MUGUN ABOKI 04

*MUGUN ABOKI...................*

👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬

             *FUTOWA TA👇
                       *(4)*

 
*TASIRIN ABOKI NA KWARAI GA ABOKINSA*

   Aboki na kwarai yana da matuqar tasiri ga abokinsa daga cikin tasiran da aboki yake dashi akan abokinsa sune kamar haka :

*1- Aboki* zai tasirantu da kyawawan dabi'u da halaye wanda abokinsa yake dashi, sai ya wayi gari shima ya zama irinsa. 

*2- Aboki na kwarai* zai dunga gaya maka aibukanka, ya nuna maka yadda za kayi galaba akansu kuma ya taimakeka akan hakan. 

*3- Aboki na kwarai* zai saka ka ka kasance wajan zama jajurtacce wajan karatu da ayyuka da Al'amuran da suka shafi duniyarka da lahirarka. 

*4- Aboki na kwarai* ako da yaushe zai dunga maka fatan Alkhairi, zai dunga yi maka nasiha akan abun da yake wajibi a gareka ka aikata sa, zai shiryar da kai zuwa ga tafarki madaidaici, kuma ya nisantar da kai daga miyagun hanyoyi. 

*5- Zama da Abokai na kwarai* Alkhairi da Albarka zasu game ku baki daya, kuma zaka samu damar fa'idantuwa da abubuwa mai tarin yawa dan gane da zama da su.

*6- Aboki na kwarai* ako da yaushe yana riqe da hannunka zuwa ga hanyar da zata kai ka Aljannah saboda ko da yaushe yana tunatar da kai Ubangiji. 

*7- Zama da Abokai na kwarai* sababine da zai janyo maka soyayyar Ubangiji saboda Allah yana cewa "soyayyata ta tabbata ga wadanda suke soyayya saboda ni kuma suke zama tare saboda ni". 

*8- Aboki na kwarai* zai qarfafeka, zai kiyaye kwarjininka agaban mutane, kamar yadda zai dunga saka ka aikata abun da ka cire tsammanin iya aikata sa. 

*9- Zama da Abokai na kwarai* zai saka kasan mutanan kirki da yawa, wanda hakan zai saka ka kawayi gari kaima ka zama mutumin kwarai. 

*10- Aboki na kwarai* yana tsaye a gefanka ako da yaushe, har ka tsaya da kafarka akan abun da yake baka wahala. 

  A qarshe nake cewa, kada ka sha wahala wajan neman aboki na kwarai, idan ka kasance na kwarai tabbas zaka samu mutanen kwarai suna kawo kansu zuwa gareka kai ma kana kai kanka zuwa garesu, haka zalika idan ka zama na banza zaka samu mutanen banza na zuwa gareka, don haka kafin kayi tunani wajan neman aboki na kwarai, kayi tunanin kai ta ya ya zaka zama mutum nagari.



*UBANGIJI KA NISANTAR DAMU DAGA MIYAGUN ABOKAI*


*MU HADU A FUTOWA TA 05*

*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
        *Dalibai masu neman ilimi*
        *Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
*MARYAM HUSAIN ABDULLAH*
       *(UMMU HANAN)*
       🥏08026799975🥏

Post a Comment (0)