MACE TA GARI 03

(MACE TA GARI 3)

2nd/Muharram/1443AH-11/the/August/2021

27. Mace ta Gari a Har Kullum Bata taɓa Ganin Ƴaƴan da ta haifa a matsayin manya, kawae dai Abinda take dubawa shine itace Wacce ta Haifesu Shiyasama Bata Taɓa Barinsu suyi Abinda Ransu Yakeso wai Sabida Yanzu Sunkai Shekara 18 ko Kuma sun Gama Jami'a da Sauransu Ballan tana ma tace ya Zatayi Dasu, Domin idan Mahaifanka Suna raye har gobe to kai Yaro ne Awajensu.

28. Mace ta Gari Ta Kasance Mai Riƙo da Addinin Allaah, ba Mai Sakaci da shi ba.

29. Mace ta Gari Ta kasance mai gaskiya da Riƙon Amana a Koda Yaushe.

30. Mace ta Gari itace Mai Sanya Allah a Ranta a duk Al’amuranta na Yau da Kullum.

31. Mace ta Gari itace mai Shigar Mutunci, Misali Sanya Hijabin da zai rufe Mata Jikinta Yayin da take Tare da Wanda ba Muharraminta ba ko kuma Yayin da Zata fita Zuwa Unguwa da Sauransu.

32. Mace ta Gari Ta kasance mai Yawan Kwalliya da Ado ga Mijinta.

33. Mace ta Gari Ta Kasance Ƙwararriya Wajen iya Girki.

34. Mace ta Gari itace mai Godiya ga Abin da Mijinta Zai Kawo Mata, Bata Raina Dukkan Wani Abin da Mijinta ya Kawo Mata.

35. Mace ta Gari Ta kasance mai Gaggawar Amsa Kiran Maigidanta Yayinda ya Kira ta Zuwa ga Shimfiɗarsa.

36. Mace ta Gari itace mai Rufawa Mijinta Asiri, Ba mai Watsa Sirrinsa ga Kowa ba.

37. Mace ta Gari itace Mai Nuna Farin Ciki idan Abin Farin Ciki Yasamu Mijinta, da Kuma Nuna Baƙin Ciki Yayinda Abin Baƙin ciki Yasa me shi.

38. Mace ta Gari itace Wacce Bata Yabon Mijin Wata Alhali tana tare da Nata Mijin.

39. Mace ta Gari Bata ba Wata ko Wani Dama Yaji Sirrinsu  (ita da Mijinta).

40. Mace ta Gari Ta Kasance Mai Ƙoƙarin Neman ilimi da Kuma Aiki da shi.

41. Mace ta Gari itace Mai Nisantar Abin da Mijinta ba ya so, kuma Take Kusantar Abinda Yake so.

42. Mace ta Gari itace Mai Bin Umarnin yi ko Bari Wajen Nuna Masa ɗa'a da so da Kauna a fili, ba a Ɓoye ba, Matuƙar ba Akan Saɓon Allaah Bane.

43. Mace ta Gari itace Mai Nuna Tausayi ga Mijinta, ba mai Jawo Masa Buƙatun da ba zai iya biya Mata ba.

Zamu da Kata Anan Inshaa Allaah, Zamuci Gaba, Domin Sanin Wane ne Miji Nagari.

Allaah Yasa Matayen mu su Zamo Nagari ga Mazajen su, Suma Kuma Mazajen su Zamto Nagari ga Matayen su Aameen Yaa Rabbul Izza.

Allaah Yabaiwa Ƴan Matan mu Mazaje Nagari, Muma Kuma Ƴan Samarin Yabamu Mata ye Nagari,

Daga Ɗan Uwanku a Musulunci

(Ustadh_Abulfawzhaan)


Post a Comment (0)