HALIN YAU 19 & 20


🌺 *HALIN YAU*! 🌺



•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


         *SADAUKARWA GA*
          *SADIK ABUBAKAR*.



             19-20.




              *MAFARI*



Malam Basiru Ado Gogel, haifaffen garin Gogel ne, wani gari a 'karamar hukumar Warawa. Karatun Allo ne ya kawo shi cikin garin Kano, ya sa himma har Allah ya taimake shi, ya haddace al'kur'ani, sannu a hankali kuma ya fara sana'ar tura kura a kasuwar Singa

Da damina zai tafi gida yayi aikin gona gadan-gadan kasancewar al'ummar garin Gogel manoma ne, duk da ya ta so ba uba, domin ya na da 'karancin shekaru mahaifinsa ya rasu, dan haka ya yi birgimar ta shi fa'din rayuwa a tsakanin mahaifiyarshi da 'yan uwan mahaifinsa.

Da haka ya hada jarin sa ya bude 'yar tireda a cikin unguwar da ya ke hayar 'daki, a unguwa uku, a shekarar kuma aka masa aure da Salamatu 'diyar 'kanin mahaifiyarsa wadda asalin mahaifiyar ta shi 'Yar asalin gamawa ce ta jahar Bauchin Yakubu, aure da rabon haihuwar sa ne ya kawo ta Gogel, kenan Salamatu ma, da ga Gamawa aka ba shi ita.

Ya taho da ita cikin kano, suna zaune lafiya, cikin rufin asiri.

 Yarinyar su ta farko da suka haifa bayan shekaru uku da aure, sunan ta Sumayya, ba sunan kowa taci ba, illa sunan Nana Sumayya, macen farko da ta yi shahada a musulunci. tare da fatan yarinyar ta sami albarkacin mai sunan.

Haka sukaci gaba da rayuwar su cikin rufin asirin Allah, dukkansu sun da ce da juna, masu ha'kuri ne, masu kuma wadatar zuci ne.

Sai da Sumayya ta yi shekaru takwas sannan aka haifi Sa'adah wadda sunan mahaifiyarsa ta ci (Sa'adatu). Daga shi har Innar su Salamatu su ke kiran ta Iyah, kamar yadda ake kiran mai sunan nata. A shekarar kuma mahaifiyarshi ta rasu, shi yasa ya tattara ko mai da ya ke dashi a Gogel ya siyar illah gona 'daya da ya bari, wadda zai dinga noma wa, sai kuma 'dakin mahaifiyarsa da yake cikin gidansu ya rufe shi saboda idan ya je Yana da gurin zama. ya zo kano ya si yi madaidai cin gida anan cikin unguwar gidan akan titine a kuma babban layin na Unguwa Uku.

Haka rayuwar su ta ci gaba da tafiya cikin ha'kuri da godiyar Allah, har Sumayya ta kammala 'Karamar sakandire manema suka mata ca kasancewar ta doguwar mace fara sol irin fulanin Gamawa.
Idris shi yafi kwanciya a ran Malam Basiru dan haka ya ce ya bashi, ba kuma ya bu'katar komai a gunsa sai sadaki da musulunci ya wajabta, komai zai ma ta idan ta je gidan shi sai ya yi. 
Wannan karamcin da iyayen Idris suka ga ni ya faranta ransu ba ka'dan ba, suka girmama lamarin Sumayya da iyayen ta, kullum cikin jan kunnen shi su ke, akan ya ri'keta cikin aminci.

Haka aka yi auranta ba wani hidima, ya 'dauke ta zuwa ogshobo ta jihar osun inda yake aiki da babban bankin Nigeria (CBN) reshen jahar osun.

Dan haka Sa'adatu ita kadai ta taso a gidansu domin kuwa, ba ta wuce shekaru takwas ba, aka aurar da yayarta kasancewar mahaifinsu bai wani damu da karatun boko ba, muhimmi dai a gunshi a haddace alkur'ani.

Tun kuma akanta basu sake samun haihuwa ba, shi yasa sha'kuwa mai yawa ce tsakanin ta da iyayenta biyu har tana rasa gane waye yafi sonta a cikin su.

Yau da gobe aka ce ba ta bar komai ba, Iyah ta kammala 'karamar sakandire, amma ganin yadda ta k'wallafa rai a boko da kuma yadda ba ta sauraren ko wanne saurayi yasa Malam Basiru barin ta ta tafi babbar sakandire, kamar wasa aka zabe su, su biyar a makarantar su, ta GGC U/Uku, su rubuta jarrabawar shiga sakandire ta gwamnatin tarayya ta Kano (FGC KANO). jarrabawar na fitowa kuwa sunanta ya fito cikin mutum uku da suka yi nasara, ita kanta ta yi mamaki tunda duk ragowan da suka fa'di sun fita 'ko'kari.

Ganin ku'di tsululu da za'a kashe a hidimar makarantar Malam Basiru ya tabbatar ba makarantar dan talaka ba ne, da bashi da ko mai da kowa sai Allah, shiyasa ya zaunar da ita yace, "Iyah kin san ni ba mai kudi ba ne, bani da halin sa ki a wannan makarantar, ki ci gaba da wadda ki ke yi, kin san dai, ko yanzu idan kin samu mijin da na yarda da nagartar shi auren ki zan yi.

Shuru tayi amma a ranta tana jin ba 'karamin abin kunya ba ne ace ta sami damar shiga babbar makaranta irin wannan, amma ace ba ta tafi ba, ba ta san ma da wanne ida za ta kalli 'yan ajin na su ba, mussaman Zainab Salisu Ma'aji da su ke kusan unguwa 'daya, kuma ita ma taci makarantar tana da tabbacin za'a kai ta tunda ta na da yayye ma'aikata.

Kasancewar ta mai tsananin tsabta da gayu sai ake mata kallon tamkar ta fito ne a gidan wadata, ita kuma ganin haka yasa ta yin alfahari mussaman da ba ta da makusa a halittar ta.

'Karfe takwas na dare ta dauki wayar innarta, ta shige 'dakin da ya ke mallakin ta ne, Yar uwarta Sumayya da a yanzu suke zaune a Jos babban birnin jahar Plateau da yaran su biyu Abba da Khalifa, ta shiga yi wa flashing, cikin 'kan'kanin lokaci ta biyo baya, tana 'daga kiran, ta sa mata kukan da ta kasa yi a gaban mahaifan nasu, jin kukanta ya matu'kar tada hankalin Sumayya, ta shiga tambayar ta menene, me ya same ki? jin yadda Sumayya ta 'daga murya a gigice ya janyo hankalin mijinta wadda ya ke kur'bar shayin da ta hada masa, cikin kukan ta fa'da mata yadda ta ci makaranta irin FGC KANO, amma kuma Baffan su ya ce ba shi da kudin sa ta a wannan makaran ta.

Jim sumayya ta yi kafin ta ce "To ban da abin ki Iyah! Ba sai ki yi ha'kuri ba, kinsan dai nan duniya idan Baffa bai mi ki abu ba, bashi da hali ne, da girman ki da komai ki zauna ki na kuka, akan abin da ki ka san ba da gan gan aka 'ki miki ba?"

Shesshkar kukan ta cigaba da yi, Sumayya ta sake cewa "kukan shagwaba ki ke yi Iyah! ni da ba a barni na gama ba fa?

Turo baki ta yi kamar ta na ganin ta, tace "To ai ke yanzu maganar ki ta wuce, kuma gaskiya Aunty, ki dena cemin Iyah". da sauri Sumayya ta furta "Yi hakuri Anty Sa'adatu"

'Dan murmushi ta yi hade da jan majina, sannan ta ce"Ina su Abba? Sumayya ta ce "gasu can sun yi barci sun gaji"

A haka Sumayya ta lalla'ba 'kanwar ta har sai da ta yi dariya sannan su ka yi sallama, amma Sumayya ta dinga jin jina halin kanwarta na yadda ta ke kai kanta inda Allah bai kai ta ba.

 Mijin Sumayya da ya fahimci maganar su, sai ya 'kudure abu a ranshi amma bai mata maganar ba, kamar yadda bata sa shi cikin maganar su ba, idan akwai abin da ya ke 'kara mata 'kima to rashin hayaniyar ta da 'karancin buri ne, da wahalar gaske ta bude baki ta ro'ke shi wani abu kai shi zai iya cewa bata ta'ba ba.

Abin da ya mata shike nan, sai shi ne da ya fahimci halin ta, sai yake yawan kyautata wa iyayenta, mussaman da ya fahimci suna bu'katar taimakon amma halin su, na wadatar zuci da rik'e girma, basu ta'ba nunawa ba, bare a gane.

Kwanaki uku a 'tsakani ya tura ku'di masu yawa ta hannun amintaccen amininshi akan ya je ya kai wa surakin nasa, ayi wa Sa'adatu hidimar makaranta, wadda da 'kyar Malam Basiru ya karba.

Ya 'kira Sumayya ya ma ta fa'da akan mai za ta 'dorawa mijin ta nauyin da ba nashi ba?

Rantsuwa ta dinga yi akan ita bata fa'da masa ba, sai dai idan ya ji sadda suka yi waya da Iyah ne, sannan kuma bai fa'da mata, zai yi wani abin ba.

Yace to " Ki masa godiya kudi masu yawa ya aiko, ki kuma 'kara masa biyayya, ki 'kara ha'kuri dashi"

Shikenan sai aka fara shirye shiryen shigar ta makarantar har komai ya kammala.

Ana cikin Shirye shiryen sai ga Baffa yazo da dimemiyar katifar yan makaranta har da filo dukkan su(Vitafoam)ne,da kuma bargo duniyar kule amma 'karamin size, sabo dal a cikin jakar shi.

Da mamaki Inna ta hau duba katifar ta na fadin "wannan katifar ai ta yan makaranta ce".

Sai da ya zauna akan tabarmar da aka shimfida domin shi sannan yace "Wallahi Salamatu wani yaro ne muke gaisawa da shi,tun ba yanzu ba, 'dan gaban tireda ta yake da shago, kullum yazo sai ya gaishe ni, a haka muka yi sabo na gaske. Yau kwanaki uku na fada mishi yarinyar waje na ta ci babbar makarantar gwamnatin tarayya. Bawan Allah sai ya zaci ta kwana ce, ashe wai akwai bangaren ta kwana (boarding), akwai ta je ka ka dawo(day)".

Ya numfasa ya dauki kofin ruwan da aka ajiye mishi ya sha, sannan ya 'dora da cewa 
"Sai ganinsa na yi 'dazu da katifar nan, wai ya kawowa 'yar makaranta, nace kai ma ka na fama da kan ka, ya za ka takura kanka"? 
Tunda dalibi ne a jami'ar Bayaro, yace min yana shekarar 'karshe, na'ki karba tare da nuna masa ita ba ta kwana ta ci ba, dan haka ya mayar ya amshi kudinsa, nan ya rantse ba zai koma da ita ba, tunda ya riga ya siya, ya kuma yi niyya, abata ta dinga kwana a kai.

Kuma abin mamaki har da ku'di wai a siyi littafai"
 Sai lokacin Inna tace "oh mukam mun gode Allah, Allah ya saka masa da alheri, Allah ya sanya alheri da farin ciki a rayuwarsa".  
Take kuma ya ce "Iya zo ki dauki katifar nan da bargon nan naki ne, wani yaron arzi'ki ne ya baki, sai ki sa shi cikin adu'oi'n ki".
 Da murna ta ja katifar tana fadin Nagode Allah ya saka da alheri.

"Ya sunansa Baffah?"
"Sunansa Muuktar amma ni Mutari na ke ce mishi ya kuma amsa ci ke da girmamawa".

Inna ma ta bi sahun Iyah a wurin murna tana sake dauko sabbin addu'a, "Madallah da wannan yaro, Allah ya bashi ilimi mai amfani,ya bashi mace ta gari".

Da ga Iyah har Baffan suka hau rige rigen amsawa da Amin.

Inna ta sake cewa "sunan shi mai da'di amma ka ke ce masa Mutari? Ni kam Muutar zance" Suka sa mata dariya, Sa'adah na cewa ai ko dai Inna gara ma ki ce Mutarin.

A daren ranar ta fito da yar tsohuwar katifar ta, da ta zama tamkar tsumma, ta shimfi'da sabuwa cike da zumudi, a ranta tana ta kwararawa wadda ya siyi katifar fatan alheri.

Shigar ta makarantar sai ya 'kara mata girman buri, saboda yadda ta hadu da 'kawaye fe'kak'ku wadda suka fita rawar kai da waye wa.

Kusan dukkan daliban makarantar ya'yan masu dashi ne, ko kuma na ma'aikatan gwamnatin da suke daraja ilimi.

Arts Class ta zaba a burinta na son zama Barista, ba'a kammala farkon zangon karatu ba (first term) sai da sabo da sha'kuwa ta shiga tsakanin ta da Halima mu'az Matazu, Safina Usman Bunkure, da Humaira Suraj wadda dukkan su iyayen su masu 'kumbar susa ne, itace kadai yar talaka, ko Halima da ba wani kudi ke gare suba, sun wuce matsayin su Sa'adatu, tunda Baban ta ma, aikaci ne a ma'aikatar Revenue yayin da mahaifiyar ta take principal a wata makarantar 'yan mata ta gwamnatin jaha(GGC).

Ita Sa'adatu kawai kwalliya da gayu ne ya janyo mata 'kawaye tunda tana samun abubuwa masu tsada daga yar uwar ta Sumayya.

Tunda suka hada group basu cika mai da hankali kan karatun su ba, illa kwalliya da kuma soyayya tunda kowa ya san FGC KANO co-education ake yi, ma'ana makarantar maza da mata ne a ha'de.

Dukkan su suna da samari a ajin, inka dauke Halima da ta ce ta fi 'karfin soyayya da yara 'kananu, kasancewar tana da saurayi na gaske a gida, wadda ya kasance 'Dan 'kawar maman ta ne.

Khalil Ibrahim na cikin wadda su ke son Sa'adatu Bashir, mahaifinsa ne kwamishinan ilimi na Kano a wanccan lokacin, ita ma kuma ya fi kwanta ma ta a rai, dan haka tana kula shi, dukkan kudaden shi na kashewa a makaranta a kanta ya ke 'karewa.

Wani lokacin ma har fakar idon mahaifiyar shi ya ke ya debo mata kudi kasancewar ta shahararriyar yar kasuwa domin Dubai take fita ta shigo da kayayyakin mata na alfarma, wani lokacin har da Abaya da lace yake daukowa dan ya bawa Sa'a🤔

Suna da 'kokari amma da yake basu mai da hankali kan karatun ba sai suka sha mugun kaye.

Halima da ta kasance ogar su saboda duk tafi su 'kokari ta kuma fi su izza da buri, ita ce kawai ta yi ta shida, amma kowacce a cikinsu ta wuce ta ashirin.

Sa'adatu ita ce kashin baya ta kai ta talatin tunda duk sun fita background din makaranta mai kyau.

Dukkan su jikin su yayi sanyi da ganin sakamakon su, amma Sa'adatu ba ta wani damu ba, tunda dai ta san daga Inna har Baffa sun san tana da 'ko'kari a makarantar da ta baro. zai yi wahalar gaske ma a wani tuhume ta in dai ba Sumayya ce ta zo garin ba.

A cikin wannan yanayin suka kammala SS1, suka shiga aji biyar, budurci sosai, ya bayyana a jikinsu, duk wadda ke FGC KANO ya san da zaman 4stars.

Barin Sa'adatu Gogel, ba wai kyau ta fi su ba, a a kawai ita ma'abociyar kwalliya ce kusan kowanne term sai tasan yadda ta yi, tsakanin 'karya da gaskiya an sabun ta mata uniform, sannan ko mai na ta mai tsada ne tunda ga kan sandal, da school bag, Sumayya ta tsaya ma ta a wannan bangaren, duk kuwa da tana mamakin yadda kowanne hutu sai ta canja komai. Hakan yasa ta saje cikin Ya'yan ma su wadata har ma ta fi su daukar ido, mussaman saboda 'kirar jikin ta.


Zangon karatu na biyu, a aji biyar din su, a ka turo sabbin 'yan hidimar 'kasa (COPPERS)
Cikin su har da Mukhtar Kabir Bichi (MK Bichi).





   `Alkalamin
  SURAYYA DAHIRU
          ✍🏼✍🏼
Post a Comment (0)