JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 07
.
LUT AS
Asalin sunannan ba mummuna ba ne, yana nufin haduwar wani abu ne da wani ya garwaya, Allah SW ya san dalilin da ya sa aka saka masa wannan sunan, ya yi zamani da Ibrahim AS ne a Iraqi, mahaifinsa Haaraaan, yaya ko qani ga Ibrahim AS, ya shaqu da shi sosai, shi ya sa ma da zai bar Iraqin suka baro tare zuwa Jordan, sai Ibrahim ya wuce zuwa Palestine ya bar Lut AS anan Jordan daidai inda Mataccen Tekunnan yake a yau, an kira shi da Mataccen Teku ne saboda ba wani abu mai rai da yake iya rayuwa a ciki, wata qila saboda matsanancin gishirin da yake ciki ne, don ya ninka sauran tekuna har sau 9.
.
Nan ne wurin da ya fi ko ina kwari a duniya, kimanin mita 400 qasa da ma'aunin teku, kenan in mun fahimci abinda Qur'ani yake nufi da "Adnal ard" wuri mafi kwari to anan ne za a gwabza da Turawa nan gaba, kodai tsakaninsu da Iran ko ya zama yaqin duniya, Allah ne mafi sani. Lut AS dai ya rayu acan ne tare da mutanensa, su kuma shagalallu ne na qarshe, banda barna ba abinda suke yi, maza su bi maza mata su bi mata.
.
To sai Allah SW ya aiki Lut AS wurinsu, kan iyaka ne tsakanin Duffatul garbiyya dake Plastine ta sama, Isra'ila ta qasa sai Jordan ta gabashi, fadin wurin a yau ya kai 17km, tsawonsa kuwa ya kai 70km, a zagaye gaba daya 650km², kenan ba qaramin gari ba ne, amma da suka lalace suka watsar da tauhidi da bauta wa mahalicci sai Allah SW ya halakar da su gaba daya ya zamanto ba wata barna kuma sai koyarwar muslunci, daganan muslunci ya ci gaba da jagoranci, don an halakar da mabarnatan dukansu, Allah SW ya hana mutane su sake zama a wurin ta yadda wurin ya zama teku, tekun da dabba ma ba ta iya rayuwa a ciki, ko mutum ya shiga ga shi dai ruwa ne amma ba zai nutse ba, zina bala'i ce bare ludu da madigo.
.
Wannan qissar tana da alaqa da maganar Musa AS da banu Isra'ila, domin kuwa Allah SW ya kawo qissar Lut AS ne a Suratu Hud, yana gamawa sai ya shiga qissar Shu'aib AS, inda yake ce wa mutanensa (وما قوم لوط منكم ببعيد) masana sun fassara shi da cewa (Ai mutanen Ludu ba nesa suke da ku ba) nisar wuri kenan ba na zamani ba, domin tsakanin inda mutanen Shu'aibun AS suka rayu zuwa wannan tekun na Lut AS duk bai wuce 20km ba.
.
Zamani kuwa ai Lut ya yi zamani da Ibrahim AS ne, ko kafin Annabi Yusuf shekaru ne masu yawa bare kuma lokacin Annabi Musa wanda shi ne ya yi zamani da Shu'aib AS, wato kenan tsakanin garin Shu'aib da na Lut ba wani nisa ne da shi ba, mun ma fadi kwatankwacin tsawon, Qissar Lut ta zo yanzu ne don kusantar wurin zaman da alaqar dake tsakanin qissoshin, da mutanen da suka rayu a wurin, da irin saba wa Allan da suka yi da ma matakin da Allah SW ya dauka a kansu.
.
SHU'AIB AS
Annabi Shu'aib AS sananne ne a wurin mafi yawan mutane saboda qissar Musa AS da Fir'auna, lokacin da Musa AS ya kuskure wani Baqibde har ya mutu aka sake kwatawa Fir'auna ya sa a kamo shi lokacin ya bar Masar ta Suwais ya isa har Madayana, wato wurin da Shu'aib AS yake kenan, duk wannan ya faru ne cikin hikimar Allah da hukuncinsa, inda aka cire masa rayuwarsa ta gidan sarauta da ya yi a baya, ya dauki wata sabuwar rayuwa ta masamman a shirinsa na karbar wahayi, ya kwashe shekaru yana kiwo a matsayin sadakin diyar Shu'aib AS, a daya hannun kuma yana karbar wata tarbiyya ta masamman don zama manzon Allah, bayan ya baro Madayan da iyalinsa zuwa Palestine nan tsakankanin ya karbi wahayin farko don fuskantar Fir'auna da mutanensa.
.
Wannan wuri yana da matuqar mahimmanci a rayuwar Annabi Musa AS, domin shi ne wurin da zai iya zama mazauninsa da sauran banu Isra'ila in zamansu a Masar bai yuwu ba, ya karbi duk abinda ya dace ya karba a wurin Shu'aib AS ciki har da sandar da ya riqa kiwo da ita, mun karanta tarihin Musa AS da wannan sandar, har a qarshe aka ce da ita ya daki teku har suka sami damar tsallakawa, Qur'ani ya tabbatar da cewa ya riqa sakin sandar ta zama qatotuwar Mesa, tabbas mu'ujiza ce da Allah SW ya ba shi.
.
To shi Shu'aibun AS a Madyan yake, wato daga Tabuka dake cikin Saudia har zuwa cikin Jordan gabas da Tekun Lut AS, da kansa ya ce "Ai mutanen Ludu ba nesa suke da ku ba" ba shakka ya hadu da kafurci da saba wa Allah mahalicci kamar dai sauran Annabawan da suka gabace shi, mutanensa sun riqa bautar gunki, da tauye mudu, da wasu nau'uka na barna kala daban-daban (Suratu Hud 83-94) haka suka ci gaba da saba wa Allah duk da gargadin da Annabinsu Shu'aib ya yi musu, har ya kawo musu labarin mutanen Nuh AS, Adawa mutanen Hud AS, da Samudawa mutanen Salih AS amma sam gargadin bai yi amfani ba.
.
Sai ma ce masa suka yi {Kai Shu'aibu wai sallolinka ne suke umurtanka da mu bar abinda uwayemmu suke bauta mawa ko mu yi abinda muka ga dama da dukiyoyimmu? Gaskiya kai mutum ne mai kawaici, shiryayye!} Suratu Hud87. Isgili kala daban-daban har sai da azabar Allah wato tsawa ta kama su aka halakar da su kamar mutanen Hud AS, muslunci ya sake dawowa da qarfinsa ya karbi jagoranci kamar yadda yake a baya, don Allah SW ya kubutar da Shu'aibu AS da mutanensa, su ne dai za su khalifanci qasa matuqar ba su saba wa karantarwar da Annabinsu yake musu ta kadaita Allah ba.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248