HALIN YAU 17 & 18

🌺 *HALIN YAU*! 🌺



    •·•·•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•


           17-18.




" A a ban sani ba bai kuma fa'da mini ba."

'Karfi ya fa'da cikin yanayi na rashin gamsuwa, tare da zuba mata ido yana ta a uziya saboda yadda shaidan ke 'kawata mishi ita, ya riga ya binne wannan abin a ransa har abada ba zai yi tarayya da MK akan mace ba, macen da ya tabbatar amininshi yana mata son da bai yi wa kansa ba.

Ya numfasa ya 'kira sunanta,
"Sa'adah karki wahalar da ku, da ke da Mukhtar kuna son junanku, nan duniya ba abin da zai kankare wannan son, dole za a sami matsala a cikin zamantakewar aure, muhimmi shine ayi afuwa, a yafe, a kuma manta, amma ba za a iya kaucewa matsalar ba. ko wani sabon auren kipka yi komai jin da'din da za ki riska sai kin tarar da matsala"

Ya nisa sannan ya sake fa'din,
"Ina tabbatar miki kuma a yanzu ne ya fi dacewa ki koma dakinki, ba a wancan lokacin da ke kadai kike son komawar ba, yanzu da shi ya bukaci hakan da kansa za ki fi 'kima, ki fi daraja"

Sunkuyar da kai 'kasa ta yi hawaye na cika idonta, amma ba ta ce komai ba, ganin yadda jikinta ya yi sanyi, hakan ya 'kwarara guiwar 'Karfi.

Ya sake kur'bar ruwa ya ce, "Kar ki bari wannan damar ta kubuce miki, ina tabbatar miki, MK bai so wata mace kamar ki ba, kar ki bari rudin 'kawaye da zuciya su sake rudar ki a karo na biyu, wai ya yi aure, ko kaza da kaza, da duk abin da zai sake dagula miki lissafi.
Ki sa a ranki cewar ko kuna tare zai auri Farida! tunda an rubuta a cikin littafin 'kaddararshi cewar matarshi ce, mu gode Allah da ya kasance rabuwa ku ka yi, ba mutuwa kika yi ba, kin san akwai rabon da ke kashe mutum".

Hawayen da ta ke tattalawa ya zubo akan lallausar fuskarta, ta ce, "Ai ni sai daga baya na gano dama auren ya 'kallafa rai zai yi shi yasa ya yi ta zungurata, komai 'kankantar laifi sai ya juya shi ya zama garma, ashe dama akwai abin da ya 'kudure, to ya aureta hankalinshi ya kwanta, ni ma kuma ai bai jini a gadon asibitin mahaukata ba, bai kuma ji labarin auren nashi ya zama ajalina ba"

Kuka ya so kubuce mata saboda haka ta yi shiru sai rishin kukan kawai. Sai da ta nisa sannan ta sake dorawa da cewa, "Ni kuma nan duniya ban ga mai zai mini na ga farin shi ba"

Ta fada cikin dakewa da shanye kukan dake son kunyata ta. Jikin Mahmoud ya sake yin sanyi, ya yi shiru cikin rashin abin cewa.

Tsawon mintuna biyar kowa ya yi shiru a tsakaninsu sai fama suke da tunanin zuci.

Shudewar yan mintuna kafin ya ce, "Ni fa ba tone-tone za mu yi da ke ba, dukkanku, kowa da irin nashi laifin amma kin sani, laifin ki ya fi yawa" 

Cikin takaici ta ce, "Baban Dadi tunda laifina yafi yawa, ai ya sake ni ya auro wacce ba za ta yi kuskure ba, wacce son da ake mata zai sa ayi ta mata uzirin ri'ke igiyar aurenta da kyau, sai dai a nuna mata kurenta cikin ladaftarwar da shari'a ta tanadar, shi yasa ni ma da na gane ba son nawa ake ba, kuma duk ni ce mai laifin sai na dau hukuncin da macen da ta san ciwon kanta za ta dauka don ta tsira daga ba'kin cikin namiji".

Shiru Mahmoud ya yi mata ya lura kishin Farida ne ya ke cinta shi yasa take ta furzar da magana, don haka ya 'kyale ta, at least dai za ta sami sau'kin ciwon dake addabar zuciyarta.

Sai da ta yi shiru don kanta, sannan yace"Ki yi ha'kuri, ki bi komai a sannu, ban hana ki nuna bacin ranki ba, amma kar ki wuce gona da iri, saboda kin san kema kin mishi laifin da sai da ya yi jinya bayan rabuwarku, tunda har ya sau'ko, to fa kar ki wuce makadi, ina fada miki wannan maganar ne a matsayin yayanki"

Ya dan numfasa, kana ya zarce da fadin, "Lamarin aure yanzu sai ha'kuri ba Perfect Marriage, kowanne aure da irin nashi 'kalubalen, duk abin da aka ce ibada ne, to fa sai an yi hakuri".

Ya mi'ke yana cewa, "Zan wuce, ki saurari zuwanmu!"

Hannu yasa a aljihunsa ya fito da yan dari biyar guda ashirin ya zuba kan kujerar daya tashi, da sauri ta ce, "Don Allah ka bar su, kullum a cikin hidima kake "

Murmushi ya yi yana cewa,
"Wannan kudin zance ne, ina fatan dai za a karbe mu da dukkannin raunin mu, kasancewar mu Malaman makaranta masu sadaukarwa, ba ma su satar kudin jama'a ba"

Ta san sarai inda maganar shi ta dosa, da Alhaji Mamman ya ke, tunda ya sha ganin ta da shi, wanda 'karara yake taya amininsa kishi.

 Dariya ta yi tana kuma godiya amma ta ci alwashin bashi ya ci, dole sai an baje maganar nan ai ya san tun farko ta zabe su tabar Alhaji Mamman din da dukkan abin da yake da shi.

Tun a mota yake 'kiran lambar MK amma bai dauka ba, har ya gaji ya mayar da wayarshi caji a jikin motar. Mintuna kusan ashirin har ya shiga layin gidansa yaji 'karan wayar shi, ganin sunan MK yasa shi dauka da sauri, tare da cewa, "Wai ina ka shiga ne?"

Daga can ya amsa mishi da cewa, "Wallahi ina tare da Farida ne ba zan so ka yi mini maganar Sa'adah a gabanta ba"

Shiru Dr Mahmoud ya yi yana jin shi kam bai san wani namiji da ke gudun 'bata wa matarshi da gangan irin MK ba, ya tuna lokaci da dama da yake zaunar dashi yana caccakar shi akan tsoron Sa'adah ya ke yi, ashe ba tsoro ba ne tunda ga Farida ma hakan ya ke mata.

Mutum ne mai martaba abin da yake so, ko wadda yake son sa, ya sake tuna ko a abotarsu, MK ke ha'kuri da shi, shi ke masa hidima ba tare da tunanin ai yasan yawan albashinsu 'daya ba, samun irin Mukhtar Kabir Bichi zai yi wuya a wannan lokacin.

Amma duk da hakan sai da ya tsokane shi da cewa, "Dadi na da kai mijin ta ce ne kai, ni ban san me ya sa kake jin tsoron mata ba, ai na 'dauka Sa'adah ce kawai dodon taka, ashe wa lnnan alankosar ma murza ka take yi".

Shi ma cikin 'kosawa da shakiyancin da ba ya gajiya da mishi ya ce, "Kai ai ba za ka gane karatun ba ne ni kadai na san mai suke jiyar da ni, ka ga kuwa ai dole na yi tattalin farincikinsu, kar ni ma a hana ni nawa farin cikin"

Dariya sosai 'Karfi yake yi yana cewa, "Ashe haka karatun yake ganewa ne ban yi ba? amma da dukkan alamu karatun naka na daban ne"

"Idan kagama iya shegen naka, ina sauraranka don waje na fito, idan kuma ba ka gama ba, to zan koma, ma hadu gobe"

'Karfi ya gintse dariyarsa hadi da cewa, "Kai MK wallahi da alama 'yar darun taka, ta shiryawa daru kala-kala, amma dai na san kishi ke 'dawainiya da ita, ka san tunda ka yi auren nan bata bude baki ta ce 'kala ba, yana ta cin ranta, na ga soyayyarka mai yawa a idanuwanta duk da bakinta na 'kirarin rashin son"

Shiru MK ya yi har Mahmoud ya yi tsammanin ko wayar ce ta katse. Amma da ya ce,
"Kana ji na kuwa?"

 MK ya amsa da cewa
"Ina jin ka. Mamakin ta ne ya ke ta kama ni".

"Ai ba mamaki a lamarin mace." A cewar 'Karfi.

"Ka shirya gobe muje mu same ta, kada Hajiya ta tambaya ta ji ba ka fara kafa tubalin kome ba ta yi fishi" 
Ya 'karasa maganar cikin zolaya.

"Hmmm!" Kawai MK ya yi tare da cewa "Na gode sosai sai mun hadu gobe idan Allah yaso"

                         *

Sa'adah tana shiga a dakin mahaifiyarta ta ci burki, "Inna na dawo" 

"Zo ki zauna magana zamu yi"

Ba ta musa ba ta shiga ta zauna daf da ita,"Waye ya zo?"

"Ba wani daban ba ne Baban Dadi ne"

Tabe baki ta yi tare da cewa "Waye hakan, kar ki ce mini Mahmoud abokin Muutar?
Cikin shagwaba ta rungumo uwar tata ta ce "Shi fa mene ne Inna?" 

Ture ta ta yi tana cewa
"Ashe baki daina bibiyar yaron nan ba ko? 'dazu amsar da ki ka bani na komai ya kusan 'karewa akan maganar aure, ashe kina nan kina zawarcin Muutar ne? Wannan shi ne al'kawarin da ki ka mini?
Tunda kin zabi son ranki sama da nawa to ki je ki ta yi,
amma ki sani ba da yawuna ba, ba kuma da son raina ba, sai don kin fi 'karfina, don kin san zaki samu goyon bayan mahaifin ki ne"

 Ta nisa sannan ta ci gaba da cewa, "Tunda na ga kina ta hanzarin shiryawa tare da 'doki na tabbatar ba kowa kike wa wannan rawan jikin ba sai shi"

"Inna ba fa yadda kike zaton lamarin ba ne wallahi ban karya al'kawarinmu ba, amma don Allah ki yi hakuri ki gafarce ni ba na son kina damun kan ki akan wannan maganar"

"Ai dole na damu tunda na gane ke da Baffanku, ba ku da burin da ya wuce ki koma gidan Muutar, ni kadai na san ba'kin ciki da wahalar da na sha kafin na samo ki a dalilinsa. kuma yanzu da komai ya wuce sai ya lallabo ya sake dama miki lissafi, saboda ya mai da ke marar zuciya, wacce ba ta san ciwon kanta ba"

Cike da tausasa murya Sa'adah ta ce, "In sha Allah Inna ba zan sake shiga halin da kike jin tsoro ba, ni ma nasan abin da kike guje mini, tuni na cire shi a raina."

"To idan dai haka ne ki ba wa Alh Mamman ko yaron nan Anwar dama wani cikinsu ya fito, ki yi aurenki idan ba haka ba, hankalina ba zai kwanta ba." 
Ta fada tana goge hawaye da hannun zaninta.

Jikin Sa'adah ya yi sanyi ashe dai da gaske Inna take akan ba za ta koma wa Malam ba? Ashe haka ta zafafa lamarin?

Wannan wacce irin ba'kar 'kaddara ce ke bibiyar ta ne? Bayan doguwar wahalar da ta sha akan komawarta 'dakinta, sai da abu ya zo a lokacin da ba ta yi tsammanin zuwansa ba, kuma mahaifiyarta ta yi bara'a da lamarin, hankalinta idan ya kai dubu to ya tashi.


*_Wai mene ne ke faruwa a tsakanin ma'auran biyu? Mene ne ainihin labarinsu? Mene ne ya raba su duk da matsananciyar soyayyar da ke tsakaninsu? Mu je ga mafari don jin wacce irin waina suka toya?_*





     Al'kalamin
 SURAYYA DAHIRU
         ✍🏼✍🏼

Post a Comment (0)