarwarinku da 'karfafa guiwa, Allah Ya saka muku da alheri, Ya 'kara daukaka.*
*GODIYA GA MAKARANTA*
*Na gode da yadda kuka 'karbin wannan labarin, ha'kika jiya na ga ruwan masoya, ban yi zaton a 'kankanin lokaci littafin zai 'karade duniyar karatu haka ba, na gode muku sosai, in sha Allah ba za ku yi NADAMAR bibiyar wannan labarin ba!Heart U all*
3-4
A sanyaye ya fito wa da Jawad kayayyakin provisions din da ya kawo mishi, tamkar wanda zai yi rabin shekara bai je gida ba, yana sake jaddada mishi ya daina damuwa ya kuma ci gaba da karatunshi.
Ya shiga mota Jawad na 'daga mishi hannu har ya fice, bai yi nisa sosai ba don kuwa bai gama barin garin Kiyawa ba, ya hango su Sa'adah da wasu matan a waje, gefe kuma an bude motar bakanike sai tabe-tabe yake, ga dukkan alamu motar ce ta lalace musu, kamar ya wuce sai kuma ya kasa.
Don haka sai ya tsaya a gabansu, bai fito ba, sai ya lalubo lambar da Jawad ya kira shi da ita dazu, ya san tabbas layinta ne duk kuwa da ba ainihin layin ta ba ne daya santa da shi.
Ya danna alamar kira, yana hango ta tana ta kici-kici da jakarta wurin lalubo wayar, amma abin mamaki ya ga ta fito da wayar amma ba ta dauka ba har ta katse, mamaki ya kama shi wai yaushe Sa'adah ta ko yi jarumta akan lamarinsa ne?
Ya yi jim yana tunanin rabon da Sa'adah ta shiga harkarsa, ba shakka ba lokaci ne Mai tsayi, ba ta sake neman shi ba, ba ta sake duba dukkan lamarin sa ba, ta yi fatali da shi da dukkan soyayyarshi, abin da ya dade yana mamakinsa. bai daddaraba, ya sake 'kira tana gab da tsinkewa ta daga ba ta yi magana ba, amma dai ta kara a kunnen ta, sanin halinta da ya yi na ba za ta fara magana ba, yasa shi cewa,
"Ke na gani a titi a na muku gyaran mota?".
Cikin rashin nuna damuwa ta ce "A a ba ni ba ce."
Bai yi mamakin amsarta ba ya ce. "Amma ba ke ce nake hangowa a tsaye kina amsa wayar nan daidai jikin Alheri bread🍞 ba?"
Shiru ta masa sai ji ya yi ta ma ka'tse wayar gaba'daya.
Shiru ya yi ranshi na suya ya na sake jaddada halayyarta a jininta ne ba za ta sauya ba.
Har ya ta da motar da niyyar barin wajen ta je ta 'karata, sai kuma ya tuna uwar Jawad ce tilon 'dansa, ya tabbatar da tare yake da Jawad din, ba zai yarda su tafi su bar Maminshi a bayan gari jejin Allah ba, ga yamma ta yi likis sosai, sanyin da ake 'dan busawa ya sake taimaka wa garin ya yi dan duhu, don haka sai ya fito bayan ya kulle motar ya nufe su.
Yana zuwa ya ga har da Zainab Ma'aji da wasu mata biyu da bai gane su ba.
Ita ko Zainab tana ganin shi ta saki fuska."Lah! Uncle kai ne ashe."
Ta gaishe shi irin gaisuwar da dalibi ke yi idan ya ga malamin da ya koyar da shi a baya. Shi ma ya amsa da jin dadin girmama shi da Zainab ke yi tun fil azal.
Hannu ya mi'ka ya dauki yaronta Walid ya masa wasa sannan ya ce, "Motar taku lalacewa ta yi ne?".
"E wallahi ga mu nan dai ana ta faman gyara".
"To ku zo mana mu wuce tun da ba tabbacin za ta gyaru yanzu".
Kallo ta kai ga Sa'adah da ta koma baya ta yi kamar ba ta gan shi ba, ta kuma cika ta yi fam kamar kububuwa.
Zainab ta ce "To uncle bari na yi wa abokan tafiyar tamu magana."
"Okay"
Kawai ya ce, yana ci gaba da wasa da Walid dake ta bingila mishi dariya tamkar ya san shi.
Bayani Zainab ta musu kamar yadda ya bu'kata, dukkan su sun amince, su bi shi, amma ban da Sa'ada. Don haka Zainab da 'yan uwanta su ma suka janye tun da dai ai sun san saboda ita ya tsaya har ya nemi ya taimake su, to kuwa ta ya ya za su ce za su bi shi alhalin ita ta yi rantsuwar gara ta kwana a nan da ta shiga motarsa!
A matu'kar kunyace Zainab take ba shi ha'kuri tare da ba shi uzirin direban ba zai ji dadi ba, ya san sarai Sa'ada ce ta'ki amincewa, amma sai ya ce ai zan sallame shi ku zo mu tafi kawai.
Nan ma sai ta sake dora wa 'yan uwanta laifi akan yayarsu tace ba zasu sab'awa direban al'kawari ba. Ya jinjina hankali da Zainab ke da shi, duk da ya san 'kawar ta ce ta'ki amincewa, amma ba ta fadi hakan ba, sai kariya take ta bayarwa, ina ma tun farko Sa'ada ita ta ri'ka a matsayin 'kawa, ba bara gurbi irin su Halima da Safina ba?
Wanda 'kawacenta da su bai amfane ta da komi ba sai muguwar asara da nadama, tunda sun mata ingiza mai kantu ta yarda har ta tsinke igiyar aurenta, a yanzu kuma sun bar ta sun koma suna zunden ta.
Don haka sai yace "To shi kenan ba damuwa ya matsa ga bakaniken dake ta iyakar kokarin shi don ya ga motar ta tashi.
magana suke yi da direba, cikin ikon Allah ba a wani dauki lokaci sosai ba motar ta gyaru, amma har an yi sallar Maghriba, dan haka malam da direban suka yi jam'i suka yi sallarsu, yayin da matan suka shiga wani kewaye su ka yi ta su.
Bai yarda ya tafi ba sai da ya ga tashin su sannan ya taka ya isa inda motarsa take shi ma ya bi su a baya.
A cikin motar kuwa yayyen Zainab sai caccakar Sa'ada suke da rashin kirkinta, "A haka kike son komawa gidan nasa? Ba kya girmama shi, a gaban kowa za ki iya keta shi?"
Cikin turo baki ta ce "Ni fa Anty da ne na yi haukan banza na son sai ya mayar da ni, yanzu kuwa ko ni da shi muka rage ba na sonsa ba zan koma ba"
Cikin fushi ita ma Anty Asiya wadda ita Zainab ke bi, kuma da ita duk a ka yi gwagwarmayar su Sa'adah, ta ce, "Ai shima ba son naki yake ba, shashasha da ba ta san me ya kamata ba."
Dattijon dake jan motar ya ce, "Um'um fa! Ba'a shiga lamarin mace da namiji, ai koni da yau na fara ganin su na hango soyayyarta mai yawa a idonsa da gangar jikinsa, ita ma kuma duk wannan kumburin da take yi da fiffi'ka duk soyayyar ce, da alama dai kishi ne ke dawainiya da ita a kansa, dan na ga fishi take mai tsanani da shi!"
Dukkan motar a kasa dariya a na cewa Baba ashe duk ka gano su?
Yace , "Haba yara mu da muka ga jiya muka yau, ku duba fa duk iya shegen da ta yi akan ba za ku bi shi ba, bai fa iya tafiya ba har sai da ya ga tashinmu, wannan kadai ya isa kowa yasa lunzami a bakinshi akan lamarinsu, suna da yara ne?"
Zainab ce ta ce "Yaro ne daya har ya fara girma, shi suka jewa visiting"
Ya ce, "Ai shike nan magana ta 'kare, ko kowa bai musu sulhu ba, yaron zai zama tsanin afuwa a tsakaninsu, mu yi musu addu'ar fatan alheri, amma soyayya akwai ta"
Aka sake sa dariya ban da Sa'ada da ta yi kicin-kicin da fuska.
Tsohon ya sake cewa, "Ina cewa da za mu zo ita ce a gaban motar nan haka da za mu dawo,har muka zo inda motar ta lalace ita ce a gaban?amma ina ganinsu da za ta shiga gaba ya galla mata harara sai kawai naga ta shige baya."
Gabadaya aka sake dariya har da Sa'ada wadda ita ta karfin halin wannan bawan Allah ne, ita ba ta ga harara ba, ta san kuma tabbas bai yi 'karya ba, kaifin idon Malam ne yasa ta kasa shiga gaban motar wani akan idonsa, sai ta bige da cewa "Lallai Baba ba komi na gode" da haka ta sace ta daina fishi.
Shi ko Malam yana tafe yana ayyana abubuwa masu girma game da lamarin ta, komai nata burgeshi yake, bai ta ba ganin halittar da ke daukan hankalinsa irin surar ta ba, kawai wasu daga cikin halayyarta ke 'dimauta tunaninshi su hana shi zaman lafiya amma duk sanda zai dora idonshi a kanta sai ya ji bai ganin komai da kowa sai ita.
Har yau har gobe yana son ta, amma ta riga ta shayar da shi bakin cikin da zaman aure zai yi wuya tare da su. Har suka iso Kano tunaninta yake idan ya tuna *happy moments* dinsu yayi murmushi, idan ya tuna *though times* dinsu sai ya ja tsaki ko ya furta ya *Salam* ko *SubhanAllah.*
Ba su rabu ba sai da suka zo Gandu ya yi wa direbansu fitila ya wuce, a nan ma sai da Baba ya tsokaneta da cewa
"To Sa'adatu wannan fitilar fa da ya yi bata kowa bace, taki ce!"
Suka hada baki wurin fadin, "Ai kuwa dai Baba!" suna kuma dariya.
```Alkalamin
SURAYYA DAHIRU``` ✍🏼✍🏼