HALIN YAU 15 & 16


🌺 *HALIN YAU*! 🌺


*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•



    *SADAUKARWA GA*
   *SADIQ ABUBAKAR*



      *Fatan Alheri ga*
_DANDALIN MUM KHADY_.
                🤝🏽




                 15-16



Mamakin ta ne ya yi matu'kar kama shi wai yau shi ta kashe ma waya? Anya Sa'adah za ta canja hali kuwa?

Sake 'kiran ta ya yi a karo na biyu, amma ga mamakin sa har 'kiran ya katse ba ta 'daga ba.

Ya ri'ke wayar ya yi jim cikin sanyin jiki da tunani iri iri.
Ya san kirkinta ya fi sharrinta yawa, har yau kuma, shi dai a idanuwanshi bai ga wacce ta iya tsara kwalliya da gayu irin Sa'adah ba, ma'abociyar son 'kyale-'kyale ce, kusan wannan dabi'ar tata na son kayan 'kawa masu tsadar gaske ya taimaka wurin sake jefa aurensu cikin garari.

Lambar amininshi ya lalubo Dr. Mahmoud Karfi, ba ta dade tana dokawa ba, ya ji an 'dauka, tare da sallama, kai tsaye MK ya ce, "Kana Ina?" Daga can bangaren ya amsa da cewa, "Ina makaranta, lafiya?" 

"Lafiya Lau jira ni gani nan zuwa"

Ya katse wayar ya mi'ke ya shiga gida, ya dauki mukullin motarshi, tare da yi wa matarshi sallamar ya fita, ta bi shi da addu'ar dawowa lafiya.


"Kai tsaye sabuwar Jami'ar Bayaro ya nufa, bai bi takan ofishin saba, ya zarce ofis din Dr. Mahmoud Karfi.
Da sallama ya shiga shi ka'dai ya tarar yana dakon isowarsa, musabaha suka yi, Dr. Karfi ya dube shi, "Ka sa ni tunani iri iri fa"

Jim MK ya yi tare da cewa, "Wallahi ru'dani na shiga, ka san Hajiya ta matsa akan maganar na dawo da yarinyar nan, to dai yanzu na amsa mata akan na amince bayan na yi addua na kuma ji na aminta da lamarin. Wai yau na 'kira ta a waya da farko ce mini ta yi waye?"

Dariya ta so subuce wa Dr. 'Karfi, amma ya kirne, shi kuma ya zarce da cewa,
"Karshe kuma sai ta kashe mini waya"

    "Alhamdulillah!"

 'Karfi ya furta a fili tare da cewa "Ni na da'de ina ji a jikina idan dai ba mutuwa ce ta sure dayanku ba, to kuwa za ku sake ha'dewa. Shi yasa na kyale ka ka sami nutsuwa, ka san dai Sa'adah ta bi ka iyakar bi akan ka yafe mata, amma ba ka yi ba, ka zo ka yi aure dole ta gaji ta yi fishi, amma na san fishin ba mai yawa ba ne, tunda tana son ka."

A sanyaye ya ce, "Anya kuwa? ba ku san ta ba ne, a makarantar su Jawad fa baka ga iya shegen da ta mini a bainar nasi ba"

Dariyar da Dr. 'Karfi ya ke ri'kewa ta subuce, ya hau yi sosai, har ta sha'kar da MK, don haka sai ya mike ya ce, "Na gode"

Da sauri 'Karfi ya ruko shi ya na fadin, "Yi hakuri ka zauna ai ba mu gama ba"

Cikin fushi ya ce, "Ya zan zo maka da matsalar da ta dame ni, ka sani gaba kana mini dariya ka mayar da ni mahauka ci!"

"Wane ni Allah ya huci zuciyarka zauna mu gama"
 'Karfi ya fada bayan ya shanye dariyarshi. Komawa ya yi ya zauna amma fuskar nan a ha'de.
"Yanzu ka san me? Zan je na same ta mu yi magana, idan ya so sai mu koma tare, daga nan kuma shike nan sanda za ka je ma ba zan sani ba"

Cikin cin magani ya ce "Ni wallahi bazan ta zarya a wajenta ta na mini iya shege ba, yanzun ma Hajiya ce ta matsa amma banda haka ta je can ta 'karaci tsiyarta"

Mahmoud ya ce, "Yanzu ma damuwar da na gani a fuskarka, akan ta kashe maka waya, Hajiya ce ta matsa ka fada mini?"

Tsaki ya ja, ya san sha'kiyanci zai masa, tunda idan akwai wanda ya san yadda yake son Sa'adah to kuwa Mahmoud ne.

Sai kawai ya mi'ke ya fice yana fadin, "Sai ka yi kai ka'dai."

Shi kuwa ya ci gaba da dariyar shi a sake yadda yake so.

Ta idar da sallar Maghrib ke nan tana zaune tana tasbihi, zuciyarta cike da farin cikin fara gyaruwar al'amuranta, wayarta ta hau kuwwa, ganin sunan Baban dady yasa ta jin wani farin ciki ya 'kara kama ta, ba ta yi azarbabin 'dagawa ba har ta katse.

Kafin ta yi wani yun'kurin, ya sake 'kira, haka ta gama yau'kinta, ta dauka hadi da yin sallama,"Ranki ya dade ai na zaci ba za ki dauka ba ne"

'Yar dariya ta yi, "Akan me? Sallah na idar."

"Ya mutanen gidan to?" Ya tambaya, ta amsa mishi da, "Duka lafiya Lau"

"Ina son ganin ki wanne lokaci zan same ki?"

sanin mutuncinsa da karamcinsa ya sa ta fadin ko yaushe "Ina gida!"

"To ki saurare ni anjima kadan zan iso."

"Sai ka zo." Ta fada tana jin wani irin nisha'di na tsirga mata.

Wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin lallausan yadi ruwan hoda, mai shegen tsada ba shi da adon komai haka yake plane sai yauki yake da 'daukar ido. Doguwar riga ne aka 'kawata da shudin stones masu sheki matu'ka, don haka ta yane jikinta da matsakaicin mayafi blue,
 mai da roll on kawai ta shafa, kasancewar turarukanta sun kama kayanta sosai kuma ma'abociyar yin turaren kaya ne irin na barebari (garam). Duk da dare ne, sai da ta shafa powder ta kuma zagaye le'banta da jan baki ruwan hoda.

Yanayin jikinta irin tauraruwar wasan kwaikwayon nan ce Hafsat Barauniya, duk da Hafsar ta fi ta shekaru, ta kuma fita hasken fata, kasancewar Sa'adah mai duhu ce, ba kuma ta yarda ta shafa man da zai canja mata launin kalarta ba,
illa tana 'batar da kud'a'de masu yawa wurin siyan tsadadden man dake fitowa da ainihin kalarta, ta goge ta yi tas da ita, ta yadda ko mace sai kin yi sha'awar launinta shi yasa idan akwai tambayar da a rana ana mata ya kai sau biyar, ita ce wanne mai ki ke shafawa, wanne mai ki ke amfani da shi? wani lokacin ta fa'da, wani lokacin kuma ta yi murmushi wushiryarta ta sake 'kawata ta tace "Vaseline"

Tana tsaye jikin Shoe Rack (ma'adanar takalman)ta ta fito da wani Tom's blue, Innarta ta shigo ta kalle ta ta ce, "To 'dawisu sarkin ado a wannan daren kike wannan kwallliyar anya Iya baza ki rage wannan 'kyale-'kyalen ba? Shi yasa ai da yawa mazan suna son zuwa gunki amma gani suke kin fi 'karfin su"

"Inna tunda ba ni na fa'da ba ai shi kenan, idan mutum da gaske son nawa yake ya zo mana idan mun daidaita ai zan aure shi ne"

"Yanzun kuma mai za ki yi da takalmi, da na ga kina gogewa? Na san dabi'ar ki ce ca'ba kwalliya ba sai za ki fita ba, amma wannan takalmi ai na fita ne, kuma kin san ba inda za ki a wannan daren"

"Kai Inna don Allah!" Ta fa'da cike da shagwaba, "Ni fa ba fita zan yi ba, ba'ko zan yi"

"Kin fa'da wa Baffanku za ki yi Ba'ko?"

Kai tsaye ta ce, "Na fada masa kafin ya tafi sallar Isha"

"Shi kenan amma don Allah Iya ki daina bata wa mutum lokaci kina kuma karbe mishi abin hannunsa alhalin kin san ba auren sa za ki yi ba,
yaudara ba kyau. Alhaji Mamman din nan ni ban ga laifinsa ba, mutum mai mutunci mai nagarta ga shi babba ne ya mallaki hankalinsa amma kina tasa 'kafa kina shure shi, kuma kina kar'be mai dukiya"

 "In sha Allah, Inna ko mai ya kusa zuwa 'karshe, ki 'kara 'kaimi wurin yi mini addua"

Dadi ya kama uwar tata kusan yau ne Sa'adah ta bude baki ta yi magana mai kyau akan aure.

Nan da nan ta hau fa'din, 
"Addu'a kam ai kullum yin ta nake, mantawa na ke da ko mai sai ke idan ina addu'a, Allah ya miki zabin alheri"

Ta fita tana sake cewa, "Ba abin da ke raina irin in gan ki a 'dakinki kin nutsu wuri daya"

Har sai da ta yi sallar Isha sannan ya mata waya ya iso. Fararen kujerun da ta tanada saboda zuwan wanda tabawa izini, ta 'diba ta fita dasu zauren gidan nasu da ke da yalwar fili, tana zuwa shi ma yana 'karasa shigowa, da sauri ya karbe kujerun yana cewa "Ai da kin sani kin jira na zo na 'debo, wannan ba aikin uwargidanmu ba ne"

Dariya ta yi, "Za ka fara ko?"
Shi ma dariyar ya yi, "Zan fara fa'din gaskiya ba"

komawa ta yi ta ha'do mishi ruwa (pure water) da kuma kunun ayan da Inna ke yi akan faranti tare da Tumbler, ta ajiye mishi tare da cewa "Ga ruwa"

Ya yi godiya ita kuma ta hau gaishe shi tare da tambayar iyalinshi, ya ba ta amsa da cewa, "Ai ta yi fishi da ke tace rabon da ki taka mata tun barkan haihuwar Kausar,
ga Kausar tana gudu ko Ina."

Ta ce, "Hidimar makaranta ce ta 'boye ni amma yanzu kam na gama za ta gan ni, a ba ta ha'kuri"

Sai da ya bude ruwa ya sha sannan ya yi gyaran murya ya ce, "Zuwan fa na mussaman ne, tare da albishir din abin da muka dade muna nema ya samu, takanas MK ya same ni ya ce mini ya kira ki, amma kin kashe mishi waya haka ne?"

Kai tsaye ta ce "E ai ban san shi ba ne"

"Ban gane ba ki san shi ba ne"?

 "To bai gabatar da kansa ba,
ya fara maganganun da ban fahimce su ba".

Shiru ya yi tare da cewa
"Amma ba ki da lambarsa ne?"

"Ban da ita" 

"Ba ki da ita?" Ya tambaye ta cike da mamaki. 

"E!" Kawai tace ta ja bakinta ta tsuke.

Kamar zai bar maganar sai kuma ya ce, "Amma aikin haddace a kanki"

Nan ma ta ce, "Na manta" 

Ya yi dariya, "Sa'adah wai yaushe kika cire mu a ranki har haka ne?" 

Murmushi ta yi ta ce, "A lokacin da na fahimci ba komai ne idan ka rasa yake dawo maka ba, ba kuma komai ne kake so yake zama alheri ba"

Da sauri Dr. 'Karfi ya ce, "To mu dai alheri ne kuma mun dawo mu sake daukar ki a karo na biyu."

"Amma bai kama ta, ya manta cewar aure ya 'kare a tsakanin mu ba?"

Ta fa'da cikin 'daure fuska.






     Alkalamin 
SURAYYA DAHIRU
       ✍🏼✍🏼
Post a Comment (0)