KARAMCIN AHLUL BAITI 01

*KARAMCIN AHLUL BAITI (01)* 
**********************
Watarana wani balaraben kauye yazo wajen Imamul Husain (ra) domin neman taimako awajensa, sai yace masa "Hakika naji Kakanka ï·º yace *"IDAN ZAKU ROKI WATA BUKATA, TO KU ROKETA WAJEN MUTUM HUDU :*

KODAI BALARABE MADAUKAKI, KO KUMA WANI UBANGIDA MAI KARAMCI, KO MAHADDACIN ALQUR'ANI, KO WANI MA'ABOCIN KYAKKYAWAR FUSKA".*

- Amma larabawa, dukkansu sun samu daukaka saboda albarkar Kakanka ï·º.

-Amma karamci kuwa, wannan halinku ne kuma dabi'arku ce, Yardar Allah ta tabbata gareku. 

- Amma Alqur'ani kuwa, agudanku aka sassaukar dashi. 

- Amma kyawun fuska kuwa, Naji Kakanka ï·º watarana yana cewa : "Idan kuka so ku kalleni, to ku dubi Alhasan da Alhusain (amincin Allah ya tabbata garesu)."

Daga jin haka sai Sayyiduna Husaini ya tambayeshi "Mecece Bukatarka?"

Sai Balaraben kauyen ya rubuta masa a Qasa. 

Sai Imamul Husain ya karanta sannan yace masa "Naji Babana Aliyyu yana cewa "Qimar kowanne mutum ita ce abinda yafi kwarewa akansa".

Kuma naji Kakana ï·º yana cewa "Kyautawa ana yinta ne bisa gwargwadon sani".

Don haka zanyi maka tambayoyi guda uku idan ka amsa guda daya daga cikinsu, zan baka sulusin dukkan abinda na mallaka (wato ⅓).

Idan ka bani amsar guda biyu daga cikinsu, to zan baka kashi biyu cikin ukun abinda na mallaka. Idan kuwa ka amsa dukkan tambayoyin nan uku, zan baka dukkan dukiyata".

Alokacin nan kuwa ba'a dade sosai da kawowa Imamul Husain wata jakar kudi (dinarai ko sulallan zinare) daga Iraqi ba. 

Sayyiduna AlHusain sai yayi masa tambayar farko, yace masa "Shin wanne ne Mafificin ayyuka?".

Sai balaraben kauyen yace "Yin imani da Allah".

Sai Imamul Husain ya sake tambayarsa "To wanne abu ne zai tseratar da mutum daga hallaka?". Sai Balaraben yace "Dogaro sa Allah".

Sai Imamul Husain ya Qara tambayarsa "Wanne abu ne yafi Qawata mutum?". Sai yace "Ilimi da hakuri tare dashi"

Sai Imamul Husain (ra) yace "To in mutum bai samu wannan din ba fa?".

Sai yace "To Dukiya da kuma karamci. (wato yawan kyauta da dukiyar) "
Sayyiduna AlHusain ya sake ce masa "To in wannan bai samu ba fa?" sai yace "To talauci da hakurin zama dashi".

Sai ya sake tambayarsa "To in wannan bai samu ba fa?" sai balaraben kauyen yace "Tsawa ta sauko daga sama ta Qonashi".

Sai Imamul Husain yayi murmushi ya jefa masa wannan jakar kudin baki dayanta (ba tare da ya kirga ba)..

- Daga Tafseerul Qur'an na Imamun Naisaburiy

Al Imam Fakhruddin yana yabon Ahlul Baiti yana cewa *"BA DON SOYAYYARSU DAKE CIKIN ZUCIYA DA JIKI BA, DA ZUCIYA BATA DANDANA ZAQIN IMANI BA".*

FASSARA DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (23/08/2021 14/01/1443).

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss

Post a Comment (0)