HALIN YAU 9 & 10


🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•
      

    _GAISUWAR GIRMA GA_
  *HAJ HAFSAT SODANGI*
_(MIJIN TACE)_


             9-10.


Tsawon lokaci suna wannan halin har ya samu nasarar dawo mata da walwalarta,
"To kawo mini abincin nan mu ci don nasan ke ma ba ki ci ba".

Ta yun'kura tana cewa, "Ina zan iya ci alhalin mijina bai ci ba!" Kicin ta nufa ta hada komi a kan faranti ta kinkima ta yi dakin nashi kamar yadda ya ba ta umarni, Sai da ta shimfida ledar cin abinci sannan ta zuba musu abincin a faffadan plate, shinkafa da miyar kifi ne, sai hadin Salad, gefe kuma zobo ne wanda ta sarrafa da tsurar sugar da cocomber sai flavour.
Ba ka jin komai sai karo tsakanin cokali da plate kasancewar shi ba ya magana idan yana cin abinci.

Suna gamawa ta kwashe komai ta gyara wajen sannan ta hada masa ruwan wanka ya shiga. Ta fice zuwa nata dakin, ta fito falo sukayi kicibus da shi, ya fito cikin lallausan yadi mai kalar sararin samaniya,(Skye blue) bai dora hula ba, amma ya taje sumar nan da ta cika kan fam! Ya dora farin glass a idanuwanshi, sai tsadden kamshin turaren Versace ne ke tashi a jikinsa.

Kugu ta rike ta zuba mishi ido tana murmushi ta ce, "Na san mijina gwanin iya wanka ne, amma irin wannan kwalliya haka da La'asariyar nan! Sai ina? ko wurin Iya Basiru za a?"

Ya fashe da dariyar tuna baya, sai ya ce, "Kinsan fa har yau fadanta na nan lalle idan ta ji wannan sunan kin san 'yan kallo zaku kwasa."

Ita ma cikin dariya sosai ta ce, "Ai na san yanzu ta girma da fada, ka san me?"

Ya girgiza kanshi, "Ada idan mun hadu sai na faki idon mutane naga ba kowa, sai na ce mata Sa'ade ko na ce Iya Basiru, sai na ga ta fara sababi, kawai sai na sulale na bar ta a wajen."

Ya sake sakin dariya "Ashe ke ce kike tsokanar ta duk mu hadu a ba ta rashin gaskiya?"

"E to ai haushi nake a lokacin, ta dauke maka hankali, har sai da ta kwace mini kai!" 

Ya nuna ta da yatsa, "ke ko! kin san irin su Sa'adah suna dadewa kafin a gane cutar su da ake yi, saboda hayaniyarsu sai sun dade kafin a gane a fahimci gaskiyarsu. yau kwana biyu ban je gidan Hajiya ba can na nufa idan kuma za ki dauko mayafinki, Bismillah".

Kai ta girgiza alamar a'a tare da cewa, "Na fi son na je na wuni, ka gaishe ta da kyau!" 
Ya fice ita kuma ta bi shi da addu'ar dawowa lafiya.

Da sallama ya shiga gidan, a tsakar gidan ya same ta zaune kan tabarma tana jin radio, kusa da ita ya zauna. suka gaisa tana tambayar Farida, daga nan kuma tayi shiru da bakinta.

"Hajiya wai har yau fishin rashin zuwanki wurin Jawad din ne? Ni ma fa ban ji da wuri ba, ina Bauchi ya yi mini waya daga can na zarce amma ki yi mini uziri, kiyi hakuri."

"Ni abin da ya dame ni, ba a kai masa abinci da 'yar miya ba!" 

Dariya ya yi sannan ya ce, "Ai yanzu ba a barin su su tafi da shi hostel, iya wanda suka ci a wajen shike nan, saboda kwalara sannan kuma a can na tarar da uwarshi ta je masa da abincin". 

Shiru Hajiyar ta yi tana jin takaici rashin Sa'adah cikin ahalinta, ba karamar asara ba ce. Tunda ita kam a iya zamanta da yarinyar ba za ta ce ga ta'kamaiman laifinta ba, sai yan 'kananun kura-kurai da ko 'danka na cikinka wani lokacin zai yi maka.

Duk artabun da ake yi tsakanin uwar miji da surukan zamani ita ba ta san shi a zamanin zaman Sa'adah ba, yarinyar ta iya zama da manya.

Komin fa'da da rashin ha'kurinta, ita dai ba ta ganin su, tunda dai mafi yawa akan kishi take fadan. duk mace kuwa ba a raba ta da kishi, sai dai wata ta iya dannewa wata kuma nata mai zafi ne.

Sannan abu mafi dadi a halayen Sa'adah yadda ta yarda ta isa da ita, duk yadda ta murde, da zarar tasa baki za ta ha'kura ta bar maganar. Amma ga shi nan, shi da ta haifa ta kasa sarrafa shi, akan komen yarinyar, shi yasa take jin kunyarta, take jin nauyin iyayenta, duk da aure rai ne da shi, Ubangiji idan ya 'karar da zama ba yadda za ayi.

Ta kalle shi, "Kuma kun gaisa da ita?" 

Tausayin uwarsa ya tsirga mishi ya san babban burinta Sa'adah ta sake zama surukarta a karo na biyu, ya yi 'dan murmushi "Hajiya ai da ma muna gaisawa"

Harara ta galla mishi tare da cewa, "Ina ce nan da ta zo duba Jawad akan idona ba ku gaisa ba?"

"An yi haka Hajiya amma ai ba ni zan gaishe ta ba ko?"

"Kai ne namiji, Kai ne zaka fara magana tunda gidanku ta zo, kuma uwar dan ka ce!"

"To ni Hajiya ba uban 'dan nata ba ne?"

Kwafa ta yi, "Wallahi ba ka ta ba bata mini rai na ji zafinka sosai ba sai akan Sa'adatu."

Kai tsaye ya ce, "Na ba ki ha'kuri Hajiya! yanzu ma shi zan ba ki, ki yi ha'kuri ki yi mana adddu'a."

"To tun yaushe nake adduar?" Niyya ce dai da ba ka yi ba!"

Ya katse mata fadan nata ta hanyar cewa, "Da kyar fa Jawad ya sa ta gaishe ni, kuma na taho a hanya na ga motarsu ta lalace, wai ni da abin arziki, na tsaya na ce su zo mu taho amma yarinyar nan a gaban jama'a ta tsinka ni! Ko kallon tsiya ba ta mini ba, bare na arziki."

Ya nisa sannan ya ci gaba da fadin, "Amma kullum sai ki yi ta dora mini laifi, ki yi ta ganin ni ne marar kirki, alhalin tsiyarta tafi ta tsohuwar mota. Inda tana son sake zama da ni ai lallaba ni za ta ci gaba da yi, tunda dai ta san ba na son rashin kunya."

Tunda ya fara magana ta zuba masa ido tana nazarta shi, tsawon shekaru bakwai da rabuwarsu, yau ne ya bude baki yake magana mai tsayi a kanta. Ta kuma lura da sassauci da afuwa mai yawa akan lamuranta a yau, ta tuno farkon rabuwarsu da ta nuna iko irin na uwa, akan sai ya mayar da ita tilas, yasa mata kuka riris lamarin da yasa ta janye takunkumin dolen da ta mishi.

Yana rufe baki ta ce, "To saboda Allah wanne irin ha'kuri ne bata ba ka ba? So kake ta tabbata tana bin ka kana walagigi da ita? kuma ko don ka nuna na isa da kai, ka ji abin da na ke fada maka, saboda rayuwar 'danku ta inganta, yau yaro ba abu mai dadi a wajensa irin ya bude ido ya gan shi a tsakanin uwa da uba. Amma ku iyayen yanzu ba ku cika duba wannan matsalar ba."

Ajiyar zuciya ya saki, "To shike nan Hajiya In sha Allah zan je na yi istikara ba za ta gagara ba!" 

Nan da nan Hajiya ta hau murna har da hawaye take sharewa tana kuma fadin, "Na gode, Allah ya tabbatar da alheri, da ikon Allah akwai alheri tsakaninku. Duk ba'kin cikin da na kwashe shekarun nan a cikinsa, wannan maganar kadai ta sanyaya min zuciyata, Allah ya yi maka albarka."


Ta mi'ka hannu ta dauko wayarta, "Kira mini Yayar ku".

Ya karbi wayar yana cewa, "Me za ki ce mata?"

"Na shaida mata wannan abin arz'kin mana, duk wannan bacin ran ai da ita muke yinsa!" 

Ya kalle ta, "Amma Hajiya na ce sai na yi istikara fa, idan kuma ban sami nutsuwa da abin ba, a zo a ce na yi baki biyu? Ni dai na ro'keki, ki yi shiru da bakinki, mu yi addu'a nan da kwana uku muga mai Ubangiji zai rinjayar mana a zuciya."

Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Da ikon Allah ma alheri ne, jiya mun gaisa da Ahmad." 

Ta fada cikin jin dadi,"Ai ni tun ina Bauchi rabon da mu gaisa ya ce mini wai satin sama zai zo."

Addu'a ta bi shi da ita kamar kullum, ya mi'ke, "Hajiya bari na tafi Magariba ta kawo kai"

"To ka gaida Farida, ya jikin nata dai?"

"Da sauki da na ce ta zo mu taho tare, ta ce yini ta ke so ta zo ta yi miki."

"Ina zuba ido Allah Ya kawota lafiya."

Ya amsa da "Amin!" Ya fice yana fadin, "Allah Ya tashe mu lafiya."

Ta bi shi da kallon 'kauna zuciyarta fes! Tamkar wacce aka mayar da aurensa da uwar dansa haka take ji. Ta san shi kansa sai ya fi samun nutsuwa idan yana tare da Sa'adah saboda ita shaida ce na tsananin son da yake mata.
ta tuna jinyar da ya yi a dakinta a dalilin rabuwarsu.

Abin kuma da ke ba ta mamaki yadda har yau bai ta ba bude baki ya ce ga sanadin rabuwar tasu ba, ita ma Sa'adah ba yadda ba a yi ba ta'ki fada, lamarin da kowa ya kyale su aka bi su da addu'ar alheri.

Duk irin sha'kuwa da aminci da ke tsakanin Sa'adah da Baffanta, ko shi ta'ki fada masa dalili. Haka ma Mk duk yadda yake jin nauyin surukin nasa bai iya fada masa dalilin rabuwar tasu ba, illa ya ro'ke shi, akan kar ya yi fushi ko ya ga laifinsa, ko rashin kirkinsa akan sun rabu da Sa'adah. 'Kadarrar su ce haka, shi ma kuma Baffan bai zafafa ba, bai kuma takura sai ya ji dalilin ba, ya yi ammana tunda suke boye sirrinsu da alamun za su iya yi wa junansu afuwa a gaba, duk kuwa da a farkon mutuwar auren hana Sa'adah zaman gidansa yayi.

              ****

Bayan yaron ya kawo mata littafin, ta dauko al'kalami ta fara, ta yi layi kamar uku ta goge tana ganin bai tsaru ba, ta ina za ta fara ne?

Daga haihuwarta har zuwa girmanta, ko kuwa daga rayuwar makaranta inda nan ne mafari tsakaninta da MK Bichi, ko kuwa ta rayuwar aurensu za ta fara?

Ashe rubuta labari da tsarawa ma iyawa ne? Lalle a gaida marubutanmu.

Sau uku tana yi tana sokewa, ta tabbatar dai ba za ta iya ba, tunda ba ta taba ba, ai ko za ta ne mi wata cikin fasihan marubuta, ta bata labarin ita kuma ta fasashi ya zama littafi. Ta tabbatar ba za a rasa darasi da jan kunne cikin rayuwarta ba.


    Alkalamin
 SURAYYA DAHIRU
        ✍️✍️
Post a Comment (0)