HALIN YAU 11 & 12


🌺 *HALIN YAU*! 🌺



```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/



        *SADAUKARWA GA*
         *SADIQ ABUBAKAR*.




                   11-12



A cikin wannan yanayin Zainab ta yi sallama a tsakar gidansu, sai da ta fara shiga gurin Inna ta gaishe ta, ta bar mata Khalifa, ta yi dakin Sa'adah.

Zaune ta same ta kan katifarta hannunta ri'ke da littafi da biro.

Gefenta ta zauna tana fadin
 "Nazari kike ne haka?"

 "A sanyaye tace 
"Wai nan littafi zan rubuta amma na rasa ta inda zan fara."

Dariya Zainab ta yi tare da cewa, "Sa'adah manya, to wanne irin labari za ki rubuta?"

Kai tsaye ta ce "Akan rayuwata, wata'kila ba za a rasa matan da suke cikin rayuwar da na yi a baya ba!"

Ina fatan su ji labarina don su farka daga barcin makantar da suke, kafin su bude ido su gan su a *HALIN YAU* da nake fuskanta! Hawaye ya zubo mata ta sa gefen dan'kwalinta ta dauke a 'ko'karinta na kar Zainab ta gani.

Cikin sanyin murya da tausayawa Zainab ta ce,
"Amma kuma Sa'adah na dauka zuwa yanzu kin gane rayuwar nan bata da tabbas, bamu muke tsarawa kanmu rayuwa ba, da ace kowa shike sarrafa rayuwarsa da baku rabu da Uncle ba, da baki yi kukan rabuwar ba, Ni kaina ba irin kukan da ban taya ki ba, ba irin walankeluwar da ba mu yi ba a waccan lokacin, amma da yake a lokacin ubangiji bai nufa zamu samu cikar burinmu ba mun hakura kan dole. yanzu kuma Allah ya karkato da hankalinsa, maimakon ki yi wa Allah godiya, ki bishi sannu a hankali,har Allah ya taimake ki, ki koma dakinki, ki ri'ke 'danki, amma sai ki 'bullo da iya shege? Ni sai yanzu na gane ashe duk kuka da damuwar da kika yi ba har zuciya bane! Wallahi Sa'adah iskancinki ya fara damuna yanzu abin da kika mishi, da ya tsaya don ya taimake mu ya yi dai dai?"

Sai a lokacin ta bude baki ta ce "Idan dai taimakon daga gareshi ne ba na so, ya je ya rike dukkan taimakonsa, ke duk wani abu da ya shafe shi bana bu'kata. ya yi harkar shi na yi tawa, idan Allah ya so ma ba zan sake kuskuren bari mu hadu ba, ai wannan visiting 'din ma dole ne yasa na je, Inna bata nan, Anty Sumayya kuma tana da uzirin mijinta ba lafiya, dama su ne suke zuwa masa. Jawad ne yace, Malam ya ce masa baya gari ba zai sami zuwa masa ba, kin ji 'karfin zuwana." Ta ja majina ta ci gaba da cewa,

"Amma ban da haka ba zan je a ranar ba, balle mu hadu!
Zainab da ne na yi haukan banza na son na koma masa, amma a yanzu ko zan mutu ban yi aure ba, zan yi iyakar 'ko'kari na ga ko zaman mota bamu sake yi ba, balle zaman aure"

Muryarta ta karye alamun kukan da take ma'kalewa gaf yake da ya kubuce mata, ta ci gaba da cewa, "Ban taba dauka Mukhtar zai jefe ni, da abin da ya jefe ni da shi ba, in da tun farkon rabuwar mu na san kallon da yake mini ke nan da ko zan mutu ba zan bi shi ba, bare na ba shi ha'kuri, tunda na san shi ban huta ba.
Ban ga kuma da me na tsira a cikin zamana da shi ba, sai ko rabon Jawad da ya ratsa shi ma Ubangiji ne Ya 'kaddara ni ce uwarshi, amma a zuciyar MK, Farida yaso ta zamo uwarshi"

Sai lokacin Zainab ta katse ta da cewa, "Wallahi karya kike yi, ina ce ba dole aka mishi ya zabe ki a farko ya barta ba? kin dai san namiji ba a mishi dole, kuma ke da kanki kin tabbatar ke ce kike da alhakin mutuwar aurenki?"

"Tabbas ina da laifi amma ai shi ma ba za a rasa nashi ba, sannan kuma bi-ta-da-'kullin da ya bi ni da shi a idonshi da zuciyarsa ya sa na ji ko son shi ne ajalina sai dai na mutu da na koma masa, balle ma ba abin da hakuri ya bari"


"Ko za ki kwana kina rantsuwar ba kya son sa, ko ba kya son ki koma, ba yarda zan yi ba don kuwa 'karya ne tsagwaronta, don kuturun munafunci kun 'ki fa'dan mussababin rabuwar taku ai wannan ka'dai ya isa a san kuna son junanku tunda ba ku yarda aji sirrinku ba. Amma ban sani ba ko kin fa'da wa Halima tunda 'kanwar Inna ce ko kuma madadin Anty Sumayya"

'Kin tanka mata Sa'adah ta yi dan ta san magana ta fada mata a fakaice. Ganin haka yasa Zainab canja magana don tasan idan ta ci gaba da zungurarta yanzun nan Inna za ta shigo ta raba su don ba 'karamin aikin Sa'adah ba ne ta rufe ta da sababin da duk wanda ke gidan sai ya san an ta'ba ta.

Sai ta bige da lallashi, "Haba Maman Jawad na san ki da fa'da amma ba ki da ri'ko sam, na ro'keki kar fishi yasa ki yanke hukuncin da za ki yi kukan da ya zarce wanda kika yi a baya".

Ta nisa ta kalli Sa'adah, ta sake cewa "Idan ma wani Abu ya ce miki da ya miki ciwo wata'kila ya fada ne a lokacin da yake cikin fishi, ko kuma ya fada ne don ya 'kuntata miki, ki ji yadda shi ma yake ji. Amma shi ba abin a ranshi yanzu, tunda akan kunnenki Baba direba ya tabbatar da shi kanshi ya fahimci irin son da yake miki, ke ma kuma ya lura kina son shi, haba Sa'adah!"


Kukan da Sa'adah ke ma'kalewa ya kwace mata sosai, har Zainab ta ji to ko akwai wata magana data fada cikin kuskure wacce tasa ta kuka haka?

Amma da ta tuna Sa'adah sarkin kuka ce ko ba dalili, yasa ta samin nutsuwa.
 
Shiru ta yi, ba ta yi yunkurin hana ta kukan ba, ta san ko ba komai dai za ta sami salama a zuciyarta, sai da ta tabbatar ta yi ya ishe ta sannan ta ruko hannunta tana fadin ya isa haka, ki yi hakuri komai zai wuce ya zama tarihi, ki yi addu'ar zabin alheri, bawai zabin ranki ba."


Ta mike tana cewa, "Kin ji har ana kiran Maghrib bari na tafi sai na sake shigowa, ko kuma sai na gan ki."

Sa'adah ba ta ce mata uffan ba, ita ma Zainab din sanin halin 'kawarta tun fil'azal yasa ba ta damu ba. Ta juya ta fita, a tsakar gida ta tarar da Inna ta goya Khalifa ya nata barci,
"Ah goyo ki kayi haka Inna? Ai sai yasa miki ciwon baya."

Murmushi Inna ta yi tare da cewa, "Ku dai yaran yau da bakwa son goyo ne kuke kallon zai sa ciwon baya, alhalin shakuwa da tausayi ke 'karawa a tsakanin uwa da danta, amma ku boko da gayu ya hana ku goyo sai dai a hannu"

Dariya Zainab ta yi tana fadin
 "Inna Allah ina 'ko'kartawa."

"Allah Ya sa!" Inna ta fada tana kunto shi, yaro yasa kuka, wai shi an saukko da shi, ai ko Inna ta ce, "Juyo na sa miki shi a bayan." Cike da kunya da girmamawa tace, "To"

Ta sunkuya ta sa mata shi har zanin Inna ce ta daura mata, sannan ta bar ta ita kuma ta hau kiciniyar gyara goyon.

A gurguje suka yi sallama ta tafi ita kuma Inna ta yi bandaki da buta a hannunta.


Ta idar da sallar Maghrib tana zaune kan sallayar tana jan carbi, wayarta ta hau 'kuwwa, hannu tasa ta janyo ta ganin sunan Hajiyar Bichi, yasa gabanta ya fadi, duk da suna waya lokaci zuwa lokaci, amma ba tasan dalilin faduwar gaban da ta ji a yau ba. katsewa ta yi sai ta kira ta, Hajiya ta ambata sai kuma tace, "Assalamu alaikum!" Ciki-ciki Hajiyar ta amsa. Sai jikin Sa'adah ya yi sanyi ta ce, "Lafiya kuwa Hajiya?"

"Ba lafiya ba Sa'a, yanzu a ce za ki tafi wurin Jawad amma ki kasa fada mini? Na san kuma kinsan ubansa baya nan?"

"Hajiya ni ban sani ba".

"kin sani mana ai ba zuwa kike ranar da ake taron ba, amma wannan karon kin je saboda wanda kike gujewa haduwar ta ki da shi ba zai jeba,
sai kuma Allah ya yi nufin haduwar taku wanda shi kadai ya san manufar hakan.
Ban ga kuma laifinki don kin kame kanki ba. Laifinki daya da kika san dukkan ahalinki ba za su sami zuwa ba, sai ki fada mini mu tafi bibbiyu, wannan abu da kika mini sai nake ganin kamar ni ma fushin da kika dauka ya shafe ni ganewa ne ban yi ba sai yanzu."

Cikin son kare kai da kuma iyakacin gaskiyarta tace, "Wallahi ko ka'dan Hajiya ba haka ba ne, ba abin da za ki mini nan duniya na yi fishi da ke, har gobe ke uwa ce. Tunani na bai ba ni na yi hakan ba, na ma yi tunanin direba zai kai ku tare da Antinsa, amma ki yi ha'kuri Hajiya"

Take ko Hajiyar ta ce, "Na huce dama rashin fahimta ne, ki gaida Innar taki, kuma In sha Allah ina nan tafe cikin satin nan"

 "Allah ya kawo ki Hajiya!"

Ta ajiye wayar tana jin idan akwai asarar da ta yi cikin rabuwa da MK to kuwa rashin nagartatciyar suruka irin Hajiya na kan gaba, jin kanta ya mata nauyi ne yasa ta ci gaba da ambaton Allah.

   





    Alkalamin 
SURAYYA DAHIRU
    ✍🏼✍️
Post a Comment (0)