MIJIN ƘAZAMA 01


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•

      
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀    
           *MIJIN KAZAMA*
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

             *Na*                            

          *Maman Hafiz* 
        
                  *Niger*


*_Bismillahi Rahamani Rahim! Wannan labarin na kirkira ne, wanda ya yi kama da labarinsa ya yi hakuri, ban yi sa ba don cin zarafi wani ko wata ba._* 😌😌


Page 1

"Amina Amina!"  

"Na'am Mama!" Ta fito daga wani madaidacin daki tana murza ido, da ka gan ta ka san daga barci ta tashi. 

Wata dattijiwa ce mai kimanin shekara 40 take kiran yar tata Amina, fada ta hau ta da shi, "Yanzu Amina yaushe za ki bar kazanta? A ce wanki kayan ki ma gagaraki yake tun jiya kika jika kayan nan amma kin kasa wanke su, dubi ruwan ki gani har ya sauya launi.

"Ba zan iya wanke su ba mama. Hanne ta ce za ta wanke mini idan ta taso daga école ( boko)."

"Hmm! Allah ya kyauta! Yanzu a ce kanwarki ce za ta rika miki wanki? Amina na ga yadda za ku yi ranar da kika yi aure."

"Mama ni ai ba zan auri miji talaka ba, wanda har zan rika wanki a gidansa. Mai kudi zan aura mai inji wanki, kin ga ai na huta da wanki."

"Allah Ya sa." Abin da mama ta furta ta shiga daki don lamarin na Amina tsoro yake ba ta, a ce ya mace ba tason yin aiki ko kadan, sai son jiki da kazanta.

Amina ma juyawa ta yi ta koma dakinsu ta kwanta kan matelas ( katifa) ta ci gaba da barcinta ajikinta. Wai an yakushi kakkausa. 🤷🏻‍♀️

Mama fitowa ta yi ta shiga cuisine ( kicin) Girki za ta daura ta ji sallama Hanane Amsa sallamar ta yi ta shiga cuisine.

Sannu mama ta yi mata ta ce, "Har kin dawo?" 

"Na dawo mama, bari na je na cire tenu ( uniforme ) na zo na daura girkin."

"A'a Hanane je ki huta daga dawowarki za ki ce za ki yi girki."

"Haba mama miye amfanin mu muna gida kina girki, na san yaya Amina ba girka za tacyi ba."

"Hmm! Wannan kazama ko ta girka ai kin san babu mai cin abincinta, wa zaici girki kazama?"

Dariya suka saka a tare Hanane ta wuce daki ta cire tenu ta saka kayan zaman gida ta koma cuisine ta karbi girkin ta dora. Mama daki ta koma ta kama sakarta da take yi, awarwaraye ne da sarka na tsakiya irin nasu na Fulani shi ne sana'arta.

Hanane ta gama girki ta tattara cuisine ta share duk kayan da ta bata ta wanke. Kayan Amina ta dauka ta wanke tas ta shanya mata, ta gyara tsakar gida ko ina fes fes gwanin ban sha'awa.

Hanane sarkin tsafta (Haka ake son mace, ba irin su o'o ba 😅😅Amina).

Dakinsu ta shiga ta tattara kayan, ta yi shara ta goge ta saka tura ta fito. Amina na can na shirgar barcinta ba ta san wainar da ake toyawa ba.  

Hanane ta yi sallama bakin kofar dakin mama, mama ta amsa. Ta ce, "Na kammala girki mama."

"To!" Ta ce ta yi mata sannu, kai tsaye ta wuce douche (bayi), wanka ta yi ta dauro alwala ta fito ta nufi dakinsu.

Mama ta fito ta shiga cuisine ta fitar da abinci ta ce da Hanane ta zo ta dauki abincinsu, ta koma dakinta.

Har yanzu Amina na barcinta, tashin ta ta yi ta ce, "Tashi ki yi sallah lokaci ya yi."

Mika ta yi ta tashi ta fito ta dauki sahani ( buta) ta wuce bayi, ta fito alwala ta dauro ta zo ta yi salla. Hanane ta gama sallah ta yi addu'a ta fito ta shiga cuisine ta dauko abincin nasu.

Bayan sun gama cin abincin Hanane ta dauki Al-Kur'ani ta fara yin tilawarta cikin tattausa lafazi.

Amina kuwa tana gama sallah ta janyo kayan kwalliya ta shiga yin kwalliya. Amina sarkin kwalliya, da a ce kwalliya kadai ce aikin mace da kin huta, za ki samu maki mai yawa sai dai kash!🤦‍♀️ Da saura rina a kaba.🤣

Bayan ta gama kwalliya komawa ta yi ta kwanta abinta. Da yamma baban su Amina ya dawo daga kasuwa tare da kanninsu  
Haifane, da ke bin sa kasuwa ranar da babu boko ko Islamiya.

Sallama suka yi a tare, mama ce ta amsa musu tana zaune bisa tabarma, Haifane ne ya zo da gudu ya hau samanta, shafa kansa ta yi ta ce, "Auta yau na yi missing dinka ko da rana baka dawo ba, ka karbi abincinku."

"Ai baba ne ya ce yau ba za mu ci girkin gida ba, fura da nono zavmu sha." 

Dariya mama ta yi ta ce, "Ashe dai yau kun more don na san Abbanku da fura ba wasa!"

Tsakar gida baba ya duba bai ga Hanane da Amina ba. Ya ce da mama, "Ina 'yammatan gidan naki?"

"Suna dakinsu, kila sun yi barci ba su ji shigowarku ba."


```Ku yi hakuri farko ne, za a kara yawan typing.``` 

*Maman Hafiz* ✍️
Post a Comment (0)