HALIN YAU 7 & 8

🌺 *HALIN YAU*! 🌺





https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/


      *SADAUKARWA GA*
    *SADIQ ABUBAKAR*.



      
                 7-8





HAWAYEN nadama marar amfani ya ci gaba da zuba da ga kyawawan idanuwanta ba 'ka'kkautawa, a hankali ta koma ta kwanta, zuciya na suya, rabon da ta shiga irin wannan yanayin tun shekarun baya da suka shude.

Shekarun da suka fi kowanne tsauri da tsanani a rayuwarta, a lokacin da ta dinga yun'kurin gyara kuskurenta amma MK bai ba ta wannan damar ba.

Duk da ta san ita ke da kaso mai yawa na lalacewar aurensu, tunda ba irin 'kabali da ba'adin da bai mata ba, ba kalar rarrashin da bai yi mata ba. amma tasa hannu har da 'kafafu ta tankwabar da dukkan ha'kurinsa, ta tabbatar akan dole ya rabu da ita, ita kanta ta shaida hakan.

Tissue tasa ta goge hawayen da ya 'ki yankewa, take kuma zuciyarta ta yi tsalle ta hasko mata irin kyaun da ya yi cikin tufafin da take matu'kar son ganin sa a ciki wato farin kaya, sam ba ya girma, ba wanda zai kalle shi yace ya kai shekaru arba'in har da biyu.

Dan kuwa idan ya ce bai yi auren fari ba, ba wanda zai 'karyata shi, Ubangiji ya mishi kyakkawan jiki matu'ka gaya.

Murmushi mai hade da hawaye take yi lokaci guda, saboda yadda ta ji a ranta da zuciyarta domin ita ya yi shigar tare da fatan ko Allah zai sa su hadu, a hankali ta fara jin sau'kin 'kullewar da 'kirjinta ya yi yana raguwa, a dalilin tabbacin da ta sake samu na har yau shi ma yana son ta, dama idan akwai abin data yarda dashi to son da ya ke mata ne. Amma kuma me yasa bai yarda da ita ba?

Nan da nan 'kuncin 'kirjinta da ya fara warwarewa ya dawo ya 'kulle fiye da farko idan akwai abin da yake 'daga mata hankali bai wuce rashin amincin daya jefe ta da shi ba, alhalin shine mutum na farko daya kamata ya shede ta,
ta kuma zama amintacciya a idonsa, kuka ya 'kwace mata sosai, da sauri tasa hannu ta rufe bakinta dan kar Inna ta jiyo.

Haka ta danna kanta a pillow ta yi kuka mai nuna tsantsar bakin ciki da takaicin da mai yinsa ke ciki, duk yadda zuciyarta ta yi zafi, kanta take 'kalubalanta, ta san ko mai Malam ya yi ko ya ce mata, ba shakka ita ce sila, ita ta janyo.

Istigifari ta dinga ambato dan ta sami sau'kin zuciyarta, tsawon lokaci kafin ta ji ta fara samun nutsuwa sai ajiyar zuciya take saukewa.

Wayarta ta dauko tana nazarin shin a littafi zata rubuta ne ko a waya? A littafin tafi gamusuwa da ta rubuta tarihin rayuwarta dan ya zama izna ga sauran mata. Idan ta sami halin buga shi, za ta buga dan ya zama gargadi ga duk wacce son zuciya da *HALIN YAU* ke dawainiya da ita.

Mi'kewa ta yi tana laluben littafi da biro a cikin jakar karatunta, amma cikin rashin sa'a ba ta samu ba, kowanne ta yi rubutu mai yawa a ciki.

Tsaki ta ja, ta rike 'kugu kafin ta yi wani yun'kurin abin yi, ta ji sallamar almajirinsu yana fadin na dawo.

Da sauri ta iso ga katifarta, ta 'daga pillow ta dauki gudar dari biyar ta fita ta ba shi, ya siyo mata littafi na rubutu mai shafi tamanin (80 leaves).

Daga nan ba ta dawo dakin ba, buta ta dauka dan tayi alwalar la'asar tunda yan mintina ka'dan ne su ka rage.

                       *****

Kwance ya ke kan sofa a dakin barcinsa, ya lumshe ido tamkar mai barci amma a zahiri ba barcin yake yi ba.

Tun ranar da ya ga Sa'adah nutsuwa ta masa tutsu duk yadda ya kai ga daurewa har abin ya bayyana a fuskarsa da gangar jikinsa gaba'daya.

Wata irin nutsuwa ya gani a tare da ita, wadda bai taba gani a tare da ita ba, gaba'daya ta canja, ilimi da hankali sun matu'kar ratsa ta. ba kamar lokacin da suka rayu tare ba. ko dan ya dauki lokaci mai yawa bai ganta ba ne?
 
Farida ce ta shiga dakin, kusa da 'kafafuwansa ta zauna tana mai jan yatsun 'kafarshi, a hankali cikin sanyin murya da halittarta ce, ta 'kira shi "Abban Jawad!"

Bai amsa ba, amma ya bude idanuwanshi da suka yi ja alamun ko barci bai ishe su ba ko kuma ana cikin damuwa.

Ta sake nazartar shi a hankali ta ce, "Tunda ka dawo na kasa gane maka, na san akwai abin da ke damun ka amma ka'ki fada mini, ni kuma na san matsalar! Idan na yi rantsuwa cewar Sa'adah ke da ala'ka da wannan damuwar da kake ciki ba zan yi kaffara ba, mai yasa ba za ka yafe mata ba, mai yasa ba zaka daina wahalar da zukatanku ba, me yasa kake gudun gaskiya da gangan? Ni dai na san ', kullaci, da rashin yafiya ba halayyarka ba ce!

 Ban san me yasa ka aro ka yafa akan Sa'adah ba! yau shekaru kusan bakwai kana ta wahalar da zukatanku, sai yaushe za ka hutar da ku? ko makaho ya ji halin da kake ciki yasan kana sonta, balle ni da nake tare da kai, na ro'ke ka ka gaggauta gyara tsakaninku, tun kawaicina bai 'kare ba, tun ban fara kishi da ita kamar yadda take yi dani ba, na tabbatar idan hakan ta faru ba zaka samu nutsuwa ba!"

Sai a lokacin ya bu'de baki murya ba amo ya ce, "Kece kike ganin haka duk yadda kike tunanin lamarin ba haka ba ne, kinsan kuma ban taba 'karyar ba zan dawo da ita ba, saboda Ubangiji ne ke jujjuya lamura, idan ya 'kaddara sake zama a tsakaninmu zan dawo da ita."

"Zuwa yaushe za ka dawo da ita din? Ka fi shekaru uku kana wannan maganar, ba irin girman kanta da ba ta ajiye ta baka ha'kuri ba, ni kaina na sha ganin ta tsugunne a gabanka. haba Abban Jawad! Wanne irin abu ne haka da ba zai wuce ba?" 
Ta fada muryar ta na karyewa.

Shi kansa bai san mai yasa ya shiga ru'du a dalilin halin ko in kular da Sa'adah ta mishi ba, da kuma yadda ta daki 'dansa a gabansa, alhalin kuma tun tuni ta san baya son ta masa haka a gabansa. Amma saboda da ta nuna masa ba shi da sauran gurbi a zuciyarta, ba shi da mutunci a idonta ta rufe Jawad da duka akan idonsa.

Sannan a gaban jama'a ya tsaya dan ya taimake su amma ta wula'kanta shi, ta nuna masa iyakarsa, idan ya tuna wadannan abubuwan sai ya ji har zazzabi ne ke neman kama shi, hakan na nufin Sa'adah ta daina son sa, ta ha'kura da shi ke nan? Zuciyarsa na bugawa idan ta hasaso masa cewar ta samu wanda take so, ko kuma za ta sabunta soyayyarta da Khalil Ibrahim wanda yake jin komai na iya faruwa da shi idan hakan ta faru.

Ya nisa ya ce, "Ke fa duk yadda kike tunanin lamarin Sa'adah ya kerewa tunaninki, yanzu bata so na, ba ta da burin sake zama da ni"

A yadda ya yi maganar ta san akwai abin da ya gani a tare da ita da ya jefa shi cikin wannan yanayin.

 Wata'kila ta gaji da bin kansa, ta tattara ta jefa shi a kwandon shara, kamar yadda ya mata, shine kuma dan son kai irin na namiji zai ji an masa rashin kyautatawa, su dai sun fi son mace ta yi ta bin su, suna jan ta a 'kasa.

"A hankali cikin son 'karfafa masa guiwa ta ce, "To ina ruwanka da soyayyarta? Ina tabbatar maka son da kake mata ya isa ya ri'ke auranku, muhimmin da za ka damu da shi mutuncinka a idonta, balle ma nasan nan duniya ba namijin da take so sama da kai, ba kuma wanda zai zarce ka a gunta. Wata'kila ta gaji da yadda kake tamaula da ita ne, ko ba ta ci albarkacin so ba, taci albarkacin Jawad! ko ka san Jawad, komai zan yi masa ba zai gamsu ba, matu'kar ba uwarshi ya gani a tare da kai ba"

Idonta ya dan ciko, ta dan tsahirta sannan ta ci gaba da magana, "nan gaba Jawad zai tattara dukkan tsana ya dora mini, zai ga saboda ni ka 'ki zama da uwarsa, kai ma kasan tunda muka dawo 'kasar nan ya canja, na ro'keka dear kar ka ruguza farinciki da kwanciyar hankalinka da na 'danka"

Janyo ta jikinsa sosai ya yi, ya ri'ke hannunta ya kalleta sosai ya ce ,"Farida ke din mai kirki ce, mai ha'kuri ce, mai sanin ya kamata ce, kina sona kina son kwanciyar hankalina, ina yaba miki, ina kuma fatan Allah ya fi ni yabawa, Allah ya ba mu zuria dayyiba!"

 Hawayen da take ma'kalewa ya zubo a kan fuskarta ta ce, "Ni da ban da lafiya ne zan haihu?"

Cikin kulawa mai yawa ya ce, "To menene ya gagari Ubangiji? Son da nake miki wallahi ko ban taba haihuwa ba, zan zauna dake a haka domin ke nake so ba wani abin da zan samu a gareki ba, sannan rashin haihuwarki kullum ke sa na ji son ki da tausayinki na sake cika mini dukkan zuciyata, ina son ki da ke da dukkan lalurarki Farida!"

Sai kawai ta fada jikinsa tasa mishi kuka, shi kuma yana dan bubbuga bayanta, yana jin ina ma zai iya bude mata 'kirjinsa dan taga 'kololuwar matsayinta a zuciyarsa?.

Ya tabbatar bata san yadda yake jin ta a Zuciyarsa ba ne.


```Alkalamin 
SURAYYA DAHIRU```✍🏼✍🏼

Post a Comment (0)