JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 06


JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 06
.
Duk wani kafurci na duniya da ka sani a hankali yake farawa har ya gagara, daga lokacin da mutane suka fara tsarkake wani dan adam an kama hanya kenan, zuwa lokacin da za su fara daukar maganarsa kamar shari'a, to ko ya mutu za su riqa tuno shi suna ganin kamar yana da wani tasiri a rayuwa, sai a riqa zuwa qabarinsa ana neman taimakonsa, ko a ajiye hotunansa ana roqonsu, abinda ya faru da kafuran Annabi Nuh AS kenan, shin mun tsira a yau ba mu tunanin salihan bayinnan da suka rasu har yanzu za su iya yi mana wani abu? To wannan kafurcin yana da iyaka amma bayan wasu shekaru sai aka zo inda Fir'auna yake ganin shi ma fa Allah ne, yake cewa {Ni ne babban ubangijinku} suratun Nazi'at.
.
Abin ya girmama don an kai ga yadda dan adam zai yi iqirarin rububiyya, wato allantaka, in da Allah SW ya so sai ya turo wasu 'yan adam din su yaqe su su karkashe su, su amshe mulkin sannan su maida su muslunci da qarfin tuwo, wanda ya qi a aika shi lahira, amma sai ya turo manzanni Musa AS da Harun AS, ya gaya musu irin maganar ma da za su yi Fir'auna don dai su shawo kansa ya dawo cikin addini, ba shakka manzannin sun hadu da qalu-bale na qaryatawar jama'arsu, da jifarsu da tsafi da aka yi, ga gargadi na kisa kala daban-daban, amma suka jure, suka ci gaba da kiran mutane zuwa ga tauhidi wato kadaita Allah, kar mutum ya taba jin cewa aljannarsa na da alaqa da sunkuya wa wani dan adam.
.
To bayan da'awa da nuna gaskiyar manzanci sai Fir'auna da mutanensa suka yi girman kai, wannan ya sa Allah SW ya umurci Musa da Harun AS da sauran jama'arsu da su bar Masar su koma matsuguninsu na farko wato Palastinu, inda suka baro tun zamanin Annabi Yusuf AS, amma fa daga inda suke ba hanya sai an tsallake jelar tekun Maliya, haka Musa AS da sauran jama'a suka surfafo tekun domin su kubuta daga qasqanci da wulaqanci gami da bautarwa, ba domin dauki daga Allah ba ba yadda za su ci nasara, haka Allah ya ba wa Musa AS mu'ujizar rabewar teku da nutsewar Fir'auna da mutanensa (Nazariyyatut tagyeer na Munir Shafiq p1)
.
Akwai wasu manya-manyan dalilai da suka tilasta yin hijirar matuqar suna so su ci gaba da bautar Allah SW, dalilan sun hada da (1) Siyasa: Qibdawa ne kadai keda iko na shugabanci (2) Tsarin rayuwa: An riga an maida su bayi (3) Yanayin wuri: Masar wurin mulki ne ba bauta ba. Matakin farko na hijira shi ne su sakankance da Allah SW da taimakonsa ga masu bauta masa masamman a kan manhajin da ya shar'anta.
.
Bayan Annabi Nuh AS akwai Annabi Hud AS, malamai sun yi ta sabani wurin tabbatar da inda ya rayu, wasu na ganin a Masar ne, wasu sun tabbatar ma a mararrabar kogin Nil ne inda ya rarrabu ya zuba a tekun Tsakiya, wasu kuma suka ce a Yaman ne, a wani gari da ake kira yanzu haka Ahqab, sai dai an kawar da maganar duk da cewa har yanzu akwai Saba a Yaman, kuma tarihi ya tabbatar da cewa nan ne sarauniya Bilqis ta rayu, a kwai wadanda Suka ce a tsakani qasashen Saudiya, Yaman da Oman Annabi Hud AS ya rayu.
.
Mohammed Salih Al-Munajjid a fatawarsa ta (225177) ya tabbatar da cewa irin wannan binciken sanin haqiqaninsa sai dai Allah SW, banda haka sauran duk harsashe ne kawai, to bayan halakar da mutanen Nuh AS sai mutanen Hud AS da ya sami kansa a cikin Adawa, tarihi ya tabbatar da cewa Larabawan qararriyar qabilannan ce ta Ba'ida, kenan suna da alaqa da Yaman din, to bayan halakar da mutanen Nuh AS muslunci ya yi qarfi, sai dai kuma al'ummar Adawan sun koma bautar gumaka da sauran barna, haka Allah ya halakar da su da tsawa, ya dawo wa muslunci da izzarsa da jagorancinsa, shi ne da kansa ya halakar da su bayan gamsasshiyar hujja.
.
Sai Kuma Samudawa, su ma suna da tsatson Larabawan ne, masana tarihi na ganin cewa a Mada'in suka rayu nan cikin Saudiya, su ma sun juya baya ne, suka qaryata manzonsu, suka koma bautar wani ba Allah ba wato gumaka kenan, sai Allah SW ya halakar da su da iskar goguwa mai qarfin gaske, to haka ya faru da Fir'auna da mutanensa, suna sakin mahalicci suka kama bawansa sai ya halakar da su dukansu, ya tseratar da Musa AS da jama'arsa, kamar yadda ya halakar da mutanen Nuh, Hud da Salih AS.
.
To bayan Banu Isra'ila sun haye kogi jagoranci ya dawo wa muslunci qarfi ya samu sai suka koma wa bautar dan maraqi ba Allah ba lokacin da Musa AS ya je karbo Attaura, sun ma taba gaya wa Musan cewa "Ka nuna mana Allan mu gansa baro-baro" tsawa ta ladabtar da su amma duk da haka suka sake kafurcewa, Allah SW ya hukunta su da cewa su yaqi kansu, wannan umurni ne ta bakin manzonsa, dole suka yi ta yaqi tsakaninsu ba ji ba gani har suka kashe kawunansu da dama kafin Allah SW ya karbi hanzarinsu, muslunci ya sake dawowa da jagorancin jama'a.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)