HALIN YAU 29

🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


    *Dan Allah masu son Halin Yau! Daga farko, ku dinga tambaya a group, a kullum nakan turawa mutane daban daban sama da sau goma, nasan soyayyar labarin ne ta kawo hakan, amma abin yana mini yawa mussaman da kullum'kara yin nisa muke yi! Idan anturo ku dinga tarawa, idan antambaya ku yi sharing, yanzu aka fara, labari na gaba, JAZAKUMULLAHI KHAIR.*



  *Comments din ku na sani nisha'di na gode sosai fans Allah ya fini yabawa*




    *SADAUKARWA GA*
     *SADIK ABUBAKAR*.





                   29.





Ta jima zaune a gun, tana jin wani irin nisha'di tare da shauki yana ratsa zuciyarta da gangar jikinta gaba'daya, tana tuno yadda ya lankwashe murya yana fadin,

 "Ke ce Bebina ba Farida ba"

Cike da farin-ciki ta na'de tabarma ta shiga gida, dakin Inna ta fara shiga ta shaida mata ta dawo sannan ta jigine mata tabarma inda ta dauka.

'Dakinta ta shiga, ta fara tattara uniform din da ba ta wanke su ba, ta fita tsakar gida ta hau wanki, hatta sandal sai da ta wanke ta shanya, tana gamawa ana kiran Maghrib. Koda Inna ta fito ta ga shanyar uniform uffan ba ta ce mata ba.

Sai da Baffa ya shigo bayan sallar Isha ta je ta durkusa gabansu, ta shaida musu gobe za ta je makaranta, Inna dai ba ta tanka ba, Baffa ne ya ce,

"Allah ya kai mu" 

Ta dade a tsugunne tana jinta wani iri, ta san fushi suke da ita dukkansu musamman Inna. don haka sai ta sanyaya murya ta ce,

"Don Allah ku yi ha'kuri na san ban kyautata muku ba, na yi musu da ku, ku yi mini afuwa"

Ta fada cikin muryar kuka, kasancewar Baffa ya fi mata sassauci, shi ne ya fara tankawa da cewa,

"Ni ban san inda kika samo dabi'ar yin musu da iyaye ba Iyah? Ni da kaina na rarrashe ki akan wannan maganar kika kafe, kika nuna mini ni ne zan bi ki ba ke za ki bi ni ba".

Jikinta ya yi mugun sanyi ta shiga kuka na sosai tana jin kunyar maganganunsa na matu'kar ratsata, musamman yadda komai take so yana kokarin yi mata duk kuwa da wani abin don ya faranta mata yake yi, ba don yana so ko yana da karfin yi ba. Cikin kuka sosai ta ce, "Don Allah ka yi ha'kuri Baffa In Sha Allah ba zan sake ba."

Ya nisa ya ce, "Shike nan na yafe miki, amma ki kiyaye, wannan ba dabi'ar kwarai bace, musamman kasancewar ki mace, ko wani daban wanda kika san ya girme miki ya ce miki kar ki yi kaza, ai kin mutunta shi ki bar abin kasancewar ya fi ki hangen nesa, bare kuma ni mahaifinki da ba zan cutar da ke ba ta kowacce fuska".

A hankali ta ce, "In Sha Allah zan kiyaye, na gode Allah ya kara lafiya da nisan kwana Baffa".

Cike da tarin soyayya mai yawa ya amsa mata da,
 "Amin Mamana!"

Sai kuma ta juya ga Inna da ba ta tsoma musu baki ba ta ce, "Don Allah Inna ke ma ki yi ha'kuri da bacin ran da na saku".

"Ni ba ki yi mini komai ba Iyah, amma tabbas inda ta ra'ayina za a bi kin gama yin boko tunda ke naki karatun na raini ne, haka siddan ana wahala da ke rana tsaka ki hau iyashegen ke ba kya son makarantar sai an canja miki, alhalin tun farkon samun wannan makarantar kin san ta fi karfinmu, amma kika kafe sai ita, kina kallon yadda yar'uwarki da mijinta suke 'dawainiya da ke, mu ma muna irin namu kokarin tunda wahalhalun makarantar yawa ne da su, sai kuma don kin raina mu ki ce lallai sai kin bar makarantar kin koma wata saboda ki nuna duk wahalar da ake yi akan makarantar ba karatun da'a kike koya ba, na raini ne da iyashege."

Jikin Sa'adah ya sake yin tubus ta san Innarsu mai zafi ce amma a yau yadda take furzar da magana ta san ba karamin fishi ta yi da ita ba. don haka sai ta sake yin kasa da kai ta ce, "Ki yi ha'kuri Inna"

Ta nisa ta ce, "Ke ce da ha'kuri Iyah, domin ina lura da take-takenki, kwatakwata ba ki ajiye kanki kusa ba, ina jiye miki kar ki jefa kanki a *HALIN YAU* na nadama marar amfani".

Sai da Baffa ya sa baki sannan ta ha'kura ta ce ta huce magana ta wuce, Sa'adah da kyar ta mik'e bayan ta musu godiya tare da tabbacin ba za ta sake 'ba ta musu ba.

Kasancewar sanyi ake kadawa yasa uniform din, nan da nan suka bushe, kafin ta kwanta barci sai da ta goge su tas! Sai da ta kammala komai ta kwanta ta fara tunanin yadda za ta kaya a tsakaninsu, anya ma ba zai ga rashin ajinta ba? daga magana daya sai ta hau bare-bare, kodai ta ki zuwa makarantar ne a iya gobe ta yadda idan ta koma zai gane ba saboda shi ta koma ba, tunda yanzu kam ta gane, ba karamar wauta ta yi na barin karatunta saboda wani dalili marar kangado ba?

Da sassafe ta tashi ta yi ayyukan da ta saba yin su, ta karya sannan ta shirya, ta yi wa iyayenta sallama ta karbi kudin makaranta ta tafi bayan sun bi ta da addu'ar albarka da dacewa.

Kai tsaye makarantar ta yi saboda ta san Zainab ta riga ta tafi, tunda ta sha biyo mata, tana cewa ba za ta je ba. Ba irin banbakin da Zainab ba ta mata ba, har ta gaji ta fusata ta daina biyo mata.

Tana shiga class dinsu aka hau ihun murna tare da fadin "Gogel is back!".

Ba su sarara ba sai da Uncle MK ya shiga don yin attendance, ya shiga rarraba ido, ya hango ta zaune kan desk dinta sanye cikin uniform sai daukar ido take yi, ga mamakin ta sai ta ga ya yi kamar bai gan ta ba, bare ya nuna wata alamar ya ji dadin ganin ta.

Ya shiga kiran sunayensu, har aka zo kanta, tana amsawa kuwa ya ba ta umarnin ta mike tsaye, sai da ya kammala gaba'daya sannan ya tambaye ta dalilin rashin zuwanta makaranta tsawon sati biyu, cikin rawar murya ta ce, "Am sick!"

Ya daure fuska sosai, cikin harshen turanci ya ce, "Waye ya zo ya fadi cewar ba ki da lafiya? Ina kuma shaida daga asibiti da makaranta za ta gamsu da gaske rashin lafiya kika yi? Ta rasa me za ta ce, sai ta yi shiru tana mamakinsa, ganin haka yasa ya ce ta fito, ta bi shi zuwa Staffroom.

Bai dake ta ba amma ya yi punished din ta, ta hanyar sata wankin staff toilet wanda duk dalibi ya tsani a sashi wannan aikin. Tana gamawa ya sake cewa ta wanke window glass din Staffroom wanda duk malamin da ya zo wucewa sai ya gan lta, wani ya tambayi me ta yi, wani kuma ya wuce. Mrs Ngozi, Maths Teacher dinsu kuwa sababi ta yi ta mata, tana cewa, "You again? You're rude student." saboda yadda kwanaki ta musu case da Farida.

Zuciyar Sa'adatu kamar ta fashe don bakin ciki, tana aikin tana kuka tana raya ashe da ma so yake ta zo ya ci ubanta shi yasa ya yi tattaki har gidansu ya mata kalamai wanda duk karya ne tsagwaronsu?.

Har aka tashi, tana wannan aikin, kuka ta yi shi kamar idanuwanta su fado kasa.

Koda aka tashin, da kyar Mr. Charles (Chemistry Teacher) ya ro'ki MK akan ya mata afuwa, ya bar ta haka nan, wanda ita a lokacin ta riga da ta fusata ba ma ta bu'katar ya mata afuwar, ai duk tsananinsa dai ba zai raba ta da numfashi ba, sai da aka gama watsewa sannan ya ce ta tafi. Tana kuka sosai ta wuce shi ya ce, "Sa'adah dawo, ba za ki gode mini ba? Takaicinsa ya sha'ke mata wuya, amma sanin halinsa na zai iya janye afuwar da ya yi mata sai ta ce,

 "Thank you!" Cikin kuka.

Zuciyarsa ta yi rauni amma sai ya dake ya kalle ta tana tsugunne cikin kasa, ya tuna yadda ta zo cikin tsabta tana daukar ido amma yanzu ta yi futu-futu ta fita a hayyacinta. Sai ya ce ta jira shi a gate, wajen makarantar ke nan.

Takaicinsa ya sake kamata, amma sai ta amsa da to ba don za ta jira shi 'din ba.

Tana tafiya ita ka'dai kasancewar duk 'daliban sun tafi, tana rayawa ita kuwa mai zai ce mata? Ai kuma ba zai sake yaudararta a karo na biyu ba.

Makaranta dai za ta ci gaba da zuwan ko don zaman lafiyarta da iyayenta, amma In Sha Allah za ta yi iyakar 'ko'kari ta cire MK a ranta, tana shirin tsayar da abin hawa ya cimma ta kusa da ita ya tsayar da mashin dinsa.

Ta dauke kai tamkar ba ta gan shi ba ya ce, "Hau na kai ki".
 Fur ta 'ki, don haka ya sauko ya kafe mashin din, suka gangara inda ba wucewar ababen hawa sannan ya tsaya ya dube ta ya ga yadda ta hade rai tamkar hadari.

Ya nisa ya ce, "Sa'adah are you angry with me?"

Hawayen ba'kin ciki ya ziraro ta ce, "A a, Am happy with you".

Ya san inda ta dosa, don haka sai ya ce, "Saboda Allah kinga ya kamata, ki yi laifi na kasa hukunta ki alhalin dokar makaranta kika karya? Kin san fa, if you want to show an example, you have to start it from your section for them to know you are not a selfish.
 Ke yanzu na san dauka zaki yi da gayya na miki hakan, Ni kuma na rantse miki, ba zan yi son zuciya a cikin aikina ba, don haka ki ri'ke, ki kuma kiyaye".

Ta tura baki irin na sakarci da nuna takaici ba tare da ta ce uffan ba.

Ya nisa ya ce, "Ba za ki daina wannan fishin ba?"

Sake daure fuska ta yi tare da 'kin tankawa.

"Amma kin san na yi farin cikin zuwan ki makaranta yau?"

Sai a lokacin ta fashe, cikin kuka ta ce, "Ni kuma ban yi farin-ciki ko ka'dan ba, sai tarin ba'kin ciki da nadama."






      Alkalamin 
*SURAYYA DAHIRU*.
      ✍🏼✍🏼

1 Comments

Post a Comment