🌺 *HALIN YAU*! 🌺
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}
https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
*SADAUKARWA GA*
*SADIQ ABUBAKAR*.
*ALLAH KA JIIKAN*
_HAUWA M. HASSAN_
*(FINE GIRL)*
_UBANGIJI KA ALBARKACI SU FA'EEZA_.
13-14
Tsawon kwanaki addu'ar za'bin alheri ya dinga yi tsakaninshi da Sa'adah ba 'kak'kautawa, kuma ALHAMDULILLAH, ya ji takurar da yake ji akan zama da ita ta kau, ya sami sau'kin nauyin da zuciyarshi ta yi akan ta.
Ranar Juma'a bayan an sau'ko Masallaci kai tsaye gidan su ya zarce kamar yadda ya saba a falo ya tarar da Hajiya zaune kan sallaya, tana lazimi. Ya jima yana zaune kafin ta shafa addu'arta ta juyo ta kalleshi, a nutse ya shiga gaishe ta tare da tambayar jikinta kasancewar kwanaki biyun nan fama take ta yi da zazzabin cizon sauro.
"Jiki kam na ji sau'ki sai rashin 'karfin jiki wanda sai a hankali."
Ta fada tana daddanna 'kafarta.
"Hajiya 'kafar ciwo take miki ne?" Ya fada cike da kulawa.
Ta ce, "Ba wani ciwo kawai kasala ce!"
"Sannu idan kin gama shan maganin ba ki ji daidai ba, sai na mayar da ke wajen likita."
Da sauri ta ce "Kai raba ni da zancen Likitan nan na ji sauki."
Dariya ya yi! dama tsokanace wannan zazzabin ma da 'kyar ta yarda ta je asibitin bare ta yarda ta koma.
"Har yau ba ka ce mini komai akan maganar Sa'a ba?"
Murmushi ya yi "Oh! Hajiya ai na ga ba ki da lafiya ne."
"A a
na ji sauki "
Gyara zama ya yi sosai ya fuskance ta, "Hajiya!" Ya kira sunanta.
"Na'am!" Ita ma ta amsa tare da mi'ka dukkan natsuwarta gare shi.
"Kamar yadda na ce miki zan yi addu'a, to na yi! kuma na ji tsoro da razanin da nake ji a tattare da zama da yarinyar nan ya gushe daga zuciyata, amma..." Sai kawai jin ta ya yi tana ambaton Alhamdulillah! tausayinta ya kama shi na ganin tsananin murnar da take yi akan abin da ba tabbacin yi yuwar faruwar shi.
Ya san Sa'adah, ta kyautata mata matu'ka. Lamarin da Hajiya ta tattara dukkan kaunar da take mishi ta mi'ka mata, duk irin laifin da za ta mishi tofa a idon Hajiya ba laifi ba ne sai ta ce ai yarinya ce, 'kuruciya ce ba kuma hankalinsu 'daya ba.
Har ya fara yi wa Sa'adah kallon macijiya ta sare shi, ta kuma koma gefe ta lullube uwarshi da alheri, haka nan hatta 'yan uwansa, mussaman Samira da Hafsatu basu dauki lamarin Sa'adah da wasa ba, saboda yadda ta kyautata musu iyaka, ya san ba ta da rowa, tana da saurin sabo, ba ta kuma sa ido a lamarinsa da 'yan uwanshi, komai zai musu kuwa, wani lokacin ma ita take ankarar da shi.
Shi har mamakin ta yake yi yadda duk wani rikicinta, fa'danta, rashin kirkinta, da kuma rashin ha'kuri duk akan shi ya 'kare.
Ta 'dago tana kuma ambaton ALHAMDULILLAH.
"Hajiya abin da nake so ki gane yarinyar nan fa yanzu gaba'daya ba yadda kike zaton ta ba ne, na tana son dawowa 'dakinta, don haka kar ki sa a ranki cewar za ta dawo, azo kuma abu bai yiwu ba, ki zo ki sake shiga damuwa kinsan dai kullum girma 'kara kama ki yake"
Shiru ta yi can ta nisa, "Shin kai a wurinka magana ta wuce ta 'bacin rai ba tashin tashina?"
Ya yi jim, yasan dole sai sun sake baje tashin hankalin da ya gitta a tsakaninsu, kafin a manta shi gaba'daya! Amma sai ya amsa mata da cewa
"Babu Hajiya! amma wallahi bazan ta bin kanta ta amince ba, don na lura yanzu wani iya shege ta ke ji"
Da sauri Hajiya ta 'daga mishi hannu,"Kai da'dina da kai ba ka fahimci yarinyar nan ba, kishi ne ke 'dawainiya da ita, ka duba mana kafin ka yi auren nan wanne irin bibiya ne ba ta maka ba? har kowa ya gane ita ce mai laifi a tsakaninku, duk da ba ku cewa kowa ga yadda abin yake ba".
Ta yi 'kasa da murya, "Yanzu fa duk girman laifinta, kama ta hukuncin da yanzu kai ne mai laifi a tsakaninku tunda ka mata kishiya, abin da nake so da kai, kar ka yarda wani borinta yasa ka yi 'kasa a guiwa, ka lallaba ta ka'dan, ni kuma sai na lalla'ba mana ita da yawa"
Dariya ya dinga yi,"Oh Hajiya saboda Allah ni da Sa'adah wa kika fi so?"
"Ai kai ma kasan ita na fi so! nan kusa za a dade ba'a samu mai girmama uwar miji da 'yan uwanshi irin ta ba. Ina fa ji ina kuma ganin yadda she'danun yaran yau suke wa iyayen mazan su iyashege kala-kala, har sunaye suka la'kaba musu, wai uwar miji ce Ulcer, BP, ciwon kai, da sauran sunaye na tsiya, amma Sa'a bata a cikin wannan layin".
Dariyar ya sake yi tare da cewa, "kun yi dace ne kawai ke da ita wasu laifin iyayen mijin ne ai, da basa 'dauke kai ga harkar gidan ya'yan su maza, sannan basa jan surukan nasu a jiki, basa kuma yi musu sassaci da uzziri.
Wasu kuma tabbas laifin *Matan Yau* ne da suke ganin uwar miji tamkar wata 'yar katsalandan ga rayuwar su sai afara zaman Allah ya kawo maraba. Allah dai ya rufa asiri kawai, amma Hajiya ita Farida fa?"
Da sauri ta ce, "Ita ma ba ta da laifi tana da irin nata alherin, amma..." Ya katse ta da cewa "Ba kamar Sa'a ba ko??"
Dariya ta yi tana cewa "Yaushe zaka je gun nata?"
"Zan je In sha Allah!" Jin yadda ya sau'ko ya kuma amince da maganar Sa'adah a karon farko tun bayan rabuwarsu, yasa bata matsa mishi da yawa ba, sai ta ce, "To ka mayar da hankali don Allah, a yi a gama komai cikin 'kan'kanin lokaci ku dai yanzu ba yara ba ne"
Mi'kewa ya yi yana gyara sakun hularsa tare da cewa, "Ke da kika ce za ki lallaba mana ita, ai ni ba sai na yi komai ba."
Cikin sauri ta furta, "Ai ko tilas kai ne mai magana a farko"
Murmushi ya saki tare da yi mata sallama ya fita yana fadin, "Sa'a ta same ki sosai Hajiya"
Gidansa ya nufa, a falo ya tarar da Farida cikin kwalliya ta burgewa tana zaman jiran shi, ta hau hidimar kawo mishi abinci, da abin sha, sai daya kammala, ta kwashe komai sannan ta dawo ta zauna tana tambayar Hajiya. ya amsa da cewa "Tana lafiya! ta ce a gaishe ki."
Murmushi ta yi tare da fadin "Na gode!"
Hannunta ya riko ya janyota sosai kusa dashi, "Ina son mu yi magana mai mihimmanci, ki nutsu ki ji me zance miki, ki kuma fahimce ni"
Idanuwanta masu sheki ta zuba masa tana jin a jikinta abin da ta dade tana jiran ya tabbata ne yake neman faruwa a wannan karon, kai ta gyada tare da cewa, "Ina jin ka."
Sai kuma ya kasa cewa komai tsawon lokaci, ita kuwa da ke ba mai gaggawa ba ce ba ta ce masa uffan ba.
Har ya gaji ya nisa don kanshi sannan ya ce, "Ba sabuwar magana ba ce mun sha yin ta, sai dai ta yau 'din ta sha banban!"
Nan ma cewa ta yi, "Ina sauraron ka!"
Abin mamaki sai ya ji shakkar furta maganar yake. Cikin dauriya ya ce, "Maganar Sa'adah ce zan fara magana da ita, idan Ubangiji bai 'karar da zaman namu baki 'daya ba, zata dawo "
Gabanta ya fadi duk da a kullum cikin tsammanin faruwar hakan take, amma sai da ta kadu matu'ka da gaske, amma da yake tana cikin jerin matan da Ubangiji ya ba su ha'kuri mai yawa da sanyin hali, da kuma ha'diye damuwa sai ta ce!
"Ai da ma ka sha fada mini a kowanne lokaci idan 'kaddarar zamanku ba ta 'kare ba za ka dawo da matarka, ni kuma na sha fada maka cewa ba zan baka matsala ba hakane?"
Ta tambaye shi, kai ya 'daga mata, "To a yau ma ina tabbatar maka baka da matsala da ni. amma zan ro'ke ka abu daya, na san kana son ta sosai, ni kuma ina son ka sosai, don Allah ka yi mini adalci"
Wani abu ya ji ya tsirga mishi tun daga kanshi har zuwa 'kafarshi. Gaba'daya ya janyota jikinshi yana jin tausayin ta na tsirga mishi a zuci da gangar jikinsa gabadaya.
Cikin murya marar amo ya ce, "Farida a tsayin zamana da ke kin san ina son Sa'adah amma abin mamaki ba ki san ina son ki ba?"
Luf ta yi ba ta amsa ba, saboda yadda take kokawa da zuciyarta da numfashin ta.
"Kai, kishi, bala'i!" Ta fa'da a zuciyarta, ban da haka abin da take da tabbacin zai faru ne, don yana neman faruwa kuma sai ya dame ta? kamar ba ita ce take ta mishi kau'din ya dawo da matarsa ba?
Amma a yau da ya amsa, har ya zauna yana fa'da mata da bakinshi akan zai dawo ita sai ta ji kishin da ba ta yi tunanin zai taso mata ba, ya taso da wani irin 'karfi mai gigitarwa.
Jin ta yi shiru yasa shi fadin, "Ban aure ki akan wani dalili ba sai don ina son ki, ina zaune da ke saboda ina son ki, ina kuma jin dadin zama dake, don haka ba wani abin dazai raba ni da ke matu'kar ba ke ce kika bijire mini ba. Ina son ki Farida irin son da zan iya sadaukar miki da komai, ba abu mai da'di a soyayya irin a so ka da kai da dukkan matsalarka, a mutuntunta ka, a kuma yarda ka isa koda kuwa a zahiri baka isan ba.
Ba abin da baki mini na kyautatawa ba, ba kuma zan manta ba, kar ki yarda ki sa a ranki wai zan juya miki baya akan Sa'adah, kar ki ji a ranki na fi son ta akan ki, ni ban san wacce na fi so ba, wacce duk ta kiyaye mini 'bacin Raina, ta zauna da ni lafiya cikin aminci, ta yarda bazan musguna mata da gangan ba, ba shakka itace zata jagoranci zuciya ta. Idan kuma kina da matsala akan dawowarta fada mini zan iya fasawa, idan har hakan zai fi zama masalaha."
Rungume shi ta yi sosai ta na jin wata irin nutsuwa ta na shigar ta.
Ashe har haka matsayinta yake, ashe darajarta ta kai haka? kai ta hau girgizawa, ta ce, "A a ban da matsalar komai wallahi, kawai dai fargaba nake kar ka canja mini kar ka juya mini baya".
Murmushi ya yi yasan tana da hujjarta tunda an yi hakan a baya, don haka sai ya ce, "Aure ya wuce wasa ba na fatan kuma na rabu da matar aure na akan wata matar, ki cire wannan tunanin don yanzu ke ce matata, zan iya ha'kura da ita, matu'kar ta ce ba za ta zauna da ke ba, ke ko ba zan iya rabuwa da ke akan ta ba"
Sai kawai ta saki kukan da take ta haniniya da shi akan kar ya zubo, ya 'dago ta ya shiga lashe hawayen nata, wanda na tsananin murnar maganganunsa ne ko da ba haka ba ne a zuciyarsa ya nuna mata girmamawa tare da karramawa, ta kuma gamsu yana son ta sosai.
"Ubangiji Ya sanya alheri ya zaunar da mu lafiya, Allah ya 'kara maka lafiya, da bu'din arziki ya kuma hore maka ikon yin adalci"
Amin ya ke ta fa'di tare da jin ba abu mai dadi a duniya irin mace ta gari, mai fahimta, mai kuma ilimi da aiki da shi, don sau tari shedanun matan masu ilimin ne, kawai aiki da shi ne ba sa yi. A fili ya ce, "Ubangiji Ya miki albarka My Feri-Feri, Allah Ya ba ki rabo mai amfani."
Zuciyarta ta yi fes ta na jin dadin wannan addu'ar da yake yawaita yi mata na albarka da samun zuri'a mai albarka.
Suna haka har aka kira La'asar sannan suka mike shi ya yi Alwala ya yi masallaci ita kuma ta yi a 'dakinta.
Bayan ya dawo Masallaci bai shiga gidan ba a 'kofar gidan ya samu gefe ya zauna ya ciro wayarshi ya fara lalubo lambarta, karon farko bayan shudewar lokaci mai yawa, daf da za ta tsinke ya ji ta dauka, Sallama ta yi, ya amsa, sai kuma ta ja bakinta ta tsuke, shi kansa sai al'amarin ya zo mishi a bai bai, cikin 'karfin halin da aka san namiji da shi ya ce, "Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?"
Cike da son ta nuna mishi ba shi da sauran matsayi a zuciyarta ta ce, "Waye?"
Bai yi mamaki ba, dan haka sai ya nufin 'kunsa mata takaici shima.
"Wadda ki ke ta sallar dare ne akansa".
Yana rufe baki ta ce, "Babu wannan halittar"
tare da kashe wayarta.
Zuciyarta na bugawa wai yau mafarki take ne ko kuwa da gaske Malam ne ya kira ta taka nas? Wacce iriin sa'a yau ta tashi da ita? tana tuna kalaminshi na 'karshen maganar su a wani lokaci da ya shu'de, sai ta ji murnarta ta koma ciki, ba za ta saurare shi ba har sai ya janye kalamunshi, da kallon da yake mata, idan ko ba haka ba, to tabbas ba za ta sake mu'amala da shi ba, bare babbar mu'amala irin ta aure, ko da hakan na nufin mutuwarta ne.
Al'kalamin
SURAYYA DAHIRU
✍🏼✍🏼✍🏼