HALIN YAU 30 & 31


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


   


    *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*



        *SADAUKARWA GA*
         *SADIK ABUBAKAR*.








                  30-31.





Kuka sosai ya kwace mata, wanda ya yi matu'kar taba shi, tun a wannan ranar kuma ta gane rauninsa yana motsawa ne idan ya ga tana kuka.

A ki'dime ya shiga tattaro duk wata kalmar sanyaya zuciya, da nuna kololuwar kulawa, duk da ba ha'kuri yake bata ba, tunda shi ya san akan 'ka'idojin makaranta ya hukunta ta, ba ya kuma fatan ya ci amanar aikinsa.

Tsawon lokaci tana kuka, ta koma ajiyar zuciya tunda dama tun safe take yinsa.

Da kyar ya shawo kanta ta yi shiru, sai da ya ga ta nutsu sosai, sannan ya samu sukuni a zuciyarsa, yana mamakin yadda yake jin matsananciyar soyayyarta na ratsa dukkan jikinsa gaba'daya.

Cikin murya marar amo saboda shauki ya ce, "Jiya na ce miki zan zamu yi magana ko?"

Bai jira amsarta ba ya ci gaba da fadin, "Ban yarda ki fada wa wani ko wata cikin makarantar nan abin da ke faruwa a tsakaninmu ba, wannan sirrinmu ne ni da ke da ba zan so ya shiga kunnuwan students ba."

"Sannan bana bu'katar, ki nuna wata alama da students za su fahimci akwai wani abu a tsakaninmu, lastly ki rabu da fitunannen yaron nan (Khalil), ki fita harkarsa in dai kina bu'katar kwanciyar hankalina".
 
Ta yi shiru tana nazari maimakon ta fahimci inda ya nufa sai ta karkace, zuciyarta ta shiga kissima mata ai saboda Farida ne yasa zai ce bai son aji yana sonta banda haka mene ne na boyewa tunda dai aure za su yi ba wata 'barna ba.

Ya gaji da shirunta, ya ce,
"Kina tare da ni kuwa?"

Nan ma shiru ta yi, bai ji dadin shariyar da ta mishi ba, amma sai ya waske, ya san dama haka take, bare kuma yau ya ta'bo ta.

'Kasa ya yi da murya sosai ya sake cewa, "Magana fa nake miki, amma kin yi mini shiru".

Cike da fishi sosai ta ce
 "To ni me zance?"

Zuba mata ido ya yi, yana kallon yadda take ta cika tana batsewa har wani huci take yi, jikinsa ya yi sanyi bai cika son mace mai fusata sosai irin haka ba, sai dai son da yake mata ya riga ya yi bunkasar jurewa duk wani kalubale daga gare ta.
 
Wannan karon ido ya zuba mata, tare da bude murya sosai ya ce, "Ina ta miki magana amma kina jina kin mini shiru, kar ki bari na ji a zuciyata son da na ce ina yi miki shi ne dalilin da za ki fara raina ni".

Kawai sai ganin hawaye ya yi yana tsere a kan kuncinta, tana ta yunkurin bude baki don ta yi magana amma ta kasa.

A ransa yake fadin akwai aiki a gabana, a kankanin lokaci ya gane shagwababbiya ce ta gaske, banda haka mene ne kuma abin kuka a maganar da ya yi? kan dole ya yi ta rarrashi akan ta fada masa abin da yasa ta kuka cikin maganganun da ya yi.

Cike da kukan kuwa ta hau cewa, "Ai an sha fada mini duk saurayin da yake boye kanshi kar a san yana son mace, to ba da gaske yake ba, yaudarar ta zai yi".

Ta 'karasa maganar cike da gunjin kuka, mamakin ta ya kama shi sosai ya ce, "Amma na sha fada miki gidanku ba gidan da zan yi wasa ba ne, tunda kina shakku a kaina a satin nan zan gabatar da kaina a gaban Baffa shike nan?"

Ta goge Hawayen da ya'ki tsaya mata, a hankali ta ce
 "To saboda kar Farida ta sani ne kake son a boye?"

Takaicinta ya kama shi, amma kuma ya kasa yi mata jan ido, sai ma lallaba ta da ya shiga yi, ta hanyar fadin. "Sa'adah ya kamata ki dinga fahimta ta, inda Farida nake so, nake burin aure ba abin da zai kawo ni gunki tunda ba dole aka mini ba! Ribar me zan ci idan na zo don na miki karyar ina son ki? Mahaifinki mutumin kirki ne, na san shi, tun kafin na san ki, akan me zan yaudari yarsa? Ina son ki yarda da ni, yarda ita ce matakin farko a soyayyar gaskiya, abin da yasa nake son mu bar maganar a tsakaninmu ba komai ba ne illa don na kiyaye dokar makaranta!

Ba makarantar da ta yarda malami ya yi soyayya da 'daliba, ni kuma zan yi iyakar'ko'kari na kiyaye kowacce irin dokar makaranta, ta kowacce fuska wannan shi ne gaskiyar magana".

Ta yi kasa da kanta, tana jin nutsuwa da maganganunsa.

Ya nisa ya ce, "Kin yarda da manufata?"

Kai kawai ta 'daga mishi alamar eh, sai ya ce "To ba ki ce komai akan wancan yaron ba"
Ta sake yin kasa da kanta ta ce,

"Ai ni ba saurayina ba ne".

Da sauri ya ce "Magana muke ta gaskiya fa Sa'adah! kin san har letter da kika masa wacce na dauka tana nan, kawai idan kin amince kina sona, to ki fita harkarsa, kin san dai yaro ne karami, da ba zan iya hada soyayyarki da shi ba, ga shi dama ba tarbiya ce ta wadace shi ba".

Kanta tsaye ta ce " To! na ji zan rabu da shi, kai ma kuma ban yarda na dinga ganinta tare da kai ba, kodayaushe tana hanyar staffroom saboda kai, kai ma da ka motsa sunanta ne a bakinka, to ba ita kadai ba ce mai 'kokari ba, ire irenta suna nan, wasu da yawa ma a cikin makarantar sun fita kokarin, ita zubin Sadakar Yallah da kuke gani a tare da ita yasa kuke ga kamar ta fi kowa".
 
Mamaki da dariya suka kamashi lokaci guda, amma ya dake bai bari dariyar ta fito ba, ya ce, "Amma ai na tabbatar miki ba son ta nake ba, sannan kin san dole wani abin zai hada mu tunda dai ni malaminta ne, abin da za ki yarda da shi shine wallahi ba budurwa ta ba ce, ba ni kuma da niyyar auren ta".

"Amma da bakinka kace mini za ka iya maye gurbina da ita".

"Tabbas na fadi hakan amma ki sa a ranki sai idan ke ce kika so faruwar hakan, ina nufin kika juya mini baya, sai na yi maleji da ita a rashin ki, kin san Bahaushe ya ce a rashin uwa, akan yi uwar'daki".

Da'di ya kamata har murmushi ya subuce mata, shi ma ya taya ta murmushin tare da cewa,

"Na rantse miki ban taba ganin wacce ta fi ki kyau a duniyata ba, musamman idan kika murmusa".

Kunya ta kamata tasa dukkan hannunwata ta rufe ido tana jin kamar su tabbata a haka.

Ganin sun dan fahimci juna ka'dan ya ce "To muje ki tafi gida kar aga kin dade da yawa, tunda ba za ki yarda na kai ki ba".

Sai da ya sa ta cikin Adaidaita Sahu ya biya kudin, sai da ya ga sun tafi sannan ya koma ya hau mashin dinsa yana jin shauki na shigarsa, yana kuma jinjina kishin Sa'adah.


       WAYE MK BICHI?

Haifaffen karamar hukumar Bichi ne, a jahar Kano. Mahaifinsa Alhaji Kabiru Wadata, Bafulatanin Bichi ne, mai arziki ne a lokacinsa, don zai shiga cikin jerin attajiran Bichi shi yasa ake masa la'kabi da Wadata. 'Dan kasuwa ne mai sana'ar fata, yana fataucin ta zuwa jahohin Arewa.

Mukhtar shi ne babban dansa na namiji, shi ne kuma na biyar a dukka gidan, an haifi mata hudu kafin shi.

Matan gidan biyu ne Hajiya Babba (Indo), tana da yara bakwai wadda ukun farko dukkan su mata ne, Zainab, Khadija, Amina, kuma duk sun girmi MK, sannan Abbas, Akil, Sameera, da auta Bilkisu.

Sai dakin amaryar gidan wacce ita ce mahaifiyar MK, Hajiya Rabi yaranta uku kacal, Hafsatu ce Babba, sai Mukhtar sannan auta Ahamad, da Mk ya girme masa da shekaru kusan goma

Mahaifin MK mutum ne mai sau'kin kai, mai kokarin wadata iyalinsa da komai na bukatar rayuwa, dukkan su, sunyi karatu, matan dai suna kammala sakandire yake aurar da su, yayin da mazan ke zurfafa karatunsu a jami'o'i daban-daban a cikin kasar nan.

Gidansu akwai zaman lafiya, duk da ba a rasa yan kananun gutsuri tsoma irin na gidan Polygamy Family, amma dai nasu da sauki ainun kasancewar iyayensu matan ba su cika samun sabani ba. Idan ma sun samu to suna bari a tsakaninsu ba tare da sun bari yaransu sun shiga rigimar da ba tasu ba.

Wannan dabi'ar tasu, tasa hankalin mijinsu ya kwanta da su, inda yake musu hidima su da ya'yansu kan jiki kan karfi.

Mahaifinsu a tsaye yake kan sha'anin tarbiya, sannan ya dace da mata na-gari da suke taya shi, dora yaran akan kyakkawar turba, domin kuwa duk yadda namiji ya kai da kula da tarbiyar yara in bai yi dace da mace ta-gari ba, to da wahalar gaske yaran su bi tsarinsa.

Mukhtar ya fara karatunsa a kwalejin ilimi ta tarayya dake garin Bichi, bayan ya kammala sakandiren hadaka ta gwamnatin jaha (Unity Boys Karaye). Sai da ya kammala NCE, sannan ya yi JAMB ta D.E, ya yi sa'a ya samu level 200 a jami'ar Bayero, inda ya karanta harshen turanci (English Language), yana shekara ta biyu ne Allah Ya yi wa mahaifinsu rasuwa a hadarin mota ya je dauko Bilkisu a makarantar kwana, wacce tare suka rasu da Bilkin.

Wannan mutuwa ta matu'kar taba ahalin wannan gidan, dole suka tattara suka ha'kura suka bi su da adduar samun rahamar Ubangiji. 

Haka iyayensu mata suka ci gaba da zama suna ci gaba da kula da ragowar yaran da ke gabansu wanda Sameera ce kawai ta rage ba a aurar ba sai maza su kuma suna ta karatunsu cikin nutsuwa. 

Da ma can suna da sana'oinsu, sai suka samu sau'kin tafiyar da gidan da kuma tallafin 'ya'yansu maza da mata, musamman MK da ya kasance shi ne babba, kuma shi ya debo kusan halin mahaifinsu, na hakuri da yawan kula da lamarin gidan.

Yana da sau'kin kai ta yadda duk yan'uwanshi suna jin da'din mu'amala da shi, kafin ya fusata yana jimawa, amma fa idan ya yi fishin wuyar sauka ne da shi.

Abu mafi kyau cikin halayyar MK Bichi, ma'abocin addini, mai kokarin kiyaye dokoki ne na gaske, sannan duk layin da ba gaskiya, ba za ka same shi a ciki ba. Akidar son bokon da ya taso da ita bai sa ya yi watsi da kyawawan al'adun Malam Bahaushe ba.

Sannan MK ma'abocin 'kamshi ne tun yana Secondary, da kamshinsa ake gane ya zo guri, bayan haka kuma He is Frank and friendly to all.

Wannan ke nan.




     Alkalamin
*SURAYYA DAHIRU*
       ✍🏼✍🏼.
Post a Comment (0)