HALIN YAU 5 & 6


🌺 *HALIN YAU*! 🌺





```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

`

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/

    *SADAUKARWA GABA'DAYA GA*
         *SADIQ ABUBAKAR*



                 
                     5-6

      

 Har 'kofar gidan yayarta Sumayya suka kaita dake kan titin Kwankwaso Gandun Albasa, sannan suka juya,
Baba direba, nata jaddada mata ta daina saurin fushi mabudin fitina ne, ta yi godiya, tana cewa su Zainab sai nan da kwana uku za ta dawo unguwar tasu lokacin innarta ta dawo daga tafiyar da ta yi.

Da sallamarta ta isa cikin katafaren falon Sumayya, ba kowa sai TV da take ta babatu hadi da dan dirin AC da ke tashi a hankali, ga 'kamshin *Air Freshner* dake tashi sannu a hankali, take ta ji duk gajiyar da ta kwaso ta taso mata gabadaya.

Dan haka sai kawai ta zube a Kan doguwar kujera ta yi kwanciyar ta ba ta jima da kwanciyar ba, barci mai nauyi ya yi gaba da ita.

Sumayya fitowa tayi daga bangaren maigidan, da a yammacin yau aka sallamosu daga asibiti, ta ganta tana ta barci. Murmushi ta yi tare da cewa, "Oh a 'yar wannan tafiyar ne kika gaji har haka?" Ta gyara mata rigarta da ta 'dage, ta shige kicin don hada tea.

Hayaniyar yaran gidan ne da suka taso da ga lesson wadda takanas aka dauki malamin da zai zo har gida yana musu bita, yasa ta tashi musamman da 'karamar cikinsu ta fada kanta tana fadin, "Mami yaushe kika dawo?"

"Khairat kin san yadda na gaji!" Ta 'daga ta, tana cewa "Ina Yaya Jawad?"

"Ya na lafiya, ya ce duk yana gaishe ku" 

Ta sake cewa, "Mami bai ba da komai ki bani ba?"

Daga Sumayya har Sa'adah dariya suka yi yadda Khairat din ta yi.

 Jakarta ta bude ta dauko wani dan abu a nade da wrapping paper ta ce, "ga shi nan ni kaina sai da ya ro'ke ni kar na bude tunda ban san ma ya saba, ya dai ce mini zan ga abin Khairat don Allah kar na bude."

Yayansu Ayman wanda shi ma yana da yayu Abba da Khalifa suna Egypt suna karatu, ta nufa tana cewa, "Bude mini yaya!" Nan da nan ko ya hau warwarewa sai ga Lush Cookies Biscuit har guda biyar sai Teddy Bear 🧸 'yar 'karama mai kyau da yar 'karamar takarda an rubuta little Khairat.

Da murna soasai tace "Yaushe to zai dawo Mami?"

Anis ne ya ce, "Sai nan da 6 weeks."

Ta galla mishi harara, "Na tambaye ka ne?" Da yake sa'kuwar shi ce ba su cika jituwa ba. Ta juya ga yayansu,"Yaya Ayman kwana nawa ne a 6 weeks?"

Kai tsaye ya ce mata, "42 days." Da sauri ta ce, "Gobe zan samo stones 42, kullum na dinga minus, ranar da suka 'kare to ranar zai dawo saboda na soya mishi wainar fulawa." 
Dukkan su dariya ta ba su, amma Sa'adah mamakin wayonta take, tana kallon Anis tana tuna daidai lokacin haihuwar sa ta shiga matsaloli masu yawa da Malam.

Shekarunta biyar a duniya amma wayonta da azancinta ya zarce na 'yan shekaru bakwai.
mutumiyar Jawad ce sosai ta fi shiri da shi fiye da yayyenta.

Shi ma kuma haka yake ji da ita musamman da shi ba shi da 'kani ko 'kanwa sai ya tattara dukkan 'kaunar da yaya yake yi wa 'kanwarshi a kanta.
 

      *Bayan kwanaki uku*

 " Iya Iya dai, na san tabbas daga shigarki ba za ki ce mini wai har kin yi barci mai nauyin da za ki kasa jin kuwwar da wayar ke faman yi ba."

Da kanta ta tashi ta leka, ganinta ta yi tana kwance ta 'kudundune ta rufe fuskarta da dukkan hannayenta,
"Kin san Allah? Idan kika bari na shigo ba ki tashi ba sai na ci mutuncinki, ai na san sarai kina ji na"

Tashin ta yi tana murtsika idanuwanta "Ni fa Inna barci nake yi!" Kafin Innar ta yi magana wayar ta sake daukan ruri a karo na uku dan haka ta kafeta da idanuwa, akan dole Sa'adah ta sa hannu ta amsa wayar.

Sannan Inna ta juya ta fita tana fadin, "Shashasha haka ki ke tunanin za mu bar ki ki yi ta zama? Ai tunda kin gama karatun to kuwa wallahi sai dai ki fito da miji cikin jerin wadanda suke son ki dan ba zan yarda da wannan zaman ba. Haka kawai kowa ya zo ki ce bai yi miki ba, kowa bai miki ba, wanda ya yi mikin kuma bai shirya sake zama dake ba. Amma kin kasa gane gaskiya, kin kasa gane ita mace lokacin ta 'kan'kani ne! Bari Baffan naku ya dawo na gaji da halinki!"

Sa'adah kuwa da alatilas ta dauki wayar Alh. Mamman wanda dan majalisar tarayya ne mai ci a yanzu, ya so ta tun tana budurwa, a lokacin yana dan majalisar dokoki na jaha, shi ne har yau yake ta bibiya, tun lokacin budurcinta ta san komai game da shi.

Mutum ne mai yawan kyauta da kyautatawa, ta tabbatar da hakan, ita kanta ta san ya mata 'barin kudi. Tun a lokacin yana da mata biyu da yara takwas wanda wannan dalilin yana cikin dalilin da ya sa ba tayi marmarin ma auren shi ba, Illa dan ta sami rabonta kawai, to yanzu kuma amaryar ce ta rasu shekaru biyu da suka wuce a wurin haihuwa, shi ne yake ta bin kanta ta maye mishi gurbinta, tunda ya riga ya saba da mace biyu ga kuma tsananin 'kaunarta da yake.

A nata bangaren kuwa ba ta fatan 'kaddara ta 'kaddaro ya zamo miji a gareta shi yasa tun watanni shida da suka shude ta yakice shi a dukkan lamarinta, tunda dai kam ai ta riga da samun rabonta🤔.

Ta yi amfani da alfarmar shi ta cimma burinta, da kuma mallakar kayan 'kawa na alfarma, idan ko hakane dole ta yi gaggawan wullar da shi tun kafin reshe ya juye da mujiya.

Uzirin tana aiki ta ba shi akan za ta 'kira shi anjima, murmushi ya yi ya ce, "Ranar da na ga 'kiran ki a wayata Sa'adah tabbas rana ce mai muhimmanci a raina!"

 Ya'ke ta yi tare da fadin, "Aiko idan hakane zan baka mamaki, ka saurare ni zuwa anjima"..

Ba ta jira cewar shi ba ta daste kiran, ta yi wulli da wayar ta na neman tsari da 'kaddarar da za ta hada su zaman aure da wannan mai tulelen ciki.

Kanta ta ji ya cushe musamman yadda Inna ta fara matsa mata a cikin kwanakin nan akan lalle sai ta tsayar da miji cikin manemanta, har zuwa yanzu ba ta jin akwai wani da za ta yi zaman aure da shi kamar Mukhtar Kabir Bichi.

Amma ko shi da ta tabbatar da abu 'daya, ta ha'kura da shi ba dan ba ta so ba sai dan ha'kurin shi yafi.

 Ta kuma gamsu ita ke da laifi da kaso mai yawa na 'kaddarar rabuwar su da Abban Jawad, ta tabbatar ya so ta, son da ba algus amma *HALIN YAU* da rudin 'kawaye ya jefa ta cikin kogin nadama. 
Irin wanda ake cewa tsalle daya mai jefa mutum rijiya, ya yi dubu bai fito ba! A hankali ta koma ta kwanta tana tariyo rayuwar ta, ta baya, tun kafin haduwarta da Mk Bichi. haduwarsu, aurensu, rabuwarsu, har zuwa yau da take jin duniyar ta yi mata daurin goro.

Ashe 'dan Adam baya rabuwa da matsala? Ashe duk matsalar da mace za ta fuskanta indai tana zaune a dakin aurenta matsalar da sauki, akan matsalar rashin auren, da rabuwa da 'ya'yanta? Wanne tabbas mace keda shi a wannan halin na yau, za ta sake samun damar aure a karo na biyu? Idan ta samu din ma ba za ta kauce wa matsalar *HALIN YAU* ba, ko kuma ta tabbata tana aure-aure.

Ta nisa ta tuna wata maganar gyara kayanka, da fasihiyar marubuciya, Fadila lamido inda take fadin, *"Uwa da sadaukarwa aka san ta, domin rayuwarta da ta 'ya'yanta, ta inganta.*'

To shin ita me ta yi ne dan ganin ta SADAUKAR da komi dan inganta kanta da tilo 'danta? Tabbas ba ta yi ko mai ba, sai rusa farincikin kanta dana 'danta Jawad! Ta yi dalilin da yake rayuwa ba a tsakanin uwa da uba ba, hawaye ya gangaro mata na takaici da kaico iri iri.

Ta tuna wani darensu a Abuja, ya dinga rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta su zauna lafiya, komai take so zai dinga yi mata a hankali, a lokacin ita kuma tana ganin tamkar idan ba ita, ba zai iya rayuwa ba, saboda yadda yake tsananin sonta da kulafacin son zama da ita, duk yadda take ganin aibun su Halima, a yanzu da take fuskantar NADAMAR biyewa Halayyar yau, ta fi ganin aibun kanta da kanta, tabbas zuciyarta da tunanin ta basu mata adalci ba, domin tunda ta taso take jin ana azanci da cewa idan mafa'din magana wawane majiyinta ba zai zama wawa ba, amma ita sai ta zama mahaukaciya ma.

Zuciyarta ta sake ba'ki wani irin numfarfashi take yi tamkar mai fama da cutar Asma, hakanan hawayen ba'kin ciki ya kwace mata tamkar mai yin Takaba.


 

```Alkalamin 
SURAYYA DAHIRU ```✍🏼✍🏼
Post a Comment (0)