(MACE TA GARI)
23rd/Dhul Hijjah/1442AH-2nd/August/2021
Mace ta Gari itace Silar Zaman Lafiya a Gidanta,
Mace ta Gari itace Mai Kulada Addinin Mijinta,
Mace ta Gari itace Mai Kulada Tarbiyyar Yaranta,
Mace ta Gari Itace Mai Yiwa Mijinta Addu'a Akoda Yaushe,
Mace ta Gari Bata Taɓason Ganin Damuwa a Fuskar Mijinta,
Mace ta Gari itace Wacce Idan Mijinta Zai Fita Zata Rakoshi Tayimasa Addu'a Sannan Tayimasa Nasi ha da Faɗin Cewa: Kaji Tsoron Allaah Adukkan Abinda Zaka Aikata,
Tace Masa Allaah Yabada Sa'a idan Kafita, Sannan Ina Roƙon ka Don Allaah. Idan kaje Naiman Halas Baka Samu ba, Kadawo Gida Kawae Zamuyi Hakuri, Kada Kasa Kanka Cikin Haramun,
Domin Zamu iya Jure Yunwar Duniya, Amma Kuma Bazamu iya Jure Azabar Lahira ba,
Mace Ta Gari, Itace Ke Rufe Sirrin Mijinta Tamkar Antona Rami An Binne,
Mace ta Gari Bata Taɓa Faɗawa Duniya Halinda Suke Ciki da Mijinta, Sai Dai Kullum Tayita Tayashi da Addu'a,
Mace ta Gari itace Mai ƘoƘarin Sauke Duk Wani HaƘƘi da Nauyi da ya Rataya a Wuyanta,
Mace ta Gari itace Mai Lura da Al'amuran Gidanta,
Mace ta Gari Bata Barin Hawayen Mijinta ya Zuba a Banza,
Mace ta Gari Bazata Taɓa Buɗan Baki Tacewa Mijinta me ka Taɓa Yimini ba, Domin A Ƙashin Gaskiya kuwa Shine ma Yayimiki Abu a Bayyane,
Kuyi Hakuri da Kalamaina Yaku Ƴan uwa Mata, Ki Tunafa Ke Kadae ya Ɗauko Daga Gidanku A Matsayin Matar Aure, Kinzoki Gidansa Babu ɗa Balle Jika, Sannan Kuma Yanzu Gaki da Yara Wata Ƙilama Harda Jikoki? Amma Kuma wai Duk da Hakan kice Mai Mijinki Yataɓa Yimiki? Anya kuwa Akwae Adalci Anan?
Allaah Ya Shiryarmana da Al'ummar Musulmai, Yakuma Karamuku Hakuri da Juriya da Zaman Lafiya A Gidajen Auren ku,
Mu Kuma da Bamu dasu Daga Cikin Ƴan Matan mu da Samarin mu dama Zawarawan Cikin mu, Allaah Ya Zaɓawa kowa Abokin Zama Nagari, Aameen Yaa Rabbul Izza.
Zamuci Gaba Inshaa Allaah
Daga Ɗan Uwanku A Musulunci,
(Ustadh_Abulfawzhaan)